← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 211

Sashe 186

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

103

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

........Washe gari da safe jirgin su ya sauka tare da security detail ɗinta aka ɗaukkosu zuwa gidan Hajiya motocin escort gaba da baya sai Jeep ɗin da take ciki a tsakiya, koda Hajiya ta ganta saida ta jinjina yadda ta rame, a bedroom ɗinta suka zauna tana kallonta tace ashe ta damu da Farha har haka amman shine taƙi goyon bayan abunda take so Hajiya Maryam ɗin ta ɗan yamutsa fuska kafin cikin karyayyar murya tace ai dole ta damu ace yarinyarka budurwa tabar gida ita damuwarta a wane hali take ciki ina taje, tana yin Maganar ƙwalla suka zubo mata sharr Hajiya tace "in sha Allahu tana cikin ƙoshin lafiya kuma a hannu nagari" a hankali ta amsa da Allah yasa,

"Yanzu in aka ganta zaki goyi bayan abunda take so ko?" Hajiya ta tambaya tana kallonta tay ɗan jimm kafin tace "Hajjaju ni a ganina ba kowanne abu yaro ke zuwa dashi a goya mashi baya ba, komai da nike yi saboda rayuwarta ta inganta ne taya za'a ce Farha ta auri yaro kamar wannan bacin ga wanda ya gina rayuwarshi wanda zai ruƙeta da kyau muna gani sai mu barta taje ta jefa rayuwarta a wahala"

ɗan murmushi Hajiya tayi tace "idan abunda yaron yazo dashi baida wani aibu lafiya lou sai a goya mashi baya mana, sannan Maganar gina rayuwa ai shima baki san abunda Allah zai yi ma tashi rayuwar ba tunda yanzu yake kan gina ta, sannan Maganar jefa rayuwa a wahala shi wanda kike hangen zai ruƙeta da kyau saboda kuɗi ke a tunaninki mai kuɗi ne ke ruƙe mata da kyau, Matan masu kuɗi nawa ne suke cikin damuwa a gidajen auransu har suna ganin dama talaka suka aura wanda zai basu farinciki, ko kuwa don ke kin dace sai kike ganin kowace mace ma hakan take a wurinta to kije ki bincika na tabbatar zaki samu mata da dama wanda kuɗaɗen mazajensu basu sa sun kasance a cikin farinciki ba face damuwa",

ɗan yamutsa fuska tay da yanayin damuwa tace "Yanzu dai fatana Farhar ta bayyana shine kawai, gani kince kina son ganina",

Hajiya na ɗan murmushi tace ta dameta ko shiyasa take son a canza Maganar, da sauri tace mata a'a kawai dai taga ba abunda yakamata su maida kai akai bane tunda wadda ake Maganar don ita ba'a san inda take ba Hajiyar tace hakane Allah ya bayyana masu ita ta amsa da Amin,

"Kinzo na tsare ki da surutu ban baki abinci ba kuma halan ko breakfast baki yi ba" Hajiya ta faɗa idonta a kanta, warware gyalen haɗaɗɗar doguwar rigar dake jikinta data laga tayi ta kwanta a saman gadon tana faɗin tasha ɗan tea Abincin ne kwata kwata bai mata daɗi gashi duk in tazo ci sai tayi ta tunanin ko Farha taci abinci, yadda ta ƙarasa Maganar kamar zata saka kuka Hajiya na murmushi tace in sha Allahu taci mai kyau ma,

"Yanzu tea ɗin za'a ƙara haɗo maki sai a haɗa da wainar ƙwai muna da farfesun kaza ma, in kuma duk baki son su sai ki faɗi abunda kike so a haɗa maki" shiru ta ɗan yi kamar bazata yi magana ba can ƙasa ƙasa tace rana tayi abar tea ɗin a kawo mata farfesun taga in zata iya sha Hajiya tace to ko a soya doya sai ta haɗa da sauri ta girgiza mata kai tace abu mai ruwa ruwa kawai take ɗan iya ci Hajiya tayi murmushi tace to bari tasa a kawo mata anan, wayarta ta ɗaukko ta shiga yin kira bayan an ɗaga umarnin kawo ma Hajiya Maryam farfesu ta bayar tare da lemu da ruwa daga haka ta kashe wayar idanunta akan Hajiya Maryam data rufe ido kamar mai yin bacci, ba'a jima ba aka turo ƙopar ɗakin Farha ta shigo tana sanye da ƙananun kaya kaman ko yaushe kanta ba kallabi sai dark ash ɗin sumarta dake a fake ta lanƙwasa ta, bata yi sallama ba Hajiya tay mata nuni da gaban gadon saitin inda Hajiya Maryam ke kwance tace taje ta aje anan kan carpet, har ta aje Hajiya Maryam bata buɗe ido ba Farhar ta ɗago tana kallonta wata irin kewar Mahaifiyar tata taji ita kanta taga canzawar da tayi bata ta6a tunanin za'a samu ranar da zasu samu sa6ani da Mom ɗin tata ba don sun shaƙu kamar abokai haka suke dalilin shaƙuwarsu ne ma yasa Farhar bata fita ƙasar waje yin karatu ba tayi a nan, da hannu Hajiya tayi mata alamun ta gaishe da ita cikin ɗan rawar murya tace mata ina kwana still bata buɗe idon ba da alama ma bata ji ba, saida Hajiya tace mata ana gaisheta sannan ta ɗan ɗaga hannu alamar ta amsa, tsaye Farhar tayi tana ta kallonta a hankali ƙamshin turarenta ya fara kurɗaɗawa cikin hancin Hajiya Maryam lokacin data shaƙe shi sosae da mamaki ta ayyana ƙamshin kamar na Farha, zuciyarta na raya mata hakan da sauri ta buɗe idanun nata suka shiga cikin na Farha dake tsaye ai a sukwane ta tashi zaune tana kallonta idanu waje, muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wannan kamar Farha a gabana Hajjaju kodai gizon data saba yi man ne dama sai inta ganinta koda yaushe" Hajiya na murmushi tace itama kamar ita take gani, maido idonta tayi kan Farha dake ta kallonta sai kuma ta maida kan Hajiya, murmushin da taga tana yi ne yasa ta gane Farhar ce aikuwa da sauri ta miƙe tsaye cikin rawar murya ta furta "F...Farha, it's You...???" shiru ta ɗan yi kafin a hankali ta furta "Yes, Mom" zaro ido Hajiya Maryam tayi gaba ɗaya ta juya kan Hajiya cike da al'ajabi tace "Amman Hajjaju ya akai kika samota ko nan tazo?" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tare da ɗan girgiza kai tace dama tana nan, cikin ɗaurewar kai ta maimaita abunda Hajiya ta faɗa ta ɗaga mata kai alamar tabbatar wa,

"Yanzu Hajjaju kina nufin duk abun nan Farha na wurin ki?" Hajiya tace mata eh ita ta tsara mata komai tasa ta taho wurin ta, wani kalan yarfa hannu Hajiya Maryam tayi tare da yamutsa fuska ta koma gado ta zauna yaraf kamar zata yi kuka tace "But Why, Hajjaju, miyasa don Allah zaki tada mana hankali har haka kika sa anata cigiya mutane nata kashe kuɗi suna zuwa jaje amman ashe tana wurinki kuma kina sane da dole hakan zai tada mana hankali ba kaɗan ba" wani irin ɗaure fuska Hajiya tayi da hannu tayi ma Farha alamar ta zauna a kan carpet, bayan ta zauna ta maida idonta kan Hajiya Maryam fuska a ɗaure ta fara magana,

"Nasani hankalin wanda bai san da tana wurina ba zai tashi kamar ke sannan Maganar kashe kuɗi da zuwa jaje duk nasan za'ai hakan saidai ina son ki sani na za6i yin hakan ne don in baki misalin irin tashin hankalin da kike niyyar janyo mana kenan koma wanda yafi wannan, saboda taurin kan ki kina ƙoƙarin ki saka mu a damuwa da danasanin da har mu mutu bazamu daina ba to aka me zamu zura ido muna kallo ki jefa mu a hakan, kina sane da illolin da auren dole ke tattare dashi amman shine kika rufe ido saboda wani kurman ra'ayin ki zaki jefa rayuwar yarinya a halaka, baki tunanin zata iya kassara rayuwarta ba ko kuma ta ƙyaleki ki ɗaura mata auren shi mijin ta illata shi ba, in hakan ya faru wane irin tashin hankali kike tunanin hakan zai haifar mana, so kike mu zama abun misali a idon duniya ki jaza mana tambarin da bazai ta6a goguwa ba har ƙarshen rayuwar mu?"" a fusace take yin Maganar,

jin tayi shiru ne yasa Hajiya Maryam ɗin cewa "amman Hajjaju wannan ai ba auren dole bane tunda akwae soyayya tsakaninsu ta tsawon lokaci kuma su duka suna son junansu kwatsam kuma sai ta dawo tace wai bata son shi....."

Katseta Hajiya tayi taci gaba "tace bata son shin ai ba laifi tayi ba dama yana faruwa yau kaji kana son mutum gobe ka dawo kaji baka son shi dama ana samun haka wanda aka ɗauki lokaci ana soyayya sai kiga bashi Allah ya ƙaddaro za'a aura ba sai daga baya mijin ya 6ullo ta inda ba'ai zato ba yasha faruwa koma yana kan faruwa ma shiyasa wasu suke gudun 6ata lokaci wurin yin soyayya suke bari sai sun shirya ma aure sannan su fara wasu kuma suna yin soyayya da shirin kota kwana, shiyasa ba'a so ana soyayya ai ta ma juna ƙaryayyaki da alƙawura tunda mutum bashi keda kan shi ba ta yuwu wanda kake hasashen aura bashi Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarka ba shiyasa yana da kyau a gina soyayya kan wannan turbar kowa yasa hakan a zuciyarshi sai kiga koda rabuwar tazo baza'a ji ciwo sosai ba, don haka ki rabu da yarinya ta auri wanda take so wataƙil dama wannan shine wanda Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarta" ba alamun wasa Hajiya ke yin Maganar,
Chapter 186 · 0% Book details