← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 211

Sashe 11

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tana ta zaune a bakin gadon ji take kaman taje part d'in Hajiyar saidae wata irin kunya take ji, tunanin gyara d'akin tayi ta mik'e, wani sabon Bedsheet taje ta d'aukko a cikin Wardrobe ta dawo ta cire na saman gadon da na pillows d'in ta fara shimfid'a wanda ta d'aukko, bayan ta gama laundry ta nufa ta d'aukko floor wiper tazo ta fara share dakin, data gama ta maida ta d'aukko bucket d'in Mopping ta dawo, tana cikin yin Mopping d'in har ta kusa gamawa taji an turo k'opar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri, shine ya shigo suka had'a ido nan take zuciyarta ta shiga raya mata daga wurin Fanan yake, ganin yana mata murmushi yasa ta d'an yi murmushin itama, rufe kopar yay ya nufo inda take tsaye hannunta ruk'e da mop, a gabanta ya tsaya ya kai hannu ya ruk'o mop d'in ta sakar mashi, janye bucket d'in yay gefe ya kai duka hannuwan shi ya matso da ita gaban shi idonta a kanshi, ganin ta d'an yi mashi k'asa yasa shi rankwafawa ya had'e goshin su slowly yace mata waya sata yin wannan aikin yanzu, shiru bata ce mashi komai ba ya d'ago da fuskar shi yana kallon ta ya d'an d'age mata gira, da d'an murmushi tace mashi taga bata yin komai ne kuma d'akin na buk'atar a gyara shi shiyasa, tunda ta fara Maganar ya maida idon shi akan bakin ta daya sha jan jambaki har ta gama, ganin yadda ya kafe ta da ido ba tare daya ce komai ba yasa ta d'an tura mashi baki ya saki murmushi, juyawa yay da ita suka nufi wurin gado, shi ya fara zama sannan ya zaunar da ita kan cinyoyin shi ta yadda fuskokin su suka kusa yin saiti, shiru sukai gazing lovingly into each other's eyes kowa kokarin nuna ma d'an uwanshi yadda yake k'aunar shi suke ta cikin idanun, kasa jurewa Fatuu tay tana murmushi ta kwanta a jikin shi idanunta a d'an lumshe tana shak'ar daddad'an k'amshin da jikin na shi ke saki, hannuwan shi yasa ya rungumeta sosae ha6arshi a saman kanta taji ya furta tayi kyau sosae still Murmushi take ta furta mashi ta gode shima yayi kyau, shiru suka k'ara yi tayi lamo idanunta a rufe she felt safe in his embrace, suna haka taji Muryar shi yana tambayar tayi Breakfast ne ta d'an girgiza mashi kai alamar a'a, d'agota yay gaba d'ayan su idanuwan su sun d'an lumshe yace "miyasa zaki zauna da yunwa ko kina so ulcer ya kama man ke?" yay Maganar tare da d'age mata gira, yar dariya tayi don ta gane abunda take ce mashi ne yace mata da sigar shagwa6a tace to ba shi take jira ba, "Ok, kiyi hak'uri na bar ki da yunwa naje gaida Hajiya da Auntie d'in ki" jinjina mashi kai tayi ya kai bakin shi saitin nata ya manna ma lips dinta kiss, yana d'agowa ta d'an waro ido sai kuma ta saki dariya tambayar ta yay miye tace ya gogi jan bakin ta ganin abun ya saka ta nishad'i yasa shi kai hannu ya matso da kanta ya kad'e lips din nasu giving her a deep kiss, sun d'an d'auki lokaci kafin ya saki kan da k'yar take bud'e ido koda taga yadda bakin nashi yayi da jan bakin sosae ta sa dariya harda k'yak'yatawa sai kallonta yake yana yar dariyar shima sosae take burge shi, can ta kai hannu ta fara goge mashi tana yi tana k'ara sakin dariyar suna cikin haka ya mik'e da ita yay mata d'aukar jarirai har lokacin tana goge mashi bakin ya nufi hanyar k'opa da ita don suje suyi breakfast.

Bayan sun gama yace su je ta gaida su Hajiya tace to, Bedroom ta koma ta d'aukko gyale bayan ta fito a corridor ta tsaya tasa takalma sannan ta dawo yana zaune a cikin parlor yana ganin ta ya mik'e yana mata murmushi ya kama hannunta suka tafi, suna zuwa k'arshen hanyar da zasu shigo cikin harabar gidan ta zame hannunta ya juya ya kalleta ta d'an yamutsa mashi Fuska, murmushi kawai yay baice komai ba don ya fahimci dalilin daya sa tayi hakan, lokacin da suka shiga cikin parlon Hajiya na zaune suka nufe ta idonta akan su tana murmushi, Haisam d'in ya nuna mata wuri ganin tayi tsaye ta zauna shima ya zauna a gefenta duk sai taji wani iri, da k'yar ta gaishe da Hajiya don duk ta sha jinin jikinta gani take kaman duk ansan abunda ya faru tsakanin su, bayan d'an wani lokaci ta mik'e tace bari su gaisa da Aunty Fanan Hajiya tace mata to, bata dad'e ba ta dawo idon Haisam a kanta ta koma ta zauna tun kafin tayi Magana Hajiya tace halan bacci take tace mata eh, kallo suka d'an yi daga baya Haisam d'in ya mik'e yace zai je ya dawo Hajiya tayi mashi a dawo lafiya ya nufi hanyar fita idon Fatuu a kan shi sai kuma ta juyo ta kalli Hajiya ganin ta maida idon ta akan Tv yasa ta mik'e sumi sumi ta bi bayan shi, lokacin da ta fita har ya nufi hanyar parking space ta kira shi da d'an d'aga murya ya dakata ya juyo, tana k'arasowa ta tsaya a gaban shi tana murmushi yace ai ya zata bazai ai mashi rakiyan ba, bata ce komai ba ya kai hannu ya kamo hannunta har saida ta d'an waiga bayanta suka nufi parking space, bakin Motar da zai hau suka tsaya ya tambayi ko tana son wani abu ta girgiza mashi kai ya furta Ok, saida yay kissing hannun nata sannan ya saki ya bud'e Motar ya shiga ganin tayi tsaye yace mata ta koma ta d'aga mashi kai alamar to amman bata da niyyar tafiyar, Maganar Hajiya ce ta fad'o mata a rai ta kwanaki data ce in itace abunda ya gani k'arshe to zaita tunaninta a waje har yay ta sakin murmushi kamar zautacce, k'ara ce mata yay koda wani abu dai ta d'aga mashi kai alamar eh yace to miye ko ya fito ne, da sauri ta girgiza mashi kai ta fara matsawa, tsaye tay gaba dashi tana ta faman murmushi, d'age mata gira yay ya d'an k'ank'ance ido yace "What do you want?" tsuke baki tay sai kuma ta runtse ido da hannu tay mashi nuni da kumatun ta, lokaci guda ya gane mi hakan ke nufi yace "Do you want to kiss me?" ba tare data bud'e idon ba ta d'aga mashi kai kawai sai ji tay ya kamo ta ya shigo da ita cikin Motar yana k'ok'arin zaunar da ita akan cinyar shi da sauri ta fara k'ok'arin kwacewa yak'i sakin ta ganin haka yasa a marairaice tace mashi wani fa zai iya ganin su ya d'age mata gira yace to shine mi, k'arshe ba yadda zata yi dole ta zauna idanun shi a lumshe yace tay kissing nashi iya yadda take so a kuma duk inda take so........
Chapter 11 · 0% Book details