← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 211

Sashe 7

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

........... After some minutes sai gashi ya fito da ita yayi mata irin d'aukar jarirai gaba d'aya ta duk'unk'une a cikin bathrobe,gado ya nufa da ita ya d'aurata aikuwa kaman tana jira da sauri ta jawo duvet ta lullube, zama yay a bakin gadon idon shi a kanta fuskar shi d'auke da k'ayataccen murmushi tunawa da yadda akai wankan, shi ganin hakan yake bak'on abu don koda Fanan tana Amarya bata yi mashi haka ba saidae kuma sosae yadda take nuna kunyar ke burge shi, jin shiru bata ji yayi Magana ba yasa tayi tunanin ko da ya ajeta tafiya yayi, a hankali ta sa hannu ta d'an janye bargon da nufin ta d'an lek'o taga ko tafiyar yay, karaf suka had'a ido aikuwa da sauri ta ja bargon ta maida Fuskar, Murmushi kawae yake saki can taji ya kira ta "Baby" runtse ido tayi tana dariya ta cikin bargon, dama tunda yana mata wankan taji ya fara kiran ta da haka, ji tay ya k'ara kiranta still idanunta a runtse suke ta amsa mashi, taji yace yanzu shi bazata taya shi yay wankan ba, dama tun a toilet d'in yaso suyi tare tak'i yarda harda yi mashi magiya kan hakan, ya lura sosae take jin kunya don da k'yar yayi mata wankan hakan yasa shi k'yaleta, k'ara yi mata magana yayi ta cikin lullubar ta girgiza mashi kai, sigh yay yace mata Ok shi ya saba sai an taimaka mashi yake yin wanka bari yaje wurin Fanan in tayi mashi sai ya dawo, wani abu taji a ranta jin motsin mik'ewar shi yasa ta raya da gaske yake kenan aikuwa da sauri ta d'ago dama yana tsaye bai tafi ba, inda yake tazo still tana kudundunan kawai sai ji yay ta kamo mashi riga, gaba d'aya ta cure a guri guda shi yadda tayi ma sai ya bashi dariya har jerarrun fararen hak'oran shi suka d'an bayyana,

"I will be back ai da an gama wankan" taji ya fad'a, da sauri ta girgiza mashi kai, d'an bud'a ido yay yace "kar in je?" Kai ta d'aga mashi, "Ok zaki taimaka man in yi kenan?" jimm ta d'an yi kafin a shagwabe tace "n...ni wllh Kunya nike ji" still dariyar yake dama wasa yake mata kawai komai nata nishad'i yake bashi ne, komawa yay ya zauna ya kai hannu ya janye duvet d'in Sumarta ta bayyana don ta kife fuskar a jikin mattress, bin ta yay da kallo cike da k'auna yana jin kaman don ita zuciyar shi ke beating, kiran ta yay ta amsa ba tare da ta d'ago ba yace tunda tana jin kunya zai k'yaleta yaje yayi amman har sai yaushe zata daina jin kunyar ta fara taimaka mashi wurin yin wanka, d'an jimm tay sai murmushi take zuciyarta ce ta tuno mata da zancen zuwa wurin Fanan da yayi kan tayi mashi wanka bata san lokacin data furta mashi gobe ba, jinjina kai yay yace promise ta d'aga mashi nata kan, ce mata yay to ta tashi ya taimaka mata ta shirya, girgiza mashi kai tayi murya can k'asa tace yaje yayi wankan zata shirya, hannu ya kai ya shafi sumar ta ya furta "Ok My Baby" daga haka ya mik'e, ta ji lokacin da ya tashi saida ta d'an bashi lokaci sannan ta d'ago ganin bata gan shi ba yasa ta tashi zaune ta juya hanyar laundry ta d'aga kai daidai zai tura kopar kawai sai gani tay ya d'ago mata hannu alamar yasan tana kallon shi, dariya ta saki ta maido kan ta k'asa,
Chapter 7 · 0% Book details