← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 211

Sashe 30

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Fatuu ta koma d'akin Jidderh wayarta ta d'auka ta hau online, sakonni na fara shigowa sai ga sak'on Haulat da sauri ta shiga voice note ne ta turo mata, bud'ewa tay ta fara saurara cike da farinciki take sanar da ita an barta zata zo, sosae Fatuu taji dad'i don tasan Haulat mai kaunarta ce kuma tana ganin komai ya faru da ita hada silarta, fita tayi daga cikin WhatsApp d'in ta fara k'ok'arin kiran Abbas bayan ya d'aga ta gaishe dashi ya amsa yana fad'in Amaryar su an je lafiya ta amsa mashi da lafiya lou, jin ta yi shiru yasa shi tambayarta ko da Wani abu da yar in ina tace dama so take ta tambaye shi yaushe zasu zo yace mata ranar laraba in Allah ya kaimu, k'ara tambayar koda wani abu yayi jin ta k'ara yin shiru tace eh dama don Allah k'awarta ce Haulat zata zo daga Nijar shine take son in ba matsala tazo nan sai a taho da ita, yana murmushi yace "an gama Amarya ai umarni kawai zaki bada bawai ki rok'a ba koda ba Mota da anyi ma Angon naki magana zai iya turowa a d'auketa koda ita kad'ai ce don na lura yanzu ke kike control d'in heart d'in shi" waro ido tay tasa hannu ta rufe baki sai kuma ta cire tana fad'in don Allah ya rufa mata Asiri kar Aunty Fanan taji dariya kawae yayi yace Shikenan dai abar Maganar, bayan sun gama wayar WhatsApp ta koma ta tura ma Haulat sakon voice note ta sanar da ita su gwaggo ranar laraba zasu taho tayi magana taje can sai a taho da ita, bayan ta tura mata sake fita tayi ta kira Fauzy suka gaisa Fauzyn tace ai ta kirata d'azun bata d'aga ba tace eh bata kusa ne, Maganar anko tayi mata tace ai Ya Haisam yayi masu harda Aunty Mareeya su turo measurements d'in su yanzu in sun gama wayar, wata irin k'arar murna Fauzy ta saka ta hau shi ma Haisam Albarka tana Addu'ar Allah ya k'ara mashi Arziki mai Albarka, Fatuu na jinta ta hau kwala ma Aunty Mareeya kira tana fad'in anyi masu anko wllh Fatuu sai dariya take, sanar da ita tay sunyi waya da Ya Abbas yanzu yace ranar laraba zasu taho Fauzyn tace eh Aunty Mareeya ma sunyi Magana da Aunty Feenah ta sanar mata, hira suka cigaba da yi nan Fatuu ke ce mata zata yi ma Aunty zee mai kaya magana tana son taje ta amsar mata sak'o sai ta kai ma Kb tailor Fauzyn tace to tana jira daga baya sukai sallama.

Gwaggo suna gama waya da Abbas ta kira Baffan Fatuu bayan sun gama gaisawa tayi mashi zancen zuwa a d'auke su sosae yaji dad'i shima ya hau godiya nan cikin hikima ta nuna mashi ba gayya za'ai ba ya za6i wanda zasu je tunda ba irin bikin nan bane yace in sha Allahu za'a yi hakan daga baya suka yi sallama, d'akin yadikko ya nufa ya Sanar mata nan ta hau murna har Fuskarta ta kasa 6oyewa, tare da ita suka tsara yadda za'a fad'i ma Ard'o da kuma wad'anda yakamata suje.

Shirye shirye sun kan kama a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah ranar laraba Abbas ya taho da Aunty Mareeya da Feenah, Abdul sai Haulat da Mino sai Tk kuma ya taho da Amadu da Fauzy sai Aunty Saude harda Zainab Muhammadu k'awar su da Fatuu tasa Fauzy ta taho da ita don ta matsa tana son zuwa, lokacin da suka iso Sosae Fatuu tay farinciki kamar zata zuba ruwa a k'asa tasha yayin da su kuma wad'anda basu ta6a zuwa ba Al'ajabi ne ya kama su ganin irin d'aular da su Haisam suke ciki har fuskokin wasu sun k'asa boye Al'ajabin, a parlor aka tarbesu ana masu sannu da hanya Hajiya da Mom da Aunty dasu Laila duk sun fito cikin parlon anata gaishe gaishe a mutunce can sai ga Nameer ma ya shigo cikin parlon tarbar Abokin shi Amadu, yana ganin shi ya mik'e ya bashi hannu suka gaisa Nameer d'in yayi mashi an zo lafiya ya amsa yanata washe baki, matsawa yay wurin Tk shima suka gaisa ya zauna daga gefen shi, bin sauran Mutanen yay suka gaisa Aunty Mareeya na Fad'in ga mai kama da mijin Zarah duk akayi murmushi, tunda ya d'aura idon shi akan Mino ya bita da kallon k'urulla don yana ganinta ya gane yar uwar Fatuu ce, duk in Mino ta d'ago sai taga ita yake kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ta fara yan kame kame kawae sai gani tay ya sakar mata murmushi har bata san lokacin data mayar mashi ba, bayan an gama gaisawa aka kira wasu daga cikin ma'aikatan da aka k'ara d'auka Saboda hidimar suka yi masu jagora inda zasu sauka, Mino na tafiya tana waiwayen Nameer da ya nufi bene dasu Amadu da Tk zai kai su part d'in shi shima waiwayen nata yake suna niyyar shigewa kopar da zata kai su baya ya d'ago mata hannu tay yar dariya, wani duplex ne a bayan gidan can wurin inda babban Kitchen yake nan aka kai su, ginin part biyu gare shi kowanne yana da babban parlor sai corridor guda biyu kowanne yana da d'akuna biyu da toilet, Fauzy da Haulat da Mino da Zainab Muhammadu d'aki guda suka shiga akwae gado da mirror sai wardrobe din bango kowanne d'aki haka yake tsaf an gyara, Feenah da Aunty Mareeya da Saude suma d'aki d'aya suka shiga ita gwaggo Hajiya taja ta d'akinta wai ta bar ma yara can, bada jimawa ba aka fara shigo masu da Abinci da abubuwan sha wasu suka fara yin salla wasu kuma suka fara cin Abincin,

"Kai! Ashe dai bamu ga komai ba a kud'in su Mijin Zarah, wannan d'aula haka! Kuma fa kina iya ganin ba iya shine gidan su ba anan Abuja d'in" Aunty Mareeya ce dake cin Abinci tayi zaman cin tuwo asaman carpet tayi Maganar, jinjina kai Feenah tayi tace suna fa da kud'i bana wasa ba, Aunty Saude ce tace "aikuwa bashi kad'ai bane gidan su anan, Senator fa yana da kud'i sosae mutumin da keda gidajen mai da kamfanoni daban daban ba a iya Nigeria kad'ai ba ga gidajen haya ko anan Abujar yana da manyan estate guda biyu da ake haya harda babbar plaza ko a Katsina ma yana da gidajen haya da filaye, Unguwar da Hajiya take fa kusan duk filayen shi ne aka saida ma mutane" jinjina kai Aunty Mareeya ta hau yi cike da Al'ajabi tace "tabb kice dai ba K'aramin mai kud'i bane, wllh wasu masu kud'in sai inta mamakin yadda suke tara dukiya" dariya Saude tayi tace "shi kinga gaskiya harda wanda ya gada a wurin mahaifinshi duk da Soja ne yana da tarin dukiya don ko kamfanonin Motocin Senator yawanci asali na mahaifin shi ne, kuma kinsan ita dukiya in dai zaka tsare hakkin Allah ka rink'a kyauta da sadaqa to lillinkuwa take" cike da gamsuwa gaba d'aya suka ce tabbas haka ne kowa zai shaide su da hakan, haka suka cigaba da yin hirar su.

Fatuu ma cikin su Fauzy ta zauna wani irin dad'i take ji sai murmushi take suna ta tsokanarta, bayan sun gama cin Abincin ne Fauzy ta bud'e jakar kayanta ta fiddo d'inkin da ta amso mata a wurin Kb, bud'e kayan Fatuu tay tana dubawa doguwar riga ce akayi gaba d'aya mix and match d'in da lace d'in duk sun yi kyau sosae sai kuma na k'annanta su Aysha suma duk dogayen riguna akai masu, Fatuu na murmushi ta mik'a ma Haulat kayan tace ankon ta ne, waro ido Haulat tayi haka ma Fauzy don ita bata yi tunanin sune ankon ba, kasa cewa komai Haulat tayi da mamaki Fauzy tace "wai dama sune ankon?" Kai Fatuu ta d'aga mata ta k'ara cewa "amman dai da gani zasu yi kud'i sosae" bayanin kud'in su tay mata gaba d'aya suka k'ara zaro ido da yanayin damuwa Haulat tace to maimakon tayi mata Mara kud'in sosae sai ta takura kanta tayi mata mai kud'i haka Fatuu na dariya tace ai ba takura kai bane tana da su ne kuma duk ita akayi sai full embroidery d'in, sosae Haulat ta hau yi mata godiya har kamar zata yi kuka Fatun ta kai hannu ta rungumo ta tana fad'in ai tafi k'arfin wannan a wurin ta, Zainab Muhammadu ce tace don dai lokaci ya k'ure itama da tayi ko normal Chiganvy gold d'in ce Fatuu tace bata san zata zo ba sai daga baya da itama anyi mata gashi yanzu lokaci ya k'ure ace a kawo har akai dinki masu yin d'inkunan ma aiki ya masu yawa don na su Fauzy ma ba'a kaiga gamawa ba da kuma nata zasu yi mata data bata tana murmushi tace ba komai tasa wasu kawai.
Chapter 30 · 0% Book details