← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 211

Sashe 6

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"To da na amincen ka tafi dani Aunty Fanan fa tunda nasan bata sani ba" a sanyaye tayi Maganar tana kallon shi, sigh yay yace zai kai ta wani wuri ne da bazata sani ba tunda lokacin ya fahimci bata son zuwa can Saboda Fanan d'in don akwae wani lokaci a baya sun ta6a Maganar yace ko zataje can taci gaba da karatu tace mashi Fanan d'in koro ta zata yi tace ta lik'e ma mijin ta,
daga baya in ya yi mata bayanin komai sai ta koma gidan su, ce mashi tay to karatun ta fa bacin tayi nisa yana murmushi yace mata acan ma ai ana karatun sai tayi kuma bai d'aukar lokaci kamar na nan, shiru kawai tay suna cigaba da kallon juna can ya d'age mata gira yace "Are u satisfied now that I love you?" Lumshe mashi ido tay irin yadda yake mata nan take ya gane kwaikwayon shi tay, murmushi yay slowly ya kai bakin shi saitin nata ya manna mata kiss, da sauri ta kauda fuskarta alamar kunya, Hannu ya kai ya juyo da Fuskar tata ya furta "is dat all u want know ko da wani abu?" had'e lips dinta tayi ta d'an d'age ido alamar tunani, kallon shi tay cike da shagwaba tace "to amman miyasa kake gudu na?" kafeta da ido yay yana mata wani kallo ba tare da yace komai ba, ganin haka yasa ta fara nazarin Maganar da tayin a d'an rud'e tace mashi tana nufin miyasa bai sake mata bayan ta tare in kuma don abunda tayi ne ai ta bashi hak'uri kuma yace ya hak'ura, wani irin murmushi taga ya saki aikuwa ta fad'a mashi ta cusa fuskarta cikin broad chest d'inshi tana fad'in itafa ba wani abu take nufi ba wllh, rungume ta yay tightly yana ji a ranshi kaman su dawwama a haka bayan ya kwantar da Fuskar shi saman gashinta a nutse ya furta "ba gudun ki nike ba Wife, I always need u badly, abunda ya faru a G.r.a nasan nima inada laifi duk da ban kai ki can ba don hakan Allah ne ya kaddara hakan zai faru, banyi fushi da ke ba kawai abu biyu ne ban ji dad'in su ba, farko yadda nayi maki nasan na cutar dake sannan kuma da kika zo sanar man u'r pregnant duk abunda kika fad'a man banji komai ba don nasan nayi maki ba daidai ba kawae abunda banji dad'in shi ba yadda nayi k'ok'arin dakatar dake amman kika k'i saurarana bazan 6oye maki ba banji dad'i ba kaman yadda na fad'a maki da kika zo bani hak'uri, hankali na ya tashi a lokacin ba kuma don rasa cikin ba sai don tsoron abunda zai iya faruwa dake I might lose u i thought to myself, hakan yasa na je na fad'i ma Hajiya duk da dama ina niyyar inje in fad'a matan Saboda abunda nayi maki.....Tun bayan da abu ya shiga tsakanin mu...Sai na sha drug nike iya bacci peacefully" lamo Fatuu tay cikin ranta ta shiga tunanin ashe Maganin data gani kenan Saboda haka yake shan shi, kai bakin shi yay saitin kunnanta cikin magana mai kaman rad'a yace mata yana gudun ta k'ara samun ciki ne yafi son sai dangin shi sun sani komai ya daidaita don yasan dole farko za'a iya samun matsala hakan kuma na iya sata a damuwa wanda ba'ason mai ciki tana damuwa k'arshe ma cikin zai iya k'ara zubewa wannan ne dalilinshi duk da yana cutuwa amman in itama ta cutu sai yafi jin ciwo, nan ya bata hakurin abunda su Hajiya Maryam suka mata ya nuna bai ji dad'i ba sosae amman insha Allah hakan ya wuce ba wanda zai k'ara mata, k'ank'ame shi Fatuu tay lokaci guda yaji sheshshekar kukan ta a cikin kukan ta fara bashi hak'uri kan tunanin da tayi ba daidai ba a kan shi da kuma wahalar daya sha saboda ita, gaba d'aya ta gama kashe mashi jiki, d'ago Fuskarta yay har tayi jage jage da hawaye, idanun shi a lumshe yake kallon ta sai kukan take itama tana kallon shi, girgiza mata kai ya fara kafin ya kai bakin shi ya fara kissing hawayen, jin tayi shiru yasa shi dakatawa ya d'ago hannu yana share mata fuskar, bayan ya gama yana murmushi ya tambaye ta ya akai ta fara son shi itada yasan ba komai a ranta sai son karatu ta zama Doctor, cikin muryar kuka ta fara bashi labari tana yi tana yar ajiyar zuciya, bata 6oye mashi komai ba tun daga kan yadda Haulat ta nuna mata son ta yake shiyasa yake hidima da ita har ranar ta tuna mashi daya tambayi Haulat d'in ko yau sun samu kud'i ne a school yaga tana cikin farin ciki tace mashi tun daga nan ta fara jin son shi, ta sanar mashi tun ranar da Aunty Fanan tazo ta gane abunda ke tsakanin su ta fara wahala akan son shi, a shagwabe ta furta "Wllh Ya Haisam nasha wahala....maimakon tunda nasan kana da wadda zaka aura in daina jin son kan amman zuciyata taita k'ara man son ka gashi kuma tasan ba samun ka zan yi ba....." Fuskarta sharkaf take Maganar, wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi har idanun shi sun k'ara sauyawa, cigaba da goge mata kwallan yay yana fadin "I promise you that this is the last time you will ever have to cry because of me" bayan ya gama goge mata rungumeta yay, suna haka yake ce mata ai da ta sani daya kirata ya tambayeta abunda ke damunta ta fad'i mashi tace mashi to ai tasan k'arshen ta ya bata hak'uri kaman yadda ta fad'i mashi su Kawu Amadu da Haulat sun ce mata a labarin data bashi kuma shima ba gashi yace lokacin da Abbas yay mashi Maganar aurenta duk da yana sonta da farko bai amince ba" shiru yay yasan kusan hakan ne zai faru, shafa bayanta ya shiga yi ana fadin she should forget about d pass, saida yaji ta samu natsuwa sosae sannan ya d'ago fuskar ta yana murmushi ya d'an dage mata gira yace yanzu yaushe zata biya shi abunda tasa ya rasa kaman yadda ta fad'a, kunya ce ta kamata ta fara mutsu mutsun son 6oye fuskar ta amman ya hana sai dariya yake hakanan sai ta kasa ce mashi ba ita ta tura sak'on ba, k'ara maimaita mata tambayar yay da k'yar tace mashi yana so ne, kai ya jinjina mata idonta a d'an runtse tace to miyasa Aunty Fanan bata haihun mashi ba tunda dai yana so, d'an jimm yay yana kallon ta har saida tasha jinin jikinta, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya sanar da ita tana da problem ne daya hana hakan amman tana cikin shan Magani, wani iri Fatuu taji sai taji dama bata yi Maganar ba, a sanyaye tayi Addu'ar Allah ya bata lafiya ya amsa sai kuma yace "in bata haihun ba zaki bata kyauta cikin naki?" Da sauri ta jinjina mashi kai tace "dana haifi na farko ma zan bata" d'an bud'a ido yay yace mata to yaushe zata biya shin aikuwa da sauri ta kife fuskarta k'ok'arin d'agota ya fara amman ta k'ank'ame shi sosae sai yar dariya yake yi, tsit kake ji zuciyoyin su sai bugawa suke a tare kowanne ya rufe ido, sun dauki lokaci a haka kafin taji ya tambayi mi zata yi a cikin Laundry room daya ga d'azun ta nufi can, ce mashi tay wanka take son yi ba tare data d'ago ba, k'ok'arin d'agota ya fara yi yace "Ok, let me help u take the bath" da sauri ta k'arasa d'agowa ta waro ido tana kallon shi ya d'age mata gira aikuwa da sauri ta fara k'ok'arin sauka daga jikin shi nan take ya gane guduwa take son yi ko kafin ta ankare gaba d'aya ya mik'e tare da ita ya sa6ata a kan kafad'ar shi ya nufi Laundry d'in da ita sai faman wuwwuntsila k'afafu take tana fad'in don Allah ya bari zata yi da kanta shi abunma dariya yake bashi yana zuwa da k'afa ya tura kopar ta bud'e ya shige da ita..............(Wayyo! An yi magani na ina niyyar sa kai don d'aukko rahoto aka bugo man k'opa a goshi, maganina kenan mai son ganin sirrin ma'aurata)

....In zauna a bakin gado in jira su su fito, amman dai goshina ya bugu dama k'opar bata wasa bace.........Ina zaunen Fanan ta fad'o man arai, ko awane hali take baiwar Allah.

*ASM 074*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
Chapter 6 · 0% Book details