← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 211

Sashe 19

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa Fanan ta rungume Farha tana k'ara yi mata godiyar fahimtar ta da tayi, bayan ta saketa Farhar na d'an murmushi tace mata "We're blood sisters" Fanan d'in tace hakane, kowa d'akin shi ya nufa. Bayan Fanan ta gama yin sallar Magrib d'aga hannu tayi tana k'walla ta shiga rok'on Allah akan kada yasa Maganar da Mom d'in ta tayi d'azun ta tabbata, Allah yasa kada Ya Haisam ya juya mata baya ya had'a kan su ita da Zarah, sosae tayi Addu'oi bayan ta shafa zaune tay saman prayer mat d'in ta kwantar da kanta a jikin gado tana tunane tunane, Wayarta ce ta fara yin ringing ta juya ta kallo ta a saman gadon kafin ta mik'a hannu ta d'aukko, ganin Haisam ne mai kiran yasa ta saki murmushi tay picking, gaida shi tayi ya amsa ta tambayi ya isa yace mata eh ya bari yayi salla ne sai suyi magana, an isa lafiya tayi mashi yace mata lafiya lou ta tambayi yadda ya iske kowa, jin yanayin voice d'inta ta d'an disashe yasa ya tambayi ko wani abu na damunta ne, tana d'an murmushi tace mashi eh cike da kulawa ya tambayi abunda ke damuntan tana d'an murmushi tace mashi missing d'in shi, shima murmushin yayi yace mata ai saida yace ta bari ba yanzu ba ta tafi ta k'iya, ita dai murmushi kawai tayi don baisan ba K'aramin k'arfin hali take ba zaman ta a gidan Hajiya tana ganin shi yana kwana da wata, rarrashinta yayi yace ai bada jimawa ba zai dawo, sosae ya kwantar mata da hankali cikin salon nuna kauna kafin daga baya sukai sallama,

*ABUJA NIGERIA*

Bayan sallar isha iyalan Senator suka zauna cin Abincin dare harda Haisam da tuni ya isa, ba laifi Haisam yaci sosae har Senator na mashi tsiyar dama yanzu in bai rink'a cin Abinci ba Sosae sai ya rink'a fad'uwa Saboda figewa zai yi su Aunty da Mom sukai yar dariya don sun fahimci dalilin daya sa ya fad'i hakan, shima Haisam d'in murmushi kawai yayi, bayan sun gama gaba d'aya cikin parlon suka koma duk suka zazzauna kusan kowa na nan banda Mutum biyu Laila da Nameer duk basu K'asar suna Makaranta, Mom d'in su ce ta fara yin magana tace ma Haisam d'in sun ji dadin yadda Fanan ta amince bata tashi hankalin ta ba Senator ma ya karba yace sosae Daughter ta burge shi Allah ya had'a kan su duk suka amsa da Amin Aunty ma ta yaba mata tace tayi namijin k'ok'ari gaskiya, yar Nasiha Senator yayi mashi kan yin Adalci a tsakanin su, bayan ya gama Jidderh tace to yanzu ai sai a kawo Fatuu nan ayi shagulgulan biki ko, shiru Haisam d'in yay kawae Fuskar shi a sake ganin baice komai ba yasa a shagwabe Jidderh tace "Big bro talk pls, yaushe zaka kawo ta sai mu tsara programs da zamu yi" d'an murmushi yay ya girgiza mata kai kafin slowly ya furta ba sai anyi wannan ba tunda an wuce wurin, tura baki tay a shagwabe tace gaskiya basu yarda ba su suna so ya za'a ce ayi Auren ba wani celebration, Aunty ce itama tace gaskiya ya kamata ayi koda bada yawa ba Saboda she needs to be introduced as one of the Family tunda duk ba'a san da Auren ba, Mom d'in shi ma ta goyi bayan ayin ba yadda Haisam ya iya don an fi k'arfin shi yace su tsara abunda suke son yi, nan suka shiga tattauna abunda yakamata ayi Jidderh sai lissafo abubuwa take cike da zumud'i, Senator ne yasa baki yace tunda ba yanzu aka yi Auren ba yana ganin ba sai an yi abubuwa ba sosae dama ya lura Angon kamar bai so ko don kar a kalle mashi mata ne ko kuma kar a wahalar da ita oho gaba d'aya sukai dariya shima Haisam d'in murmushi yayi, k'arshe dai abu biyu suka yanke zasu yi Walima wadda zata kama ranar Friday ayi kaman yinin biki sai washe gari ayi Dinner party, ita Jidderh hakan bai isheta ba sai yamutsa fuska take tana shagwabar gaskiya a k'ara ita kenan Sis Zarah d'in baza ayi Ethiopian Night ba dasu Arabian Mom d'in su na yar dariya tace tayi hak'uri a barshi hakan,

"Yanzu sai Maganar lefe ko, shi banji anyi Maganar shi ba" Senator ne yayi Maganar, Aunty tace "Eh nima ina niyyar yin Maganar shi" Mom d'in su ce ta kalli Haisam tace ya za'ayi lefen, yana a d'an kishingid'e yace suyi yadda ya kamata, Aunty tace "dama k'awata Hajiya Sakeena yanzu haka tana Dubai ina ganin duk abunda ake so za'a iya tura mata in sha Allahu nasan zata yi komai yadda ake so ta aiko batare da 6ata lokaci ba in ma ba yanzu zata dawo ba, sannan ga Zee Collections ma itama za'a iya yi mata magana sai a za6i abubuwan da ake so ta aiko da su" sosae hakan yayi ma kowa nan suka shiga tattaunawa kan yawan akwatunan da za'ayi kowa na fad'in yadda yake ganin yakamata Jidderh tafi kowa fad'in masu yawa a hakikance take fad'in Sis Fatun fa big girl ce gaskiya ayi mata masu yawa har saida Senator yasa baki yana yar dariya yace ya lura dai tana ji da wannan sabuwar Yayar tata, bayan sun gama yanke yawan akwatunan da za'ayi Aunty ta tambayi Haisam lokacin da zai kawota don ai fixing date da za'ai programs d'in, sanar dasu yay zata fara Exams ne next week kuma bai san date d'in da zasu gama ba sai dai ya tambaye ta tace Ok, daga baya suka shiga tattauna ankon da zasu yi Jidderh tace yakamata a kira Aunty Laila ta za6a tunda tasan takan gayu sosae duk suka yi dariya su Yasmeen da twins sai murna suke za'a sake yin biki a gidan, Haisam ne ya tambayi Shikenan ko akwae wani abu Mom d'in shi tace in aka gama tsara komai za'a mashi magana ya furta Ok daga haka ya mik'e yay masu saida safe Senator na dariya yace "halan Amarya tayi kira" faffad'an murmushi Haisam d'in yay ya mik'a mashi hannu Senator d'in ya dunkule na shi ya buga mashi ya wuce ya nufi upstairs yana murmushi duk suka bi shi da ido su Mom d'in suma dariya suke, gaba d'aya sun lura da canzawar da Haisam d'in yayi tun bayan da yazo yayi wani irin Fresh daka gan shi kasan yana cikin nishad'i, yana shiga part d'in nashi bedroom ya wuce har zai kira Fatuu sai kuma yayi tunanin ya fara yin wanka sai ya kwanta gaba d'aya ya nufi toilet, within 30 minutes ya gama shiryawa cikin sleeping dress, a bakin gado ya zauna ya kai hannu ya d'aukko wayarshi dake ajiye a gefe, Fatuu ya kira lokacin suna a parlor ita da Mino suna yin kallo basu dad'e da dawowa daga part d'in Hajiya ba, bayan tayi picking ya sanar da ita zasu yi Video call cike da Farinciki tace mashi to, dama tunda ya tafi sau d'aya sukai Vedio call d'in sai dai suna yin waya akai akai, mik'ewa tayi tace ma Mino in ta gama ta kashe kayan kallon ta nufi hanyar Bedroom da sauri...

Next Day......

Washe gari Friday bayan sun gama shirin Makaranta harda Mino ma anan ta shirya suka nufi parking space. Lokacin da akai ma su Fatuu break ganin tayi zaune yasa Fauzy ce mata ta taso suje su yi break kawae sai ta fad'a jikinta a shagwabe tace "Wayyo Fauzy miji na, don Allah ya dawo wllh ina kewar shi" dariya Fauzy ta sa dama kullum sai tayi mata magana akan mijin nata tace "to mai miji kiyi hakuri zai dawo ai" d'agowa Fatuu tay tana dariya itama, Fauzyn ta k'ara cewa "da alama dai Magana ta zata tabbata in exams tazo inaga labarin mijin ki zaki rink'a rubutawa banda zana shi dana ce" lumshe ido Fatuu tay tare da langa6ar da kai hannunta dafe da k'irji Fauzy ta kai hannu ta 6aka mata bugu a shoulder, bud'e idon Fatuu tay tana dariya tace "Fauzy ina rok'on Allah ya baki miji wanda ya iya buga love irin Ya Haisam wato gaba d'aya jin ki zaki rink'a yi a wata duniya ta daban kina rayuwa mai cike da nishad'i" sosae Fauzy ke dariya tace "na lura dai giyar soyayyar Ya Haisam na bugar dake sosae da alama Maganar Aunty Mareeya akan ki ta faru wato ke kika zaucen kullum baki da magana sai ta mijin ki" cigaba da dariya Fatun tayi Fauzy ta k'ara cewa "Wai ni anya ma kina karatun jarabawa kuwa sosae a gida?" Kashe mata ido tay a hankali ta furta soyayya bata bari, jinjina kai Fauzy tay tana dariya tay yar k'wafa tace sai ki rinka rubuta hakan ai a jarabawar, da kuwa an kad'a k'eyar ki, murmura idanu tay tace "ba Shikenan bama sai inje in ta shan soyayya ta da hujja in muka gama soyewa har muka kone bayan mun koma US sai in yi karatun" dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in ina Magana kuma in aka k'one itama Fatun dariyar take Fauzy ta mik'e tana fad'in ta taso suyi sauri su dawo su k'ara duba book kafin a shigo yi masu Test d'in da zasu yi tace to ta mik'e.
Chapter 19 · 0% Book details