← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 211

Sashe 140

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce mata tayi to ta d'an kwanta aga zuwa d'an anjima k'ilan a kawo masu breakfast da wuri ta d'aga mata kai ta fara k'ok'arin hawa gado ta kwanta Auntyn na k'ara yi mata sannu sosae take jin tausayinta don tasan dole ma taji jiki, bayan ta kwanta itama Aunty Mareeyar kwanciya tayi basu dad'e ba da kwanciyar akai sallama bakin k'opa Aunty ta d'ago kai tana bada izinin a shigo, wata yar dattijuwar mata ce ta shigo tana ruke da wani had'addan basket sai k'yalli yake jikinta sanye da apron Aunty na ganinta ta mik'e zaune, nufo ta tayi da murmushi ta gaishe da ita ta amsa mata itama tana murmushin tace dama Yalla6ai Sameer ne yace ta kawo ma Amarya Aunty tace to ta tashi tsaye ta kar6a, kafin matar ta tafi ta nuna mata magunguna dake ciki basket d'in tace hada su aka ce ta kawo ta sake cewa sai kuma wannan ta Mik'o mata wayar Fauzyn, amsa tayi tay mata godiya Matar ta tambayi da wani abu Aunty tace mata a'a ta k'ara mata godiya ta juya ta tafi, nufar side drawer tayi ta d'aura kwandon kafin ta shiga bud'e had'add'un Warmers d'in dake ciki, d'aya farfesun kaza ne yaji kayan k'amshi gwanin kyau a ido, bayan ta rufe ta bud'e d'ayar soyayyen dankalin turawa ne da dafaffun k'wai sai kuma Flask wanda da gani set ne da Warmers d'in nan tea ne da yaji kayan k'amshi daga gefe akwae plates da cup sai cokulla sai Madara da milo da kwalin sugar, Murmushi Aunty ta shiga yi a fili ta furta "Su surukina kenan tunda fa an cuci yar mutane dole aita nan nan da ita" a ranta kuwa dad'i ne ya kamata don da alama komai ya kasance yadda take so, tashin Fauzy ta shiga yi bayan ta bud'e ido tace mata ta tashi ga Abinci nan Angonta ya aiko mata ta kamata ta tashi zaune, Fauzy taji dad'in Abincin dama a lokacin ta fara jin yunwar sosae, ba laifi ta ci sosae ba kamar kazar Aunty tasata tasha romon sosae, ganin tana ta ci yasa ta kalleta cikin d'an disashewar murya tace mata itama ta ci mana Aunty Mareeya tayi d'an murmushi tace ita dai ta ci ta k'oshi tukun don ta fita buk'ata, tana cikin ci sai ga kiran Sameer ya shigo Aunty ta d'auki wayar ganin shine tay d'an murmushi, picking tayi ta kara ma Fauzy a kunne shiru tay ta dakata da cin Abincin taji ya kirata da Babes d'an kallon Aunty tay data ruk'e mata wayar kafin can k'asan mak'oshi ta amsa, tambayar ta yay jikin a hankali tace mashi da Sauk'i yace ya manta bai sata ta zauna ruwan ba ta bashi amsa da tayi anan yace Ok sai kuma ya tambayi taci Abincin da aka kawo tace eh gashi nan tana ci yace Ok bari ya barta taci amman pls taci sosae sai tasha magani ta amsa da to ya katse kiran, bayan ta k'oshi ta bata magungunan tasha kafin ta koma ta kwanta sannan Aunty Mareeya itama ta zuba tana cikin ci Yaya Fareeda ta farka wai k'amshin abincin ne ya kai mata cikin bacci tama yi zaton Mafarki take Aunty tay dariya tace ango ne ya aiko ma amaryar shi shine take cin saura itama ta wanko baki tazo taci tace to. Wuraren k'arfe tara da rabi aka kawo masu breakfast lokacin Fauzy nata shan bacci tun bayan data ci Abinci, sanin ba yunwa take ji ba yasa Aunty bata tashe ta ba su Gwaggo nata tambayarta aka ce masu bacci take, bayan sun gama zama sukai anan falo suna kallo kafin zuwa k'arfe sha biyu suka fara shirin Walima don ana gama sallar Azahar za'ayi Saboda masu tafiya don gobe Monday, sosae Fauzy tasha bacci don saida Aunty ta tasheta Saboda shirin Walima kaman zata yi kuka tace ita dama an k'yaleta tayi kwanciyarta a d'aki Aunty tace ai tasan hakan bazai yuwuwa ba ta dai daure da anyi angama ai shikenan. Zuwa bayan Azahar kowa ya shirya Amarya Fauzy ansha rantsattsiyar shadda da ta sha ubansun aiki wuyanta da hannunta duk diamond ne, ba tare da 6ata lokaci ba aka shiga gudanar da Walimar data samu halartar manyan mata k'awayen su Her Excellency kowacce ka gani hamshakiyar kanta ce tsadaddun sutturu kawai kake gani kowa tayi shiga mai sunan shiga ansha gwalalai abundai sai wanda ya gani suma su Aunty ba laifi sun yi shiga mai kyau daidai k'arfin su, sai la'asar aka gama an ci an sha an kuma ba Fauzy kyaututtuka, ana gama Walimar su Mom sukai shirin tafiya harda yan Ethiopia zasu tafi can Abuja tare suma su Gwaggo suka ce tunda dai an gama mi suke jira akace Aunty tayi ma Her Excellency magana, koda tayi mata cewa tayi a'a yamma tayi su bari sai gobe da safe za'a maida su, sosae Fauzy taji dad'i da har ta shiga damuwa da suka ce zasu tafi, Fatuu ma da zata bi su Mom Aunty Mareeya ta rok'eta ta tsaya sai in zasu tafi koda ta kira Haisam ta sanar mashi cewa yay ba komai Allah ya kaimu, bayan gama Walimar ne aka kawo masu sauran akwatunan lefen Fauzy set biyu suma guda goma an narka uban kaya su Aunty suna ta jinjina yawan akwatunan har guda ashirin, bayan sun natsu ne Fauzy tace ma Aunty ta d'aukar masu kaya cikin lefen tunda dama wanda aka fara kaiwa ba'a d'auki komai ba don kayan duk a d'inke suke Fatuu ma tace mata ta d'auki abunda take so tace mata a'a ta bar shi aikuwa Fauzy tace in dai bata d'auka ba to tasan zaman da zata yi da ita wato ita ta amshi nata sai itace zata k'i amsar nata Fatuu na dariya tace to ai abun ba gasa bane ko kuma ita duka yaushe akai sunan su twins ta samu kaya sosae, duk da haka matsa mata Fauzy tayi sai ta d'auka k'arshe dai sai Aunty Mareeya ce ta d'aukar mata wasu abubuwan. Da daddare bayan sun yi shirin kwanciya Aunty tace ma Fauzy ta tafi wurin mijinta ta kwa6e fuska tace bazata je ba su Fatuu nata dariya ganin abun ya zamar masu drama Yaya Fareeda k'asa ta kwanta kan Carpet ganin gadon bazai ishe su ba don ga su twins. Washe gari bayan sunyi breakfast suka hau shirin tafiya gaba d'aya Fauzy duk tayi sukuku da ita, Misalin k'arfe sha d'aya na safe duk suka fito don tafiya Fauzy nata k'walla suna ta bata hak'uri Hajiya Zainab data rako su tana murmushi tace ma Fauzy nan ma ai gida ne ko, sha tara ta Arziki akai masu harda kud'i aka babbasu ganin da gaske tafiya zasu yi yasa Fauzy yin kuka sosae har ta karya ma Aunty Mareeya zuciya itama saida tayi k'wallan, aure kenan mai raba Y'a da uwa mai kuma raba dan'uwa da dan'uwa dole Aunty Mareeya taji kewar Fauzy don sun saba sosae, tana ji tana gani suka tafi suka barta sai fatan Allah ya kiyaye hanya ya kai su lafiya. Bayan tafiyar su Aunty part d'in Hajiya Zainab aka tafi da Fauzy anan Sameer ya sameta tana zaune a parlor ita kad'ai tana kallo saidai hankalin ta ba'a kan tv d'in yake ba damuwar tafiyar su Aunty ce a ranta yaran gidan duk sun tafi Makaranta da Amal ta zauna suna d'an yin hira jefi jefi don basu saba ba daga baya ta tashi don itama shirin barin K'asar take ta koma Makaranta dama bikin ne yasa ta zo, yana sanye cikin sabuwar farar shadda sai baza k'amshi yake ya zauna a kujerar gefenta, a sanyaye ta gaishe shi ya amsa yanata kallonta ganin yanayinta yasa a hankali ya tambayi ko har yanzu jikin nata su tafi hospital ta d'an girgiza mashi kai yace to ya ya ganta haka kaman abu na damunta tace mashi ba komai, shiru yay yana mata wani kallon ta kauda idonta can ya mik'e tare da kama hannunta yace suje, marairaice mashi tayi tace Momy ce ta taho da ita nan ya za'ai su tafi yace to sai ta zauna ita kadai tace ai tasan zata dawo sai kuma ta sameta bata nan, ce mata yay zai kirata ya sanar mata shi ya tafi da ita tana niyyar k'ara magana ya d'an d'aure fuska yace bai son gardama dole tayi shiru yana ruk'e da ita suka nufi barin falon, bayan sun fito ne ganin bata iya tafiyar sosae yasa hannu ya d'auketa gabanta sai fad'uwa yake kar wani ya gansu ahaka cikin sa'a har suka isa part d'in nashi basu had'u da kowa ba, bayan sunje a bakin gado ya d'aurata shima ya zauna ya kai hannu ya kamo nata yace ta fad'i mashi Mike damunta in ba ciwon bane, k'walla ne suka ciko mata cikin karyayyar murya tace mashi ba wani abu bane kawai ta damu da tafiyar da su Auntyn ta sukai ne tana yin Maganar k'wallan suka zubo mata sharr, jawota yay jikinshi ya sa hannu yana shafa bayanta alamar rarrashi can ya kai bakin shi saitin kunnanta yace mata ba gashi tare da ita ba miyasa zata damu, lamo tayi tana ta shak'ar daddad'an k'amshin shi mai narkar da zuciya, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin ya d'ago fuskar ta suka had'a ido nata sun d'an lumshe, tambayar ta yay jikin yana sauk'i ta d'aga mashi kai ya k'ara tambayarta ta zauna ruwan zafin yanzu tace mashi eh lokacin da tayi wanka da safe yace Ok bari a bari zuwa anjima sai ta k'ara a hankali tace to, bin juna sukai da kallo yanayin fuskar shi da d'an murmushi haka itama sun d'an d'auki lokaci haka jin bata iya jurewa yasa ta fad'a jikin shi tana d'an murmushi, kai bakin shi yay saitin kunnanta ya rad'a mata wata magana sai gashi ta d'ago da sauri tana kallon shi idanunta a d'an waje ya d'age mata gira, yamutsa fuska tayi idanunta sukai raurau alamar zata saka kuka kawai sai gani tay yay yar dariya har fararen hak'oran shi sun bayyana, maidota yay jikinshi ya rad'a mata he won't do it again until she've healed, murmushi ta shiga yi idanunta a rufe tana jin wani irin son
Chapter 140 · 0% Book details