← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 211

Sashe 171

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari kafin ayi salla ya iso Ya yi shigar manyan kaya ya fito a dattijo mai kamala anan gidan yayi sallar Juma'a suka ci Abinci tare da Hajiya a dining, bayan sun gama cin abincin ne suka dawo falo yana zaune a kujerar dake gefen ta Hajiya yace "Hajjaju gani na amsa kira Allah yasa na lafiya ne" tana murmushi ta bashi amsa da lafiya lou sai alkhairi ya furta Alhamdulillah shi suke fata a koda yaushe, Maganar zuwa neman auren Tk tayi mashi tace tana son ya shige gaba tasa anyi mata bincike akan gidansu yarinyar an tabbatar mata da basu da matsala shi mahaifin nata asali mutumin Gombe ne aikin custom ya kawo shi Katsina daga nan zaman ya ɗore don yanzu har ma yayi retired to tana son ya tuntube shi kan su bada lokacin da za'aje neman auren, jinjina kai yayi yace to ba matsala a yau ma kafin ya tafi sai ya tuntube shin a bashi Address ko kuma lambar wayar shi tace to dama ta amshi lambar a wurin tukur ɗin, bashi lambar Baban Asma'un tayi yayi saving ya ɗago yana murmushi yace ashe sun kusa shan bikin ɗan gidan Hajiya itama murmushin take tace aikuwa yay fatan Allah ya sanya alkhairi ya nuna masu,

bayan ta amsa da Amin tace "Kai ma in kana son ƙara Auren akwae mata a ƙasa zan baka" waro ido yay ya ɗan buɗa baki sai kuma yayi dariya yace yasan ai wasa take, ɗan ta6e baki tayi tace dama ana wasa da Maganar aure, yana dariya ya tambayeta wacece matar, tace "Kana so ne?"

"To Hajjaju taya zansan ko ina so ba tare dana ganta ba" yana ta dariya yay Maganar,

"To ai in kai baka santa ba ni na santa kuma na yaba da ita ne shiyasa nayi maka maganarta tuntuni ma nake kwaɗayin wani cikin Family ya aureta saboda kyawun halinta Allah bai nufa nayi ma wani maganarta ba sai kai da nayi mawa yanzu",

"To ai Hajjaju kyau dai in ganta" still dariyar yake itama haka tace "ai ina ganin ma kasan wacece Kakar matan su Haisam da Nameer ce, ba wani tsufa tayi ba kawai don anyi mata auren wuri ne da yake asalin Fulanin daji ce in ba don haka ba bazata aje ma jikoki kamar su ba don ina ganin ka girmeta kaga kai baka dade daka samu Yan jikokin ba" shiru yay yana ƙoƙarin tuna ko yasanta can yace gaskiya ya kasa ganeta koda ya santa Hajiyar tace bari taga ai kaman akwai hotonta da akayi da bikin su Nameer anan falonta kuma shima ranar yana nan dashi akai hotunan, hoton gwaggo da tayi tare da Mino a ranar ta buɗo mashi ta miƙa mashi ya amsa ya bi hoton da kallo yana ɗan murmushi can ya ɗago ya tambayi Hajiyar bata da aure ne tace inda tana dashi zatayi mashi tayin auren nata ne ya sake tambayar abunda ya rabata da mijin nata ta faɗi mashi aurenta biyu na farko na dole ne akai mata da yake ta taso marainiya shine kawunta da ya riƙeta ya aura mata abokin shi to hardai zaman ya ƙare basu haihu ba bayan ta dawo wurin kawun nata Daura tana zuwa tallan nono a kasuwar mashi Allah ya haɗa ta da mijinta na biyu data aura shine suka haifi yara biyu kafin ya rasu sanadiyyar haɗarin mota tun daga nan kuma bata ƙara yin aure ba kusan shekara ashirin da biyar duk da tana da masu son auren nata itace bata so cikin dangin mijinta daya rasu wani ya samo mata aikin asibiti tana yi farko ma a gidan shi ta fara zama daga baya saboda rashin jituwar da suke samu da matarshi ta baro mashi gidan tazo ta gina wannan da take ciki a filin da suka gada, nan ta bashi labarin yadda mahaifiyar Fatuu tayi aure ta haifesu su biyu da yadda Gwaggon ta ɗaukko su ta riƙe ta kuma shiga nuna mashi kyawawan halayenta, ajiyar zuciya Kawu Mani ya sauke ya sake kallon hoton gwaggon kafin ya miƙa ma Hajiya wayar ta amsa tare da tambayar tayi mashi ko kuwa yana yar dariya yace tunda tayi mata tana son ya aureta in dai zata amince zai auretan,

"A'a ba wani tunda tayi man inason ka aureta salon kaja man matanka su ƙullace ni, kawai in kaji kana son ta zaka aureta to in kuma bata yi maka ba lafiya lau ka fito ka faɗi man ai ba wani abu bane dama don naga kana da ra'ayin mata fiye da ɗaya ne tunda yanzu haka biyu gareka shiyasa nayi maka Maganarta" sosae yake dariya jin abunda tace bayan ya tsagaita yace to yanzu koda tayi mashin in ita taƙi amincewa dashi fa tunda tace tana da masu son aurenta itace bata so Hajiyar tace ai sai suma su jaraba sa'ar su ƙilan Allah yasa ta amince dashi, gyaɗa kai yay yace to yanzu ya za'ai tasan dashi,

"Wannan mai sauƙi ne in ka shirya haɗuwa da ita kuyi magana sai in kirata in mata magana", yar ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace abunda za'ai yanzu zai kira mahaifin ita wadda tukur ke so yayi mashi maganar haɗuwarsu in ya bashi dama da yayi sallar la'asar sai ya tafi yanzu abunda za'ai tayi ma ita Matar magana in ya fita sai ya fara tsayawa wurinta su gaisa kafin ya wuce, wani kallo Hajiya tayi mashi tace "Humm, su Mani anga farar fata har an zurma da anaso ai man bariki" Dariya ya 6a66ake da ita harda buga ƙafa yace "Sai Hajjaju mai dalilin aure, saboda dai kina so ne kawai"

"To tunda hakane a barshi kawai na janye....." da sauri ya katseta "a'a Hajjaju ba'a yi haka ba tunda dai kinyi niyyar haɗawa kada kima kan ki buƙulun lada ki kiratan kawai sai inje mu gwada sa'ar" wani kallo mai kaman harara tayi mashi ya saka dariya, ce mashi tay ya bari ayi sallar la'asar ɗin zata kirata Kawu Manin harda ce mata to ai kada ta fita unguwa Hajiyar na dariya tace ya dawo wani lokacin,

"gara dai ayi komai yau hajjaju kinsan ance da zafi zafi ake dukan ƙarfe" Dariya Hajiya tay tare da girgiza kai, bada daɗewa ba aka kira sallar la'asar ya miƙe don yaje masallaci itama Hajiya ta tashi tana ruƙe da sandarta ta nufi hanyar Bedroom don taje tayi sallar, bayan ta gama ne ta kira layin Gwaggo wayar na fara yin ringing ta ɗaga cikin girmamawa ta gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a bayan Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida tace mata eh bata daɗe data dawo bama daga wurin aiki, an dawo lafiya tayi mata Gwaggon ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah,

"to ga baƙo nan na turo zai zo ku gaisa" ɗan jimm Gwaggo tay a ranta ta maimaita abunda Hajiyar tace kafin ta amsa mata da to sukai sallama, zugudum Gwaggo tay ruƙe da wayar tana ta nanata zancen zuwan baƙon don abun sai taji shi wani iri saboda basu ta6a haka da Hajiyar ba wai tace mata ga wani nan zai zo su gaisa, Bayan sun gama yin wayar fitowa Hajiya tayi cikin falon kusan a tare suka dawo da Kawu Manin, bayan sun zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace yayi na yara duk sukai salla sai sun gaishe da mutum shima murmushin Yay yace ai haka yakamata kafin yace mata yanzu bayan ya fito ya kira Mahaifin yarinyar har ya bashi Address zai je ya same shi daga can zai wuce Daura duk yadda sukai dashi zai sanar mata ta amsa da to tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya, shiru suka ɗan yi bai miƙe ba can yace mata bata kirata bane tay dariya tace ai ta zata ya manta yaje ta kirata a waya, tambayar inda gidan yake yayi ta kwatanta mashi da shagon Amadu tace in yaje yaronta ne mai shagon sai yasa shi yaje yayi mata magana ya amsa da to tare da miƙewa tana murmushi tace Allah yasa taji Alkhairi ya amsa da Amin ta ƙara cewa zata turo mashi kuɗi yanzu sai ya zuba mai yayi mata godiya itama tayi mashi da fatan Allah ya kiyaye hanya tace ya gaida iyali daga aka ya fito,

A daidai shagon Amadu ya parker Motar shi lokacin basu daɗe da dawowa daga Masallaci ba, fitowa yay bayan ya kulle ƙopar Motar ya tunkari shagon, a gaban shagon ya tsaya fuskarshi ɗauke da murmushi yayi masu Sallama tunda ya fito Amadun ke kallon shi yana ganin kaman ya sanshi saida ya ƙaraso gaban shagon ya gane shi shima Amadun murmushin ya mayar mashi bayan ya amsa sallamar cikin girmamawa ya gaishe dashi Kamalu ma dake zaune kan plastic chair yana latsa waya ya ɗago kai ya gaishe dashi shima da murmushi ya amsa mashi, tambayar waye Amadu a cikin su yayi Kawu Amadu yace shine ya nuna Kamalu yace to shi kuma wannan fa ya bashi amsa da ɗan Yayarshi ne,
"Kenan ɗanka ne" Amadu na murmushi ya bashi amsa da eh,

"Ko shine Yayan Matar Haisam" da sauri Amadun yace mashi eh,

"Allah sarki, Allah yayi maku Albarka ya jiƙan Mahaifiyarsu da Mahaifin ka" a tare duk suka amsa mashi da Amin,
Chapter 171 · 0% Book details