← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 211

Sashe 145

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ko Dr Fanan zata iya d'aura su kan hakan, yana yin Maganar da sauri Fanan ta kalle shi zuciyarta ta shiga harbawa don bata jin da hannunta zata taimaka ayi abortion ga wata ma balle kuma wannan, Haisam ne yace ma Doctor ɗin a bata maganin kawai ya furta Ok yana k'ok'arin tashi a ruɗe Fatuu ta kalli Haisam tare da girgiza mashi kai tace "a'a Hubby a barshi kawai kar a cire ana iya zuwa kuma a samu matsala tunda Allah ya bamu kawai mu barshi muyi fatan ya zama Alkhairi kada mu cire kuma muzo daga baya muna so Allah yak'i bamu wasu ma da yawa suna nema basu samu ba" yanayin yadda ta k'are Maganar kamar zata yi kuka, shiru Haisam d'in yay idon shi akanta wani irin tausayinta yake ji na ratsa shi dama dalilin tausayin nata yasa yace a cire ba wai don bai son cikin ba, Maganar k'arshe da Fatuu tay ita ta ƙara karya ma Fanan zuciya har bata san idanunta sun ciko da kwalla ba saidai ji tayi sun zubo da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, duk yadda taso kar tayi kuka abun yaci tura, jin sheshshekarta a hankali yasa su kallonta da sauri ganin yanayinta yasa Fatuu kiran sunanta ta amsa cikin Muryar kuka ba tare da ta d'ago ba aikuwa zumbur ta mik'e ta nufeta, a gabanta ta tsaya tasa hannu tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta, bin fuskar Fanan da tayi sharkaf da hawaye tay da d'an rud'ewa ta hau tambayar "Aunty Fanan what happened? Miya sa kike kuka don Allah?" Girgiza mata kai tayi kafin cikin kuka tace mata ba komai, shiru Fatuu tay tana yamutsa fuska itama kamar zata yi kuka ta shiga tunanin miya sa Fanan d'in kuka lokaci guda zuciyarta ta tariyo mata da Maganar da tayi, waro ido Fatuu tay tare da ɗan buɗa baki da sauri ta shiga faɗin "Aunty Fanan wllh ba dake nike ba da nayi Maganar kawai na bashi misali ne ban san abun zai ta6a maki zuciya ba don Allah kiyi haƙuri" idanunta har sun ciko da ƙwalla, girgiza mata kai tayi tace "No Zarah, baki man laifi ba ai abunda kika faɗa gaskiya ne kuma ni ai nasan ba dani kike ba Saboda ni inada yara ko?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tare da kai hannu ta fara goge mata ƙwallan Fanan ɗin na ɗan murmushi, bayan ta gama goge mata hawayen ta tambayeta itama bata son a fitar da cikin ko farko shiru Fanan ɗin tayi kafin ta ɗan jinjina mata kai alamar eh, juyawa tayi ta kalli Haisam cikin harshen turanci tace mashi Auny Fanan ma bata so don haka koda ita bata son cikin to zata haƙura ta haife shi, murmushi yay tare da ɗan lumshe ido haka ma likitan don yanzu ya fahimci komai da bai gane abunda ke faruwa ba saboda da Hausa suke Maganar sai jefi jefi suke saka turanci, kama hannunta Fanan tay ta d'an girgiza mata kai tace duk da bata ta6a haihuwa ba tasan tun daga rainon ciki akwae wahala in dai itama taji tana son a cire d'in kada Saboda ita ta canza ra'ayi Fatun tace a'a da gaske bata son a cire har cikin ranta ta amince a bar mata suyi mata Addu'a Allah yasa kada ta sha wahala kuma ta haife shi lafiya Fanan na murmushi tace in sha Allah daga yanzu ta fara mata Addu'a kan hakan har zuwa ta haihu ta kalli Haisam dake kallon su fuskarshi a sake tace daga yanzu su fara mata Addu'a ya jinjina kai, tattaunawa Fanan ta shiga yi da Doctor kan maganin daya kamata a bata wanda zai sa ta daina amai ta rinka cin Abinci haka su twins ma suma za'a basu wanda zai k'ara inganta lafiyar su Haisam ya tambayi yanzu zata iya cigaba da breastfeeding nasu doctor din yace k'warae ba wani abu taci gaba da basu koda har zuwa ta haihu ne kuma a rinƙa basu maganin da zai basu yay mashi godiya.
Chapter 145 · 0% Book details