← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 211

Sashe 21

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tana shiga ciki corridor d'in da zai kaita Bedroom d'in shi ta nufa, tura k'opar tay ta bud'e ta shiga, tana shiga ta tsaya tana k'are ma Bedroom d'in kallo tsaf tsaf da shi ga wani sanyi mai had'e da daddad'an k'amshi sun karad'e shi gadon ya sha lallausan bedsheet kai kace ba d'akin namiji bane, wurin kujeru ta nufa ta d'aura ledojin akan c-table kafin ta sauke bag pack d'inta ta aje a k'asa gaban kujera itama ta zauna akan kujerar fuskarta a sake tana k'ara bin d'akin da kallo, tunanin abunda ya kamata tayi ta shiga yi zuciyarta ta bata ta yi salla itama, mik'ewa tay ta nufi hanyar corridor d'in da toilet yake, bayan ta shiga cikin toilet d'in sai kuma ta canza ra'ayi ta yanke tayi wanka kawae, after some minutes ta fito cikin Bedroom sanye da bathrobe d'in Haisam har ta kusa kai mata k'asa ta nufi gaban mirror, kallon kanta ta shiga yi tana d'an murmushi ita kanta taga canzawar da ita fuskarta tayi wani sumul tayi wani Fresh, mai ta fara shafawa bayan ta gama ta fesa turarurruka ta goga roll on, tunanin to wane kaya ma zata sa ta shiga yi don bai kamata ta zauna da bathrobe d'in ba, zuciyarta ce ta raya mata taje ta duba cikin kayan shi k'ilan ta samu wanda zata iya sakawa, laudary room inda press d'in shi take ta nufa, bayan ta bud'e ta fara bin kayan ciki da ido ganin wurin su shadda ne yasa ta rufe ta bud'e d'ayan side d'in anan taga k'ananun kaya suke, hannu ta sa ta fara d'add'agawa idanunta ne suka kallo wata jar riga a linke ta raya bari ta duba k'ilan babbar t-shirt ce in zata d'an saukko mata sai ta saka ta kawae, bayan ta d'aukko tana warware ta ba shiri ta waro ido da sauri ta kai hannu ta rufe bakinta alamar Al'ajabin ganinta, cire hannun tay ta fara murmushi ganin jar rigar data sa ranar da suka je dinner party d'in abokin shi har suka wuto nan, tun lokacin da abun ya faru bata bi ta kan rigar ba tasa jallabiyar ta kawae da yake mai zip ce ta tafi, rigar sai sakin k'amshi take ta yanke bari ta saka ta ma kawai, cikin Bedroom d'in ta dawo ta tsaya a gaban mirror ta fara kiciniyar sakata dama ko wanccan lokacin da k'yar ta shige ta don ma tana roba, yanzu ma ta shigeta saidae ta kamata kaman lokacin data sakata da farko, sosae shape d'inta ya fita ita dad'in hakan taji don dama tana son kaya su kamata, bayan ta gama d'aukar bathrobe d'in tayi taje ta bazata a laundry kafin ta dawo gaban mirror ta fara gyara gashinta, tana cikin sharce shi a cikin ranta ta shiga raya yakamata tayi kitso duk da ba son kitson take ba amman ko rannan saida gwaggo tayi mata Maganar kitson har tace zata yi mata k'arshe ta zille ba'ayi ba, tana haka taji an turo k'opar da sauri ta kai idon ta, shine ya dawo aikuwa da gudu ta nufe shi kafin ta isa ya bud'a mata hannuwan shi tana isa ya kamata ya d'aga ta sama, sosae hakan ya burge ta sai dariya take shima dariyar yake fararen hak'oran shi har sun bayyana, sauke ta yay ya rungumota jikinshi ta d'aga kai tana kallon shi suna sakar ma juna murmushi a shagwabe tayi mashi sannu da zuwa cikin cool voice d'in shi yace yauwa, tambayar shi tay yayi masu Addu'ar ya d'aga mata kai alamar eh tace to wace iri, d'an jimm yay yana mata murmushi sai kuma ya rankwafo da kanshi ya kai bakin shi saitin kunnanta ya rad'a mata wadda yayi masu ba shiri ta kife fuskarta a jikinshi tana dariya, d'ago Fuskar tata yay sai d'an runtse ido take alamun kunya, bin fuskar yay da kallo yana jin wata irin sabuwar k'aunarta acikin zuciyar shi, bayan ta bud'e idanun tambayar ta yay taci Abincin ko ta girgiza mashi kai alamar a'a tace shi take jira ya bata a baki yace Ok, kama hannun ta yay suka nufi ciki anan take ce mashi bai ga rigar data saka ba yay murmushi ya had'eta da jikin shi yace ya gani tayi kyau, wurin kujerun suka nufa ya saketa, matso da c-table d'in yayi a gaban kujera bayan ya zauna ya mik'a ma Fatun hannu ya ruk'ota, a saman jikin shi ya d'aurata tana ta murmushi ya kai hannu ya fara bud'e ledojin Abincin, tambayar shi tay a ina kitchen yake ta d'aukko plates slowly yace ta barshi ai zasu iya ci haka, Fried rice suka fara ci shi yake bata a baki tace ya barshi ta ci yana d'an murmushi yace bai son ta wahala, cike da soyayya ake cin Abincin wani lokacin in ya bata sai yay ta kallon bakin yadda take taunawa tana murmushi wani lokacin kuma sai ya kai bakin shi yay pecking bakin nata, saida suka ci suka k'oshi ya bata lemu ta sha itama ta d'ago ta bashi, k'ok'arin mik'ewa tay tana fad'in bari ta d'auke kayan, maido ta yay jikin shi da sauri ta kalle shi tana ganin yanayin idon shi ta lumshe mashi nata, romancing juna suka shiga yi bayan wani lokaci ya dauketa ya nufi bed da ita, sosae suka shiga nuna yadda sukai missing d'in juna, kamar yadda ya tara mata gajiya haka itama, sun d'auki tsawon lokaci suna faranta ma juna, yau dai iya magantuwa d'an Senator yayi har dai Salati saida aka ma Manzo SAW da Aure ya kasance sunnar shi.

Lokacin da aka fara kiran sallar la'asar Haisam ya farka daga baccin da suke tun bayan da sukai wanka, toilet ya nufa yayo Alwala jikin shi sanye da jallabiya ya fito don tafiya Masallaci, saida ya koma wurin gadon ya tsaya yana kallon Fatuu dake ta shan bacci yasan tana buk'atar shi hakan yasa ya yanke tafiya in ya dawo sai ya tashe ta tayi sallar. Motsi ta fara yi a hankali ta fara bud'e idanunta har ta ware su kallon gefenta tay taga ba Haisam ta maida idonta sama, k'ura ma ceiling ido tay tana yi tana lumshe ido Memory d'inta da Haisam na d'azun na dawo mata fuskar ta d'auke da k'ayataccen murmushi, ta d'an d'auki lokaci a haka kafin ta fara tunanin ina Haisam d'in ya tafi ne, tunawa da Salla yasa tayi tunanin k'ilan yana Masallaci, tashi tayi ta saukko da k'afafunta gaba d'aya jin jikinta take ba k'wari duk ga6o6inta kwankwasa suke sai faman langa6ar da kai take da k'yar ta mik'e ta nufi toilet,
Chapter 21 · 0% Book details