← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 211

Sashe 27

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani corridor suka shiga sukai yar tafiya nan suka k'araso bakin wasu kopopi dake opposite da juna Jidderh ta tura ta 6angaren hagu ta juyo tace ma Fatuu ta shigo, d'aki ne mai d'an girma akwae madaidaicin gado daya sha bedsheet da side drawers d'in shi da dressing mirror sai wall cabinet sosae d'akin ya tsaru yasha decorations su frames da artworks da flowers harda wall stickers ga labulayen ciki ma masu kyau fentin d'akin ma kusan kala ukku ne amman yadda akai masu wani design sun k'ara k'awata dakin , suna shiga Jidderh ta juyo tace "Welcome to Jidderh's palace" jinjina kai Fatuu tay tana murmushi Jidderh tace "ya kika ga d'akin nawa" Fatuu tace "it's a beautiful palace gaskiya ya tsaru" dariya Jidderh tay tace ta gode, bayan ta aje trolley d'in a gefe ta nuna ma Fatuu gado tace ta zauna itama a gefe ta zauna su twins suka saka Fatun tsakiya,

"Kinsan abunda nike karanta kenan interior design yanzu haka na kusa gamawa kuma ina gamawa zan tafi Dubai in k'ara yin wasu courses d'in kan hakan, so nike in bud'e babban company in nagama da zai rink'a supplying kayan decorations irin su furniture, labulaye, carpets, flowers harda fitilu da dai sauran su sannan kuma ba iya saidawar ba harda tsara wuri kamar gidaje, Offices, Hotel rooms da dai sauran su" Fatuu nata jinjina mata kai har ta gama sannan tace gaskiya tayi tunani mai kyau don irin aikin na kar6uwa yanzu Jidderh d'in tace sosae ma, kallon su twins tay ta d'an d'aure Fuska tace "wai ku bazaku k'yaleta ta huta ba ku tashi ku tafi tunda kun gaisa" mak'e mata kafad'a sukai suka tura mata baki sai kace ana latsa masu remote komai a tare suke Fatuu ta kai hannu ta rungumo su jikinta tace ta k'yale su ai an dad'e ba'a had'u ba, Jidderh na murmushi tace "koda yake suma zauna kita kallon su pls ki haifo mana irin su amman ba masu irin halin su ba don sai su haukata ki kullum cikin ba mutane ciwon kai suke" tana rufe baki suka murgud'a mata baki ta yunk'uro zata make su suka k'ank'ame Fatuu suna dariya itama dariyar take tace ma Jidderh tayi hak'uri don Allah, mik'ewa tayi ta nufi wardrobe, bud'eta tayi ta kai hannu ta fiddo wasu kaya dake a goge bayan ta rufe ta nufo gadon, a kan cinyar Fatuu ta d'aura su tace "kinga anko d'in da akayi na Walima da Dinner" sakin jikin su twins tay ta kai hannu ta fara d'aga kayan Jidderh tace ta warware mana ta gan su sosae, atamfar ta fara warwarewa sosae ta burgeta saidai da gani bata rasa kud'i, kallon Jidderh tayi tace "amman dae tayi kyau wllh" tace "sosae ma Chiganvy gold mix and match embroidery ne" jinjina kai Fatuu tay sai kuma ta tambayeta nawa take tace "kinga atamfan kaman kashi ukku ne, mutum zai iya yin Chiganvy gold d'in kawae ko yay mix and match da embroidery d'in ko kuma yayi embroidery d'in kawae gaba d'aya dai duka Atamfa kala d'aya ce ai kin gani kawae ita wannan normal atamfa ce mai gold ita kuma d'ayar sai akai mata aiki gaba d'aya jikinta, so mutum in yayi mai mix d'in zai iya ai mashi style mai kyau da mai aikin da mara aikin kaman yadda akai man, in Normal Chiganvy gold d'in mutum zai yi just 18k ne in kuma mix and match d'inne 37k sai kuma mai gaba d'aya embroidery 50k, su Aunty Laila mai gaba d'aya sukai nima naso ayi man ita amman aka k'i saida aka d'inka man mix and match d'in kuma sukai ta cewa dama ita sukai" ta k'arasa tana murmushi itama Fatuu murmushin take kafin ta tambayi lace d'in tace shi 35k yake, shiru Fatuu tay tana tunanin kawae dae in mutum zai yi ankon sai wurin 100k ya tashi harda kud'in d'inki saidai in ko mutum yayi normal Chiganvy d'in, tambayar ta tayi ina ake saida su Jidderh d'in tace Zee Collections ce ta kawo masu tace Ok zata mata magana tana son siya ma su gwaggon ta da k'anwarta da sauri Jidderh tace "ai fa Big Bro ya siya masu dama cewa yayi a bari kizo sai a tambaye ki wand'anda za'a d'inka mawa atamfa biyar da lace biyar yasa aka amsar maki yace in kinzo basu isa ba sai ayi mashi magana" d'an murmushi Fatuu tay yana daga abunda ke sawa tana k'ara son shi kenan akwae shi da sanin yakamata, tunanin wanda zata sa a d'inka ma su ta shiga yi nan ta yanke gwaggo da Mino sai Fauzy da Yadikko sai Aunty Mareeya, tunanin Haulat ko zata zo tayi don sunyi waya tace mata zata zo in sha Allahu k'arshe ta yanke tunda tana da number d'in Zee Collections d'in zata mata magana kawae ba sai Haisam din ya k'ara siya ba tunda tana da kud'i da yawa a account d'inta sai ta siya ma Haulat da k'annanta su Aysha tasan inta rok'i Kb mai d'inki zai d'inka masu, daga baya Jidderh tayi mata Maganar zuwa taci Abinci tace tunda Magrib ta kusa ta bari in tayi salla sai ta ci.

Bayan sunyi sallar Laila ta shigo tana murmushi ta k'ara yi ma Fatuu ya gajiyan hanya tace mata ai ba wata gajiya, kallon Jidderh tay tace "ke haka ake kula da bak'o kin ruk'eta ashe har yanzu bata ci Abinci ba yanzu Mom ke man magana akan haka, so kika Big Bro yace mun bar mashi mata da yunwa ne" ta k'arasa tana d'an harararta tura mata baki tay tace ai saida tayi mata magana ita tace a bari sai tayi salla, ce mata Laila tayi ta taso suje taci Abinci tana murmushi tace to ta mik'e, ganin zata fita da Hijab Laila d'in tace ya zata je cin Abinci da Hijab, cire Hijab d'in tay Laila tabi jikinta da kallo ganin tana niyyar d'aukar gyalenta dake akan gado yasa Jidderh yin saurin d'auke shi tana dariya tace wai miye zatai ta wani lullube lullube nan fa gida ne Laila tace ato ta fad'a mata dai, ba yadda Fatuu ta iya haka ta bita duk ta takura suka fita.

Da daddare sun gama shirin kwanciya cikin kayan bacci Jidderh ma tasaka nata Fatuu na kwance saman gado ita kuma tana zaune a gefen ta suna hira aka turo kopar d'akin duk suka kai idanuwan su wurin, Mom d'in su ce ta shigo da yar sallama itama tana sanye da kayan bacci riga da wando brown kanta ta yafa bak'in gyale, Fatuu na ganinta ta tashi zaune sosae tana mata murmushi, a bakin gadon kusa da Jidderh ta zauna itama fuskar ta d'auke da Murmushi Fatuu ta gaishe da ita ta amsa, kallon Jidderh tayi tace "nazo ki ban aron Yayar ki" yanayin face d'inta ne ya canza tace "aro kuma Mom, mi zata maki da daddaren nan" har saida tay yar dariya jin wata tambaya ta Jidderh tace to zasu je d'akinta ta kwanta ne, da sauri tana yamutsa fuska tace "gaskiya Mom a'a bacin gashi har ta kwanta anan lafiya lou" still Murmushi take tace mata ai ba lalle taji dad'in kwanciya anan ba gadon zai iya masu kad'an shiyasa, a hak'ik'an ce tace "No mom ba wani kad'an da zai mana yana fa da d'an girma in ma yayi kad'an d'in ni zan yi shimfid'a a k'asa", d'an bud'a ido Mom d'in tayi ta hau jinjina kai Fatuu dai sai faman murmushi take, kallonta Mom d'in tayi tace mata lafiya lou taji dad'in kwanciya anan da sauri tace mata eh harda ce mata ta tabbata ta k'ara cewa eh, mik'ewa tayi tana fad'in ai tasan Jidderh bazata bari ta fad'i mata gaskiya ba Saboda ta faranta mata duk sukai yar dariya tayi masu sai da Safe ta juya, tana fita wayar Fatuu ta fara ringing Jidderh ta d'aukko mata akan bedside drawer tana kallon screen d'in ta gane Haisam ne mai kiran kallon Fatuu tay ba tare data bata ba tace "Ya Haisam ne yanzu haka shima yana iya cewa kije part d'in shi ki kwana wllh, don Allah bari in ce mashi kin yi bacci" shiru Fatun tay don tana son jin muryar mijin nata Jidderh tace "pls is just for today gobe Kya je can in ma so yake ki kwana acan d'in" kunya ce ta kama Fatuu a dabarbarce tace mata a'a wllh ba haka bane lafiya lou tace mashi tayi baccin kiran na gabda yankewa ta d'aga tun kafin yayi Magana Jidderh tace mashi tayi bacci tun d'azun yay d'an shiru kafin ya furta Ok ya katse kiran Jidderh nata Murmushin jin dad'i.
Chapter 27 · 0% Book details