Sashe 28
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Washe gari da Asuba suka tashi don yin salla, bayan Fatuu ta yo Alwala ta d'aura doguwar rigar bacci asaman kayan Jidderh ta shimfid'a masu prayer mat suka kabbara a tare, bayan sun gama kowa ya cire Hijab d'in jikin shi ya linke Jidderh ta maida su cikin wardrobe, gaida Fatuu dake tsaye Jidderh tayi tana murmushi Fatun tay shiru itama murmushin take duk sai taji nauyin gaidatan da tayi don ta girme mata, ta fahimci dalilin k'in amsawar tata tace mata ita fa yanzu Yayar suce har Yaya Laila ma, ganin tayi tsaye yasa tace mata ta hau gadon mana su k'ara yin bacci kafin lokacin breakfast don malamin su mai masu karatun safe yayi tafiya, harda tambayar Fatuu wai ko tana jin yunwa ta had'o mata wani abun Fatun ta girgiza mata kai, suna kwanciya bada jimawa ba wayar Jidderh ta hau ringing ta kai hannu kan side drawer ta d'aukko, saida ta duba mai kiran nata kafin tay picking shiru tay tana sauraren abunda ake fad'i mata kafin ta furta "a'a" sai kuma ta k'ara cewa "Okey" daga haka ta cire wayar daga kunnanta bayan ta maida ta inda ta d'aukko ta juya ta kalli Fatuu data juya mata baya ta kira Sunanta, amsa mata tayi ta juyo tana kallonta da d'an murmushi tace "dama Ya Haisam ne wai yana main parlor yace in raka ki wurin shi" d'an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce Jidderh na murmushi ta tashi ta zura k'afafunta k'asa, mik'ewa tay tana kallon Fatuu ganin bata saukko ba tace mata yana jira fa, saukkowa tayi tace ma Jidderh ta bata Hijab d'in data cire tana murmushi tace sai tasa wata Hijab suje haka mana Fatun tace a'a ta bata dai, bayan ta d'aukko mata ta saka Jidderh tayi gaba tana biye da ita suka nufi k'opar fita, lokacin da suka iso cikin parlon yana zaune akan Royal sofa 2 seater dake kusa da tagwayen benayen da zasu kai ka sama ya d'aura kafa d'aya akan d'aya jikin shi sanye da farar jallabiya, basu dad'e da dawowa daga Masallaci ba suda Dad d'in su da sauran Mazan gidan kowa ya wuce d'akin shi, idon shi akan Fatuu har suka k'araso Jidderh ta zauna akan 1 seater Fatuu ma ta zauna akan d'ayar one seater d'in, gaida shi Jidderh tay ya amsa fuskar shi a sake tana murmushi tace "gata nan ko sauro d'aya ban bari ya cije ta ba in ma akwae shi" d'an murmushi yay ya furta mata thanks, gaida shi Fatuu tay ya bita da ido kawae ganin kallon da yake mata yasa taji kunya ta sadda kanta k'asa Jidderh dai sai murmushi take saki, ce mata yay taje tace zata jirata ne su koma yay mata wani kallo kafin yace zata 6ace ne, dariya tayi ta girgiza mashi kai alamar a'a ta mik'e ta nufi hanyar barin wurin, jin ta bar wurin yasa ta d'ago suka had'a ido dashi k'ara gaishe da shi tay kawae sai taga ya mik'e ya nufo wurinta, yana zuwa ya kamo hannunta ya mik'ar da ita Slowly yace suje inda ya kamata ta gaida shi, hanyar bene ya nufa da ita yana ruk'e da hannunta sai d'an waige waige take gudun kada wani ya gansu, sosae cikin ranta take jinjina tsaruwar ko ina na gidan don shima saman benen ba K'aramin had'uwa yay ba, part d'in shi ya nufa da ita bayan ya tura k'opar ta bud'e ya shige da ita, daddad'an k'amshi mai had'e da sanyin Ac ne suka tarbeta bayan sun shiga bin d'akin tay da kallo sosae ya burgeta, maido idon tay kan shi ya jawota jikinshi suka tsaya suna kallon juna da murmushi can tace mashi ina kwana Slowly ya amsa tare da d'an lumshe ido, had'e foreheads d'in su yay k'asa k'asa ya furta "I didn't sleep well last night because u weren't by myside" rufe idanunta tay tana shak'ar k'amshin shi daya cika mata hanci, ganin abun na neman yin yawa yasa ta fara k'ok'arin raba jikin su, k'in sakinta yay ya bita da kallo idanunshi a d'an lumshe har sun fara canza yanayin su tana yamutsa fuska tace "Hubby kar wani ya shigo" shiru yay yana kallonta kaman bazai tanka ba can kuma ya d'age mata gira yace "d'akin wani ne da zai shigo?" da yanayin damuwa tace "naga ai ba gidan mu bane nan d'in" d'an guntun murmushin gefe yay yace "gidan su waye?" rasa amsar da zata bashi tay sai yamutsa fuska take, sakin ta yay yace "i'm sorry ina damun ki, u can go" waro ido tay da sauri ta kama shi da d'an rawar murya tace "a'a Hubby ba haka nike nufi ba fa, kawai dai naga kaman ni matsayin bak'uwa ce ina jin kunya ne a ganni anan" shiru yay yana kallon ta kawae ta d'an jijjiga shi tace yayi Magana mana, still bai tanka mata ba sai kallonta kawae da yake shi kanshi yana mamakin kanshi yadda yake mata wanda sam ba haka ya saba yi ma Fanan ba mafi yawancin lokutta ma ita ke neman shi yanzu kuma sai abun ya juye duk in ya kasance da ita wata irin natsuwa ta daban yake samu, har idanunta sun ciko da k'walla kawae zai gani yay sun zubo mata sharr ta fad'a jikin shi tana fad'in don Allah kada yay fushi da ita sigh yay ya kai hannu ya d'agota Fuskar shi a sake yace mata waya fad'i mata zai iya hakan kawai dai bai son yana takura mata, da sauri tace "ni baka wani takura man hubby kawae ina jin kunya ne" murmushi yay yace to miye abun kunya nan fa d'akin mijinta ne dama ai anan yakamata ta zauna ba wani wuri ba, kai ta jinjina mashi ya kama hannunta suka nufi hanyar Bedroom yana fad'in har yanzu kuka bai mata wuya ko tay murmushi ta d'an fad'a jikinshi ya tallabo ta,
Bayan tayi wanka zaune tayi jikinta sanye da bathrobe tana son ta koma d'akin Jidderh amman kunya ta hanata don ta d'auki lokaci anan, bin Haisam dake gaban mirror yana gyara sumar shi jikin shi sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt tay, bayan ya gama nufo inda take zaune yay ya tsaya a gabanta yace tazo ya rakata sai ta sa kaya, mak'e mashi kafad'a tay tana yamutsa fuska tace Allah ita kunya take ji tun d'azu fa take nan murmushi yayi sai kuma yay moving wurin side drawer ya kai hannu ya d'aukko wayar shi dake ajiye asama, Jidderh ya kirawo tana fara yin ringing ta d'aukka don lokacin itama ta tashi daga baccin data koma ta fito wanka tana cikin shiryawa, ce mata yay ta d'aukko ma Fatuu kaya a cikin trolley d'inta tace to, bayan ya gama wayar komawa yay wurin ta ya zauna daga gefen ta ta kai kanta ta kwantar a saman shoulder d'in shi k'asa k'asa da murya yace "Yunwa ko?" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace yasan zuwa yanzu dole taji yunwa, ba'a jima ba Jidderh ta kawo kayan ta tsaya a bakin k'opa tana knocking, mik'ewa yay ya nufi kopar yana bud'ewa ta sakar mashi murmushi tana sanye da riga da wando skin tight sai rigar ta saukko mata zuwa rabin cinyoyin ta, mik'a mashi kayan tayi ya amsa ya furta mata thanks har zata juya sai kuma ta dakata lokacin shima har zai koma ciki tace mashi ko ta jirata su tafi tare d'an shiru yay sai kuma yace ta zauna a parlon ta jira ta fito tana murmushi tace to ta juya ta nufi wurin kujeru, bayan ya kai mata kayan waro ido tay tana kallon su ganin skinny jeans ne da riga wanda in tasa kayan sosae suke kamata, da alamun damuwa ta kalle shi tace gaskiya bazata saka su ba yace Saboda me, nuna mashi kayan tay tace baiga wanda ta d'aukko mata bane,