← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 211

Sashe 164

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari misalin ƙarfe goma saura gaba ɗayan su sunyi wanka suna parlon Alhaji Lawal suna yin Breakfast tare Fatun na ruƙe da Abie Hajiya kuma na ruƙe da Adam ta samu yanzu ya yarda da ita dama shi in dai zaku wuni tare to zai fara yarda da kai, baka jin komai sai ƙarar cokulla sunyi nisa a cikin cin Abincin suka ji anyi sallama cikin parlon a kusan tare duk suka kalli entrance, wani irin bugu gaban Fatuu yay da tayi arba da wanda ya shigo ba kowa bane face Khalid yana sanye da ƙananun kaya idanunshi na sanye cikin farin glass irin nasu na likitoci har yanzu dai yana nan yadda yake bai yi ƙiba ba, da sauri ta kauda idonta daga barin kallonshi ya nufo dining area ɗin yana ta sakin ƙamshi, bayan ya ƙaraso a gefe ya tsaya kusa da Dad ɗinshi ya gaishe da shi ya amsa tare da ce mashi yazo lafiya da tambayar iyali duk ya amsa mashi kafin ya kai idon shi kan Hajiya yana ɗan murmushi ya furta "Mom, Good Morning" itama murmushin take ta amsa mashi tare da tambayar Matar shi da kuma ɗiyar shi Zarah ya amsa mata da suna lafiya suna gaishe ta, tace maimakon ya taho masu da Zarah still murmushi yake yace lokacin da zai taho bata tashi ba ta jinjina kai, a cikin ran Fatuu ta shiga maimaita sunan ɗiyar shi da aka faɗa tana kokonton dalilin saka sunan, Alhaji ne ya nuna mashi Haisam da idon shi na kan Abincin gabanshi kamar bai ma ji shigowar Khalid ɗin ba yace mashi "ga baƙon mu mijin ɗiyata Fateema" kai ya jinjina Alhaji ya kalli Haisam yace mashi ga babban ɗan shi Khalid su gaisa sai lokacin ya ɗago fuskar shi a sake kafin yace wani abu Khalid ya miƙa mashi hannu ya aje cokalin hannunshi shima ya bashi nashi suka gaisa yayi mashi anzo lafiya Haisam ya amsa mashi da lafiya lou, bayan sun gama gaisawar maida idon shi yay kan Fatuu da taki ɗago kai ta kalle shi ya furta "Fateema an zo lafiya" damm gabanta ya faɗi ta haɗiyi abu saida tay ƙoƙarin daidaita natsuwarta sannan ta ɗago tana yin ɗan ƙaƙalallen murmushi ta gaishe dashi da ƙyar ya amsa don saida gabanshi ya faɗi ganin yadda ta koma saidai bai bari an fahimci wani abu ba, tana gaishe dashi da sauri ta janye idonta daga kanshi, kallon Abie dake hannunta yay yace "Wannan yaran mu ne?" kafin ta bashi amsa Mom ɗin shi ta riga ce mashi eh twins ne ta nuna mashi Adam dake hannunta ya jinjina kai tare da kai hannu zai amshi Adam da yake Mom ɗin na kusa dashi Adam ɗin ya ƙanƙameta alamar bazai je ba Mom tace mashi suna yin ƙyuya ne sai sun saba da mutum suke yarda ya ɗaukeshi yana murmushi ya furta Ok, Dad ɗinshi ne ya nuna mashi seat da ba kowa yace yay joining nasu yasan ƙilan bai yi Breakfast ba tunda da wuri ya taho, gaba ɗaya Fatuu ta takura zaman Khalid a wurin da ƙyar take cin Abincin can ta saci kallon Haisam taga idon shi na kan Abincin gabanshi tana son ta gane yanayin fuskar shi amman ta kasa, Khalid bai daɗe da zama ba Haisam ya miƙe duk suka kalle shi Alhaji yace badai har ya ƙoshi ba yana murmushi yace mashi eh yace to amman ai kamar bai ci sosae ba still da yanayin murmushi ya bashi amsa da yaci da yawa Alhajin yace shikenan ya manta ma Yan gayu basu cin Abinci sosae Haisam ɗin yay yar dariya haka ma Hajiya Rabi'atu Khalid kuma murmushi yayi Fatuu kam bata ma ɗago ba balle aga yanayin fuskar ta, bayan tashin Haisam wurin duk sai taji ta ƙara takura sau biyu tana satar kallon Khalid taga ita yake kallo abunda bata sani ba dana sani kawai yake acikin ranshi don ganinta ya fama mashi babban tabon sonta dake cikin zuciyarshi sai kallon su twins yake yana raya ƙilan da yanzu su yaranshi ne, gaba ɗaya Abincin ya fice ma Fatuu arai haka shima Khalid ɗin ba don yana jin daɗin shi ba yake ci, Haisam bai daɗe ba da tashi itama ta miƙe Dad yace wato Romeo ya ƙoshi shine itama Juliet zata tashi Fatun tay yar dariya kafin tace ta ƙoshi ne, cikin parlon ta nufa inda Haisam ke zaune yana latsa waya, Bayan sun gama cin Abincin gaba ɗaya a falon aka zauna ana hira jefi jefi Haisam ke saka baki anan ma Fatuu ta lura da yadda Khalid ke fakaitar idanun mutane yana kallonta cikin sa'a bayan ɗan wani lokaci Abie yay bacci ta miƙe tace zata je ta kwantar dashi, bata daɗe da tafiya ba shima Adam yayi baccin Hajiya ta bita dashi ya rage saura Alhaji da Khalid sai Haisam suka cigaba da yin hira wadda yawanci akan aikin su ne suna cikin haka Haisam ya roƙi Khalid kan yana son ya shige ma su Baffan Fatuu gaba zasu kai Arɗo Asibitin da yake aiki a duba shi sosae yace mashi ba matsala, suna zaunen har lokacin sallar Azahar yayi Dad yace suje suyi kafin su tafi Haisam ya kira Fatuu a waya yace ta shirya da sun dawo daga salla zasu je can ruga suyi bankwana dasu sai su koma Yola ƙarfe biyar jirginsu zai tashi zuwa Abuja tace to, suna dawowa sallar ya sanar ma Dad zancen zuwa rugar yace Ok amman zasu dawo ta nan ko sai Driver ya kai su Yola ɗin Khalid na jin haka yace bari suje rugar tare sai ya duba jikin arɗon in sun dawo sai su wuce Yolar tunda shima komawa zaiyi Alhaji yace yauwa to hakan yayi, Part ɗin da aka sauke su Haisam ya wuce don ya shirya lokacin daya je Fatuu har ta gama shiryawa cikin doguwar rigar shadda ta saka sarƙa da yankunnan Diamond su twins ma ta saka masu ƙananun kaya iri ɗaya, yana shigowa ta nufeshi tana murmushi ya buɗe mata hannu yay hugging nata can ƙasan maƙoshi ya furta mata "I luv you with every single beat of My Heart Baby" lumshe ido tayi jin yadda hucin Maganar ya bugi kunnanta, shiru yay yana breathing a hankali can ta ɗago da fuskarta ta kalle shi sai taga kaman wani yanayi da bata sani ba akan fuskar shi, tambayar shi tayi ko da wani abu a hankali ya lumshe ido tare da ɗan girgiza mata kai daga haka yay pecking goshinta ya saketa yace bari yay wanka, juyawa yay ya nufi hanyar toilet tabi bayan shi da kallo can ta ɗan ɗaga murya tace "....Know dat am breathing because of you Hubby" dakatawa yay ya juyo yay mata murmushi itama shi tayi mashi kafin ya juya, zama tayi a bakin gado tay shiru kamar mai nazarin wani abu, bai daɗe ba ya fito sanin tafiya zasu yi ita ta taimaka mashi ya shirya yasa brown shaddar cikin wanda Alhaji ya kawo mashi sosae ta hau jikinshi ita ta ɗaura mashi agogo ta saka mashi links ta feshe shi da turare yanata mata murmushi, bayan sun gama shiryawa sun tattara komai suka fito kowa na ɗauke da yaro guda abun gwanin sha'awa, koda su Alhaji da Hajiya suka gansu saida suka yi santin kyaun da sukai Khalid dai murmushin karfin hali kawai yake shi kaɗai yasan mike faruwa a cikin zuciyarshi, har bakin Mota su Alhaji suka rako su sukai masu sai sun dawo, tunda suka hawo hanya Fatuu bata bari ta kalli saitin Khalid ba shi ke driving ɗin Haisam na a kujerar gefe ita kuma tana baya saitin kujerar Haisam, bai wuce sau ɗaya zuwa biyu ba sukai magana shida Haisam har suka iso, a tare gaba ɗaya suka je ɗakin Arɗon bayan sun gaishe shi Khalid ɗin ya shiga dadduba shi tare da yi mashi tambayoyi da fulatanci yana bashi amsa bayan ya gama ya faɗi ma su Baffan su Fatuu ranar da zasu kai shi asibitin suka ce to nan Haisam yayi mashi sallama da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa yana ta mashi godiya da saka mashi Albarka, wani ƙumshin leda yasa Baffa ya ɗaukko mashi yaba Fatuu yace ga magungunan nan ya faɗi mata yadda zata masu da yadda zata rinƙa ba su twins har itama yace tasha da Haisam sukai mashi godiya, bayan sun fito ƙopar gida Khalid ya koma su kuma suka nufi bangaren su Yadikko sai faman leƙowa ake ana kallon su, a parlor aka zazzauna suka shiga gaisawa bayan ɗan lokaci Haisam yayi ma Yadikko sallama tanata mashi godiya da saka albarka ya kai hannu aljihun rigarshi ya fiddo kuɗi masu yawa ya miƙa ma Baffa yace gashi a raba ma mutanen gidan sannan ya tambayi Account ɗin shi yace zai tura kuɗin da za'ai ma Arɗo amfani a Asibitin Baffan nata roƙonshi kan ya barshi za'a kai shi yana murmushi yace ba wani abu yayi niyya ne, kuɗi masu yawan gaske ya tura har saida Baffa ya jinjina kuɗin yace hidiman tayi yawa shidai ba komai kawae yake cewa, Godiya sosae sukai mashi ya miƙe yace ma Fatuu in ta gama yana waje Baffan ma ya miƙe suka fita tare, bayan fitar shi ne Yadikko ke mata tsegumin Khalid don taji dashi suka zo Fatuu ta faɗi mata yadda akai suka taho tare tace kuma Haisam bai nuna komai ba tace mata a'a, itama Fatun saida taba Yadikko kuɗi harda Baffanta ta bada ta bashi dasu Aysha sukaita Godiya ta ɗaukko mata wasu magunguna da zasu inganta lafiyar ta data cikin jikinta da kuma wanda zata samu sauƙin haihuwa ta faɗi mata yadda zatayi amfani dasu, tare da Yadikko suka zazzagaya yi ma sauran mutane sallama nan fa aka shiga ba su twins kyautar abubuwa su kaji, zabbi harda akuyoyi cikin wanda suka basu akoyoyi harda Yaya, duk Yadikko ta amsa tace zata kiwata masu kafin daga baya a aika masu tunda ba'a Mota zasu koma ba, bangaren su Yadikkon ƙwai masu yawa suka basu da uban dawon fura da Nono harda zuma mai yawa da man shanu duk akai masu dubara yadda ƙwan bazasu fashe ba haka Nonon ma harda ƙanƙara aka saka mashi
Chapter 164 · 0% Book details