Sashe 165
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
yadda zai tsaya da sanyin shi gaba ɗaya cikin wata jaka aka saka su a haka ma kayan sunyi ma Yadikko kaɗan tace inda da Mota suka zo sai an cika boot ɗinta da fura da Nono saboda su twins Fatuu nata dariya tace a haka ma ai da yawa, kusan gaba ɗaya gidan aka fito rakiyar su waje anata masu Allah ya tsare hanya, bayan sun baro rugar gidan su Khalid suka koma anan suka ci abincin rana kafin sukai masu sallama Hajiya Rabi'atu taba Fatuu kyautar atampopi masu kyau guda biyu da lace harda humra masu ƙamshi da turarurrukan wuta su twins ma ta basu kaya sosae tayi mata godiya harda Haisam, har bakin Mota suka rako su lokacin da suka baro gidan ƙarfe ukku na rana zuwa karfe huɗu da wasu mintuna suka iso Yola, har gidan Senator Buba Khalid ya kai su da har yace bari ya jira su sai ya kai su Airport Haisam yace mashi ya bashshi kawai kar su 6ata mashi lokaci akwae Driver da zai kai su yayi mashi godiya kafin ya amshi lambar shi yace zai kira yaji yadda ake ciki dangane da jikin Arɗo Khalid ɗin yace Ok, harda kuɗi yaba su twins Fatuu tace ya barshi yana murmushi yace ai ba ita yaba ba yaranshi yaba ta amsa tayi mashi godiya tare da cewa ya gaishe da iyali yace zasu ji daga haka ya tafi, da suka shiga cikin gidan basu daɗe ba salla kawai sukai koda aka basu abinci cewa sukai a ƙoshe suke sukai masu sallama nan ma saida aka ba Fatuu da twins kaya Senator Buba ma ya basu kyautar kuɗi masu yawa zumunci mai daɗi, a wata jibgegiyar Jeep aka tafi kai su Airport harda Senator Buba yay masu rakiya, suna akan hanyar ne Fatuu taji ƙarar shigowar saƙo a wayarta, lokacin data duba saƙon har saida gabanta yay bugu da ƙarfi don ta gane Khalid ne ya turo duk da bata da lambarshi amman daga yanayin saƙon ta gane nashi ne, da turanci ya rubuto mata yana mai bata haƙuri da kuma neman yafiyarta akan abunda ya faru a tsakaninsu a baya yayi nadama da kuma danasanin da yasan har ya mutu bazai daina yi ba sai dai ta wani bangaren yayi farincikin shigowarta rayuwarshi don ta dalilinta Allah yasa ya daina duk wani abu mara kyau a ƙarshe yana son ta sani ta zamo wani bangare na rayuwarshi wanda hakan ne ma yasa shi saka ma ɗiyarshi sunanta, tana gama karantawa ta ɗan saci kallon Haisam dake gefenta taga idon shi na a gaba suna yar hira da Senator Buba dake a seat ɗin gaba, kamar ta share Khalid ɗin ba sai ta mayar mashi da amsa ba sai kuma wata zuciyar ta raya mata yana iya cewa zai ƙara turo mata wani saƙon saboda rashin jin amsarta hakan yasa ta maida mashi da amsa, itama da turanci tace komai ya rigada ya wuce don har tama manta kuma tun bayan da aka fasa aurensu ta yafe mashi don haka tana fatan shima ya manta sannan ta gode da karar da yayi mata ya gaida mata da Zarah da Mamanta, tana tura saƙon ta goge duka nashi daya turo mata da nata data tura mashi sannan tayi blocking ɗin lambar tashi yadda bazai iya sake turo mata saƙo ba ko ya kirata tay shiru zuciyarta ta shiga tariyo mata da abubuwan da suka faru tsakaninsu yadda ya rinƙa yi mata a cikin Mota da gidan gonarsu da ya kaita, idanunta ne suka fara tara ƙwalla da sauri ta fara ƙoƙarin mayar dasu tare da kawar da tunanin daga ranta.