Sashe 17
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai bayan sallar isha ya dawo Fanan tace mashi suje suci Abinci, kusan gaba d'aya suka ci Abincin harda Farha da Hajiya Maryam da ba laifi ta sakar mashi fuska da suka gaisa, sai can wurin k'arfe goma na daren Dad d'in su ya dawo har part d'in nasu yazo suka gaisa Fanan ta rungume shi tana mashi shagwa6ar tayi missing nashi sosae shima yana fad'i mata yayi nata Haisam dai sai murmushi yake daga baya ya tafi, tun daga lokacin Fanan ta fara zille ma Mom d'in nata bata bari su zauna tare su dad'e don karta yi mata zancen, Sosae Haisam yake k'ok'arin faranta mata duk suka kasance tare, haka Fatuu ma yana yawan kiranta a waya tay ta zuba mashi shagwa6a,
Ranar Alhamis da yamma ya shirya zai koma saidae a ranar da safe Mom d'in shi ta kira shi ta sanar dashi tana son ganin shi yaje Abuja kafin ya koma don tasan yana Lagos d'in, lokacin daya kira Fatuu ya sanar da ita yayi tunanin zata nuna damuwa amman ga mamakin shi bata nuna ba tana murmushi tace mashi ba komai Allah ya dawo dashi lpy sosae yaji dad'i dama duk itace damuwar shi, a ranar da yamma yayi sallama da Hajiya Maryam Fanan ce ta tafi kai shi Airport, ita ke driving Motar yana gefe hannun shi ruk'e da nata, cike da k'auna sukai sallama da shi ta dawo cike da jin kewar mijinta, bayan ta parker Motar a parking space, tana shigowa cikin parlor ta iske Hajiya Maryam zaune da Farha suna kallo a Tv, nufar su tay tana sanye da jallabiya tayi rolling veil ta tsaya a bakin kujerun tay mata sannu tana kallon ta tace har ya tafi tace eh, shiru suka d'an yi kafin ta juya zata tafi d'aki taji muryar ta tace "Wait I want to talk to you" daramm gaban Fanan ya fad'i, dakatawa tayi ta kai idonta akan Mom d'in su ta nuna mata sofa d'in gefen ta tace ta zauna,
"Yanzu dai ai nasan kin huta sosae so am all ears ya kukai da Hajjaju ta amince an saki yarinyar nan?" Shiru Fanan tayi idonta a kan had'add'an carpet d'in k'asan parlon, maimaita mata tambayar tayi sannan ta d'ago ta kalleta gaba d'aya sun kafeta da ido harda Farha itama tana son taji amsar da zata bada, Sigh tay a sanyaye tace mata Hajiya ta k'i amincewa tace tayi hak'uri su zauna tare da ita, tun kan ta k'arasa Hajiya Maryam ta yamutsa fuska tana kallon ta har ta gama sannan cikin d'aga murya tace "You're telling a lie Fanan, daga yanayin face d'in ki nagane ba gaskiya kike fad'a man ba, kar ki manta ni na tsugunna na haife ki, so zan iya gane in kina 6oye man abu, dama tun da kika zo na fara zargin wani abu k'in tsayawa muyi magana ya k'ara k'arfafa zargin nawa, Now tell me the truth, else, ranki zai yi mummunan 6aci!" A fusace tay Maganar, abu Fanan ta had'iya kafin murya na rawa tace Ok zata fad'i mata gaskiyar, nan ta fara fad'i mata yadda sukai da Haisam ya nuna mata in ya saki Yarinyar za'a cuceta ne tunda shi ya fara saninta ya san hakan ne ma yasa Hajiya tun farko ta hana ya saketa, tun kafin ta gama ta katseta da tambayar "sai kika amince yaci gaba da zaman da ita???"
Cikin yar in ina tace mata yayi mata alk'awarin zai masu Adalci kuma daga ita bazai k'ara Auren wata ba shiyasa ta amince don tasan ko sun zo wurin Hajiyar ba amincewa zata yi ba tunda shima ya nuna zai cigaba da zama da ita.....,
Buga hannun kujera Hajiya Maryam tayi tare da mik'ewa tsaye cikin daka tsawa tace "Enough Fanan! I never knew you were such a fool until Today, ba a iya sakarci ko wawanci kika tsaya ba har hankali baki da shi, yanzu ke ashe dama baki da wayau har haka, wato ya zauna yayi maki dad'in baki shine kika hau kika zauna ke gaki shashasha har ki ka kasa gane cewa son yarinyar yake shiyasa ya fake da hakan, in don abunda ya shiga tsakanin su ne ba sadaki ya biya ba to miye abun cuta ko wani cin zali a ciki......!" Sosae take fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita ba a k'arshe tace sam bata yarda da amincewar da tayi ba don haka dole ta canza ra'ayi ta nuna mashi bata amince ba, shiru Fanan d'in tayi kanta a k'asa, ganin yadda ta d'auki zafi yasa ta d'ago kai idanunta cike da k'walla tace ma Mom d'in nasu ita gaskiya ta riga ta amince bazata canza ra'ayin ta ba tunda ya nuna yana son cigaba da zama da itan kuma Hajiya ma na so ita ta hak'uri sannan ita yarinyar sam bata da wata matsala zasu zauna lafiya,
rai a tsananin 6ace Hajiya Maryam ta nuna kanta tace "Fanan! Ni kike fad'a ma haka! ni kike k'ok'arin nuna ma kin za6i faranta ma mijin ki fiye da ni duk da komai nike ina yi ne don ki dawwama cikin Farinciki, don in ga rayuwar ki baki shiga cikin matsala ba!" Girgiza kai Fanan ta fara yi k'wallan da suka taru suka fara zubo mata cikin karyayyar murya tace "No Mom ba haka bane wllh, is just dat in life Sometimes we must sacrifice our own happiness for the sake of those we love, yanzu in na za6i farinciki na kad'ai zan bak'an ta ma mutane da yawa, Hajiya bata so, shima baya so sannan ita kanta Zarah bazata so ta zama bazawara ba, sannan yan'uwanta ma bazasu so ace an sake ta ba that's why na hak'ura kuma nasan in sha Allah zan ci riba tunda Allah yace yana tare da mai hak'uri" wani kalan murmushin takaici Hajiya Maryam tay tana jinjina kai da alama ta kashe bakinta ta kasa ma magana, ganin yanayinta yasa Fanan sauka daga saman kujerar ta duk'a saman knees d'inta ta shiga bata hak'uri tana fad'in don Allah ta fahimce ta, can ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Ok, kiyi yadda duk kika ga yayi maki Fanan rayuwar ki ce ba tawa ba, dama katsalandan ne irin nawa yasa na zaqe, amman ki sani ba baki nayi maki ba indai Namiji ne gaki ga shi zaki nadama ne, ina zaune wataran zaki kira ni kina kuka tunda har kika za6i farincikin shi fiye da naki farincikin ma na k'arfafa mashi ya zauna da wadda yake so, uhmmm harna tausaya maki Fanan, duk da a lokacin bazan ji tausayin ba ko misk'ala zarratin!!!" A kausashe tayi Maganar tana huci ta na gamawa ta nufi hanyar Bedroom a fusace Fanan ta fashe da kuka tana bata hak'uri tana fad'in ta Fahimce ta don Allah hakan kaddarar ta ne.......
*ASM 077*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Sosae Fanan ke kuka maganganun Hajiya Maryam sun ta6a mata zuciya sosae hakan ya k'ara tado mata rad'ad'in da take ji dangane da Auran Haisam d'in, dama ko a can Katsina ba K'aramin k'ok'ari take ba ta na dannewa, gaba d'aya abun yayi mata yawa a zuciya sosae take ta Kuka cikin kukan ta fara fad'in ita ya zata yi ne, tasan ko ta nuna bata so in dai hakan kaddarar ta ce dole sai yaci gaba da zama da Zarah k'arshe zata tada hankalin ta ne a banza, duk wannan abun Farha na zaune a inda take idon ta akan Fanan d'in dake a durk'ushe tana kuka bazaka gane yanayin da ke akan fuskar ta ba, mik'ewa Farhar tayi tana sanye da doguwar riga roba da ta kamata, wurin Fanan d'in tazo ta kai hannu tana k'ok'arin d'ago da ita Fanan d'in ta kalleta idanunta har sun yi ja fuskar jage jage da hawaye, ce mata tay ta tashi Fanan d'in ta mik'e ta koma kan kujera ta zauna itama Farhar ta zauna daga gefen ta idanunta akan ta, itama Fanan d'in kallonta take tana cigaba da zubar da hawaye can Farhar tace mata tayi shiru karta yi ciwo fuskarta a d'an yamutse tayi Maganar, hannu Fanan ta kai ta kamo hannunta guda cikin Muryar kuka ta fara Magana "Farha kema na baki haushi ko?" shiru tayi fuskarta kamar a d'aure dama ita yanayin fuskar ta a koda yaushe haka yake can tace a'a ita bata ji haushinta ba tunda taji zata iya kawae dai tayi mamakin yadda ta amince ta zauna da wannan yar talakawan a matsayin kishiyanta dama wadda suke the same level ne da sauki, hannu d'aya Fanan ta kai tana share hawayen fuskarta bayan ta gama a nutse ta fara ma Farha magana da sautin kuka tace "I want u to understand wacece Zarah ba yadda kike tunanin ta ba take, she's a very nice person bata da matsala wllh, kuma don ita talaka ce hakan ba yana nufin tana da illa ba Saboda da mai kud'i da talaka we're all the same a wurin Allah kuma in yaso zai iya canza rayuwar su suma su zama masu kud'in da baki ta6a zato ba, muma da kike ganin muna dasu bafa fin su muka yi ba ya bamu, kawai hikiman sa ne yasa ya raba don kowa yay benefiting da kowa, in ya bamu kud'i so yake muyi amfani da su wurin taimaka ma wanda bai ba bawai mu ci mu kad'ai ba kuma mu kyamace su, kinga kenan kamata yay mu rink'a girmama wanda bashi dashi tunda ta silar shi Allah zai k'ara bud'a mana because whenyou give you always get back more in return, sannan ta silar yi masu Alkhairi zai kai ka har Aljanna, Farha i advise u, stop hating the poor pls ki rink'a kyautata masu I assure u zaki ji dad'in rayuwar ki don kema Allah zai rink'a kyautata rayuwar ki zai rink'a baki way out a dukkan matsalolin ki....." Dakatawa tay tana numfasawa ita dai Farhar bin ta da ido kawae take still da yanayin da fuskar ta take tun farko,