← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 211

Sashe 14

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu Zarah nace sai in maido magungunan aro ko, dama shekaran jiya tayi promo jiya aka kawo man wanda na siya" shiru ta d'an yi kafin cikin jin kunya tace mata eh to tunda akwae, dariya Aunty Mareeya tasa tace "ja'ira da ba kince in ma kwashe duka ba, in ce dai na farkon sun yi maki aiki yadda nike ta fata Allah yasa ya magantu iya magantuwa" k'asa k'asa Fatun tace mata eh, kafin da k'yar tace mata harda kuka ma, wani irin ihu da Aunty Mareeya ta saki har saida Fatun ta cire wayar daga kunnanta tana dariya Fauzy ce ta taso da sauri tana tambayar Auntyn wai mi akai tay mata alamun ta tafi da hannu tace mata Maganar manya ce wannan, ce mata tay zata bada in zata je Makaranta gobe sai Fauzy ta tafin mata da su tace eh zata je, daga baya sukai sallama sai farinciki Aunty Mareeya ke yi, bayan Fauzy ta amshi wayar itama sukai sallama tace mata sai sun had'u School gobe, Fauzyn tace ita da ke shan Amarci ta bari ta gama, Fatuu na yar dariya tace yadda in jarabawa tazo zata rubuta hakan ko, duk suka yi dariya nan tayi ma Fauzy godiyar sak'on da ta tura tace dama koda ta nuna bata ji dad'i ba Saboda gudun abun da zaije ya dawo ne, Fauzyn na dariya tace mata haba ba komai ai tun lokacin ta fahimceta tayi mata Addu'ar Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lpy yasa nan da nine months su sha suna Fatuu dai nata dariya daga baya sukai sallama. Cikin parlon Fauzy ta koma ta zauna kusa da Aunty Mareeya nan suka dasa hirar farinciki Fauzy na fad'in ita wllh dama ranta ya bata shima yana son Zarah bawan Allah ashe ma ya fita shiga hali.

Saida aka gama sallar isha Haisam ya dawo yace mata ta shirya suje part d'in Hajiya suci Abinci tace to, k'ananun kaya skinny jeans da riga wadda ta hau da shi ta fiddo, yana kwance saman gado ya jingina da headboard yana kallonta ta fara shiryawa, tana yi suna sakar ma juna murmushi in tazo kan abunda take jin kunya sai ta duk'e k'asa a haka har ta gama sakawa ta nufi gaban mirror tana gyara parking d'in gashinta, kasa jurewa Haisam yayi ya saukko daga gadon Slowly ya nufe ta, ba zato taji ya rungumota ta baya har saida ta d'an yi firgit, hannu ya kai ya janye gashinta data baza shi tana sharcewa fuskar shi da ya d'aura akan shoulder d'inta ta bayyana, murmushi suka shiga sakar ma juna ya d'an lumshe ido ya furta mata "Baby you're very beautiful" itama Lumshe mashi ido tay itama ta furta "Hubby you're very Handsome man" gaba d'aya sukai murmushi, hannuwan shi yasa yana bin shape d'in jikinta tamkar yana zana ta, d'an runtse ido da mak'e kafad'a Fatuu ta shiga yi, ganin bai da niyyar dainawa yasa tace mashi zai hanata ta gama shiryawa su tafi, juyota yay ya kai hannu ya fara k'ok'arin yi mata parking d'in gashin, suna haka take ce mashi wai a da can da ya fara saninta yana ganin kyaun ta, shiru yay yana d'an murmushi kafin yace bazai iya ganewa ba kawai dai yasan komai nata na burge shi, bayan ya gama d'aure mata gashin d'ago da ita yay ya d'aura ta akan k'afafun shi yadda ta d'an k'ara tsawo hannuwan shi tallafe da waist d'in ta itama ta zagayo da nata hannuwan ta bayan shi, bin juna sukai da wani irin azababben kallo kowa K'ok'arin nuna irin k'aunar dayake ma d'an uwan shi yake ta cikin kallon, As they held each other close, their bodies seemed to melt together like two puzzle pieces that were made for each other, Fatuu ce ta sare ta rufe fuskar ta a jikinshi idonta a lumshe can k'asan mak'oshi taji ya furta yana son ta itace best thing d'aya ta6a faruwa dashi tana mak'ale dashi ta furta mashi itama haka, d'agota yay suna sakar ma juna murmushi yace suje tace bari ta d'aura After dress, bayan ta d'aukko ta saka tayi rolling veil d'in ya kama hannunta suka tafi.

Wuraren k'arfe goma da rabi lokacin basu dad'e da dawowa ba suna zaune a parlorn su suna kallon American film Fatuu ta cire after dress d'in tana mak'ale jikinshi kamar yar mage sai shak'ar k'amshin juna suke, d'aga kai tayi ta kalle shi tace mashi gobe zata je school, shiru ya d'an yi yana kallonta kafin yace bazata bari ta huta ba, a d'an shagwabe tace mashi Exams d'in su ta taho fa Upper week zasu fara bata son ayi wani abun bata nan kuma ma test ake ta masu, jinjina mata kai yay suka cigaba da kallon, bayan wani d'an lokaci taji ya fara magana ta k'ara d'aga kai tana kallon shi, shima kallon ta yake yace mata jibi Fanan zata tafi Lagos yana son zasu rakata, jimm Fatuu tay tana kallon shi ba tare data ce mashi komai ba hakanan sai taji bata son zuwa duk da bazata so ya tafi ya barta ba, ganin tayi shiru yasa shi tambayarta ko bazata rakata ba, da alamun yar damuwa tace ba wai bata son zuwa ba kawae dai bata son wani abu ya faru in taje gidan su, shiru ya d'an yi yana nazarin Maganar tata can yace mata Shikenan sai su sauka a Hotel kawai, bin shi da ido Fatuu tayi don hakan ma bata ji ya kwanta mata ba gani tay in suka yi haka kuma ai kaman ba'a kyauta ma Fanan d'in ba anan suna tare kuma acan ma su ware duk da bata san ya suka tsara da ita ba game da kwanakin da zaiyi da ita ba,

tambayar shi tay kwana nawa zasu yi yace just 2 days, sauke idanunta tayi ta shiga tunanin tunda ba dad'ewa zai yi ba kodai ta k'i bin shi don k'arshen ta hakan ba komai zai k'ara mata ba face bak'in jini a wurin su Hajiya Maryam in dai suka san da ita yaje kuma ya sauka da ita a Hotel tunda dai tasan ai k'ilan duk in suka je da Fanan a gidansu suke sauka, tana haka taji ya tambayi koda wani matsalan ne, kallon shi tay ta d'an girgiza mashi kai kafin a sanyaye tace tana jin saidai yaje ya dawo don a jibin tana da test, shiru ya d'an yi sai kuma yace Ok bari a d'aga tafiyar sai bata da test d'in da sauri tace "Ai Hubby daga jibin fa kusan kullum sai munyi don upper Wednesday zamu fara exam, tunda just 2 days ne ka rakata kawai" shiru yay yana kallonta sai d'an yamutsa fuska take, sam ba haka ya so ba don a yadda ya tsara tare zasu, ganin yanayin shi yasa ta kai hannu tana shafa kwantacciyar sumar sajen shi cikin nuna damuwa tace "You shouldn't worry pls" d'an murmushi yay ya lumshe mata ido, cigaba da shafa beard d'in tayi shi kuma yaci gaba da kallon yana yi yana maido idon kanta, k'arfe 11 na yi yace suje su kwanta tunda zata school suka mik'e a tare yana ruk'e da hannunta sai kace k'anwar shi, bayan ya kashe kayan kallon ya rage hasken Parlon suka nufi Bedroom yana tallafe da ita.

Washe gari bayan ta gama shiryawa tare suka fito da shi zai kaita, saida suka tsaya suka d'auki Mino sannan suka wuce, Mino aka fara ajewa suka wuce, a inda ya saba ajeta nan yayi packing ta kalle shi tana murmushi tayi mashi godiya tana niyyar juyawa ta bud'e kopar taji ya ruk'o hannunta ta juyo ta kalle shi, idanun shi a d'an lumshe ya jingina kanshi jikin headrest, tana kallon shi ta fahimci ruk'on kona miye tay mashi nuni da lip glow d'in da ta shafa ya ida lumshe idon, matsawa tay wurin shi ta kai baki ta manna mashi kiss a kumatun shi tana niyyar janye fuskar ya ruk'o kan, lokacin daya saketa gaba d'aya ba lip glow d'in, komawa tay ta zauna itama ta jingina kanta da kujerar tana breathing rapidly haka shima, bayan sun natsu ya tambayi tana tare da Atm d'inta ta d'aga mashi kai yace ok zai tura mata kud'i ta tabbatar taci Abinci mai kyau ta k'oshi nan ma kai ta d'aga mashi suna kallon cikin idanun juna, har zata juya taji yace ko ya kawo mata Abincin da break, da sauri ta girgiza mashi kai tace a'a ai anan akwae Abinci mai kyau zata ci.

A class ta iske Fauzy don da wuri tazo Saboda zumud'in ganin Fatun, tana shiga ta taso da gudu tazo ta rungume ta cike da Farinciki itama Fatun sai dariya take, bayan sun je sun zauna gaba d'aya Fauzy ta kafeta da ido tana ta washe baki sai kace wadda aka ma Albishir mai dad'i tama kasa Magana, Fatuu na dariya tace "wai sai kallo na kike sai kace yau kika fara ganina" yarfa hannu tay tace "bazaki gane irin farincikin da nike ji ba wllh don abu ne da ban yi zaton shi kusa ba, kinga wai yadda kika canza cikin kwana biyu kacal har fa wani glowing kike wllh ga k'amshin amarci, koda yake dama fa irin su Ya Haisam ba dai iya zuba ruwan love ba wllh kina ganin su shiru shiru sai hum....." dariya kawae Fatuu take ta kasa cewa komai itama Fauzyn dariyar take can tace "k'awata kukan ya Haisam bai damu da ni ba bai sona ya k'are ko" bugu Fatuu ta kai mata tana fad'in "leave me alone Fauzy" gaba d'aya dariya suke a haka malamin su ya shigo, tun bayan da malamin ya fara masu bayani Fauzy na lura da Fatuu sai faman sakin murmushi take da gani ba K'aramin nishad'i take ciki ba, sai da akai break sun fito take ce mata ita wannan Amarcin anya ma zai bari tayi wani karatun Exams Malam na explanation tana sakin murmushi inaga in jarabawar tazo kar ta kai fa in aka tambayi zane ta zana Ya Haisam, sosae Fatuu ke dariya suka nufi inda zasu ci Abinci.
Chapter 14 · 0% Book details