← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 211

Sashe 33

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jingina da kujerar Haisam yay idon shi akan Sameer yace "Kai wai sai yaushe zakai aure ne naga alamar ma baka da ko niyya" d'an yamutsa fuska yay idon shi akan Screen d'in wayar shi cikin husky voice d'in shi ya furta " I'm not as promiscuous as you are, ni ba dole sai nayi ba" d'an bud'a ido Haisam yay alamar mamaki yace "U call me dat!" Sai lokacin ya d'ago ido ya kalle shi yanayin fuskar shi yay d'an alamun murmushi Abbas sai dariya yake, ce mashi Sameer d'in yay ai ya fahimci ta farkon bata satisfying nashi ne shiyasa har ya k'ara itama yasan bada jimawa ba zai k'ara, a fiffizge yake Maganar yana yi yana d'age gira, Abbas sai dariya yake hakan ne ya janyo hankalin Salim ya maido idon shi kan su, shi dai Haisam murmushi kawae yake don bai san mi zai ce mashi ba, mik'ewa Sameer d'in yay idon shi akan Haisam yace yana bashi shawara daga wannan yayi hak'uri hakanan don a yawan aure ana samun cuta daga haka ya nufi hanyar Bedroom Haisam ya bi shi da ido yana murmushi haka Salim ma murmushin yake Abbas kuma sai dariyar k'eta yake, har ya kusa Bedroom d'in Haisam ya d'an d'aga murya yace Abinci fa, hannu ya d'an girgiza mashi ba tare daya ce komai ba bai kuma juyo ba har ya shige d'akin, bayan shigar shi ne Abbas yace "ashe ya iya tsokana haka" d'an girgiza kai Haisam yay yana dariya ya furta "d'an iska ne da kake ganin shi" Abbas din ya fashe da dariya.

Sai bayan Magrib su Fatuu suka dawo anyi mata k'unshin a k'afa da hannu yayi kyau sosae ja da bak'i ne saidae jan yafi yawa kuma ba wani mai yawa bane sosae, su Fauzy da Mino duk ba'ayi masu ba don sun yi tun a Katsina kawai rakiya sukai, Jidderh ma anyi nata yan sarkoki masu kyau, d'akin Jidderh Fatuu ta wuce don kayanta na acan Fauzy kuma ta nufi baya, tana zuwa wanka ta shiga bayan ta fito Jidderh ma ta shiga, shiryawa tayi da doguwar riga bayan ta gama ta shimfid'a prayer mat ta kabbara salla da suna a hanya aka yi ta, bayan Jidderh ta fito tana cikin shafa mai su twins suka shigo ganin yadda suka fad'o cikin d'akin yasa ta kalle su tace daga ina suna dariya suka ce daga wurin Momyn Nasarawa suke, d'an waro ido tay tace "Momy ta zo kenan ashe shiyasa naga an k'ara security a gate, aikuwa bari in je mu gaisa" ta k'arasa tana ta washe baki, ba 6ata lokaci ta shirya itama doguwar rigar ta zura ta d'aukko Hijab ta kabbara salla, Fatuu na gamawa ta kalli su twins tana murmushi, wurin ta suka nufa suka zauna a gefen ta duk suka kama hannunta suna yabon k'unshin ta itama ta kamo hannun Mubeena tana yabon nata, Jidderh na sallamewa tace ma Fatuu tazo suje ta gaisa da twin sister d'in Mom d'in su First Lady d'in Nasarawa, d'an murmushi tay tace mata taje kawae Jidderh d'in ta matsa mata tace tasan ma za'a aiko kiran ta don su gaisa gara tazo suje kawae, dole ta mik'e Jidderh ta cire Hijab d'in jikinta ta d'aukko gyalen rigar itama Fatun tace mata ta cire hijab d'in mana, cirewa tayi ta d'auki gyalen rigar ta yafa su twins na ruk'e da hannuwanta suka tafi, part d'in Mom d'in suka nufa security detail d'in na a bakin k'opa suka gaishe da ita ta amsa a raina nace rayuwa kowa da hanyar cin Abincin shi wata na ciki tana hutawa ga wata k'ik'am tana gadin ta, nima dai sannu nace mata ta d'aga man kai na wuce sumi sumi, a parlor suka fara tsayawa suka gaggaisa da Mutanen ciki wasu na nuna Fatuu suna itace Amaryar ita dai sai d'an murmushi take tana Sunna kai, Bedroom suka wuce lokacin da suka shiga gaba d'aya Mom d'in su data Nasarawar suna zaune a saman gado jikin Her Excellency sanye da jallabiya cotton mai gajeran hannu bak'a anyi mata sak'a mai kyau orange a gaba itama Mom d'in su Haisam doguwar riga ce a jikinta gaba d'ayan su ba kallabi a kan su sai tarin sumar su dake a nad'e, daga d'an nesa Fatuu ta tsaya tana kallon su, ba don tasan dama su yan biyu bane to da ba k'aramar razana zata yi ba duk da yanzun ma saida ta d'an rud'e ganin Mutum biyu iri d'aya bata yi zaton haka suke kama ba komai nasu iri d'aya, nufar gadon Jidderh tay da gudu tana zuwa ta fad'a jikinta tana fad'in "Welcome lovely Mom" hannu tasa tana d'an bubbuga bayan Jidderh tace "thank you beloved Daughter" d'agowa Jidderh tay tana dariya itama murmushi take tace sun dawo kenan ai ta tambaye ta ance sun je k'unshi ne da bride d'in, ce mata tayi eh ai gata nan ma tare suka zo ta juya ta kallo Fatuu da tayi tsaye kamar an dasa ta, Mom d'in su Haisam ce tace mata ta k'araso ciki mana tana murmushi, nufo gadon Fatuu tay tayi mata alamar taje su gaisa ta nufi side d'in da suke, kokarin duk'awa tay k'asa Hajiya Zainab d'in ta nuna mata kusa da Jidderh tace ta zauna, a sanyaye ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace mata ya hidima a hankali Fatuu tace Alhamdulillah, jinjina kai tayi tace Allah yasa Alkhairi Fatun ta amsa da Amin a hankali, daga haka bata k'ara ce mata komai ba ta maida idon ta akan Jidderh tana tambayar ta karatun ta nan ta shiga bata labarin yadda yanzu ta k'ware wurin tsara wuri, tana murmushi tace ma sha Allah zata gayyato ta Government House tazo ta tsara masu wasu wurare, washe baki Jidderh tayi tace da taji dad'i amman ai tasan wasa take tana murmushi tace mi zai sa tayi mata wasa indai ta k'ware yadda ta fad'a, sosae Jidderh ta shiga washe bakin jin dad'i Fatuu dai kanta na a k'asa sai jefi jefi take d'agowa ta kalle su ita mamaki ne duk yabi ya cika ta don bata ta6a ganin yan biyu ba haka masu bala'en kama, Mom d'in su ce tace ma Jidderh sun ci Abinci ne da suka dawo tace a'a ai basu dad'e da dawowa ba salla kawai sukai, tace to ta tashi suje kar a bar Amarya da yunwa Fatuu ta d'an kalleta tana murmushi, mik'ewa Jidderh tayi ta kamo hannun Fatuu ta mik'e suka nufi hanyar fita idon Hajiya Zainab akan Fatuu don Mom d'in su ta bata labarin komai game da yadda har akai Auren. Suna fita parlor Jidderh taga d'aya daga cikin ma'aikatan dake hada hadar Abinci tace mata ta kawo masu Abinci a d'akin su tace to, suna cikin cin Abincin wayar Jidderh ta fara ringing ta kai hannu ta d'auko, ganin mai kiran nata ta saki k'ayataccen murmushi Fatuu na ganin haka itama tayi murmushin, picking tay bayan ta kara ta a kunne ta furta Ok daga haka ta cire wayar tana yar dariya ta fara k'ok'arin mik'ewa tace ma Fatuu ta k'arasa cinyewa heartbeat d'inta ya zo, d'an bud'a ido Fatuu tay tana murmushi tace mata ashe tana da saurayi ai tayi zaton bata kula samari don bata ji tana Maganar su ba,

"Ai Aunty Fatuu na kama dahir ne shiyasa ban Maganar wasu samari, d'an Abokin Dad ne Minister of finance" jinjina kai Fatuu tay sai kuma tace "dashi za'a yi kenan?" Jidderh dake a gaban mirror tana gyara fuskarta tace "in sha Allahu yanzu haka ma shi so yake a sa mana rana nice nak'i yarda nafi son sai Aunty Laila ta fara yi tukunna da ta k'arasa karatunta za'ayi bikinta don har an tsaida magana ma tuni" Fatuu dake saurarenta tace mi zai hana to ta bashi dama sai a had'a su kawae tana murmushi tace shima haka yace amman ita tafi son ta gama Karatun ta gaba d'aya don shima a cikin karatun yake a London yanzu in ko sunyi aure bazasu zauna a wuri guda ba tunda itama Dubai zata tafi k'arin karatu dama ya gama nashi ne tasan zai bita Dubai d'in gara ya gama tukunna, bayan ta gama gyara fuskar tambayar Fatuu tay ko ta canza kaya tace mata ai rigar jikintan ma lafiya lou tunda bata dad'e da sakata ba ta yafa mayafinta kawai tace Ok, nufar k'opa tay tana ce mata sai ta dawo Fatun tace a gaida mata shi. Bayan fitar Jidderh bada dad'ewa ba wayar Fatun ta fara ringing, ganin mai kiran nata yasa ta saki murmushi kafin tay picking, gaishe da shi tay bayan ya amsa ya tambayi sun dawo ne tace mashi eh tun d'an d'azu ma,

"Shine ko ki kira ni kina mantawa da ni ko" murmushi tay a shagwa6e tace "zan iya mantawa da kai na kenan, ai kai ne ni so ban iya mantawa da kai Hubby u'r always in my heart, kai ne ma zuciyan nawa ai" tana jiyo sautin murmushin shi can yace "ya akai kika iya wannan d'in?"
Chapter 33 · 0% Book details