← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 211

Sashe 181

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Nasan saboda abubuwan da suka ta6a faruwa tsakani na da Sister ɗinka ne yasa zasu ƙi goyon bayan ka aure ne amman ai i'm a changed person now, na canza tun ba yanzu ba kuma nayi dana sanin komai bazan sake ba, yanzu nasan da mai kuɗi da wanda baya dashi duk ɗaya ne at least they should give us chance zan tabbatar masu da na canza gaba ɗaya bazan basu matsala ba" cikin breaking voice take Maganar gaba ɗaya tausayinta ya kama shi don daga yadda take yin Maganar ya tabbatar da gaske tana son shi kuma yaji ya amince da cewa ta canza ɗin, jin yayi shiru tace mashi in shi bai son tane to zata haƙura amman ya sani tana ƙaunarshi kuma ta fara son shi ne tunda ta fara ganinshi wannan dalilin ne yasa suka shaƙu bata gane hakan bane sai yanzu da sauri yace mata a'a wllh shima yanzu yaji yana son ta to amman kowa gani yake hakan ba mai yuwuwa bane za'a iya samun matsala don ba lalle iyayenta su Amince ba, katse shi tayi tace ita buƙatarta itace shima ya sota ya kuma amince zai aureta Maganar iyayenta zata yi duk yadda zata yi in ma basu amince ba tasa su amince yace mata shikenan shima yana sonta kuma zai je yanzu suyi magana da gwaggon shi zai nuna mata ta canza yasan zata amince tunda tana da sauƙin kai tace Ok tare da yi mashi godiya yana murmushi yace to ta daina yin kuka bai jin daɗin hakan ace tana kuka saboda shi, a hankali tace ai ba kuka take ba yace shida ya santa sosae ai daya ji muryarta zai gane tace to ta bari sai kuma ta ƙara cewa ai duk laifin shi ne da son shi yay mata babban kamu yay yar dariya yace to ai shidai yasan abota suke bai san ya akai abun ya koma haka ba nan ta shiga bashi labarin bayan ta dawo gida gaba ɗaya ta shiga damuwar rashin shi a kusa da ita kullum cikin tunaninshi take nan ta gane son shi take yace to ai shima duk hakan ya faru dashi bayan tafiyarta ko abinci bai mashi daɗi duk sai ya rinƙa jin shi kamar mara lafiya har Uncle ɗin shi saida ya gane saboda tafiyarta ne ya shiga damuwa haka a School ma Friends ɗinshi suna ta tambayarshi mike damunshi koda ya faɗi masu saboda tafiyarta ne sai suka ce sonta yake shi kuma ya ƙaryata su yace kawai abota suke, tana murmushi tace duk sun faɗa son juna ba tare da sun sani ba yace hakane, daga haka suka shiga shan soyayya Farha ba wasa dama gata ruwa biyu ta wani bangaren a wurinta ba abun kunya bane don ta riga cewa tana son shi nan fa ta shiga yi mashi kalamai harda faɗi mashi irin soyayyar da zasu sha in suka zama married couple, shima Kamalun ba laifi ya shigo birni ya iya kalaman soyayya masu daɗi, sun ɗan ɗauki lokaci suna wayar kafin Farhar tace mashi ga Brother ɗinta yazo zata taimaka mashi yayi wani Assignment Kamalun yace Ok sukai sallama cike da nuna ƙaunar juna, bayan gama wayar zaune Kamal yay yanata sakin murmushi wani irin nashaɗi yake ji sai yanzu yake jin son Farhar sosae na shigarshi amman ada bai ta6a tunanin jin yana sonta ba don gani yake tafi ƙarfin shi ta ko ina, yana haka ya tuna da kalaman su Gwaggo zuciyar shi ta bashi yaje ya faɗi ma Gwaggon yadda sukai da ita da sauri ya miƙe ya nufi hanyar fita, bayan ya fito part ɗin Gwaggon ya nufa lokacin daya shiga a parlor ya isketa zaune tana kallo ruƙe da Abdallah yaron Amadu yana bacci, ciki ya shiga gabanshi na ɗan faɗuwa saboda fargabar kada ta ƙi amincewa da zancen Farhar, bayan ya zauna yay mata sannu da fulatanci idonta akan shi ta amsa mashi daga haka ya sunkuyar da kai ya rasa ta yadda zai sanar mata, tana ɗan murmushi da fullanci tace mashi ya akai ne ya ɗago cikin kama kai yace dama sunyi magana da Farhar ne Gwaggon tace to ya sukai da ita nan ya faɗi mata abunda tace na ta canza yanzu tasan mai kuɗi da talaka duk ɗaya ne bazata bada matsala ba in aka bata dama za'a tabbatar da haka, yar dariya Gwaggo tay tana kallon shi tace to ai su dama ba matsalarta suke hange ba ta iyayenta da za'a iya samu ba kamar Mahaifiyarta, da sauri ya tari numfashin Gwaggon yace suma tace ita tasan yadda zata sa su amince Gwaggon tay shiru kamar mai nazarin wani abu can ta tambayeshi yana Son Farhar ne da sauri ya sunkuyar da kai alamar kunya tace ita ya bata amsa ba wani sunkuyar da kai ba a yadda yake ya ɗaga mata kai alamar eh yana sonta tay ɗan jimm tanata kallon shi bayan ɗan wani lokaci tace ya tashi yaje zuwa da safe zata neme shi yace to tare da miƙewa yay mata saida safe ta amsa da Allah ya basu Alkhairi, bayan tafiyar shi tunani ta shiga yi a cikin ranta ita dai sam bata son Al'amarin ya haifar da fitina ƙarshe ta yanke zuwa ta sanar ma Hajiya kawai.

Washe gari ya kama Juma'a da safe wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Gwaggo ta nufi gidan Hajiya sai da ta tsaya a bakin gate suka gaisa da Securities wanda yanzu sun kai su Biyar don bayan Senator ya zama shugaban ƙasa an ƙaro wasu, bayan ta shiga a parlor bangaren Hajiyar ta isketa zaune tana ruƙe da ɗiyar Tk tana mata wasa da abubuwan wasa, da murmushi Gwaggo ta ƙarasa cikin parlon Hajiya ta ɗago tana mata maraba bayan ta zauna kan kujera suka gaisa,

"Ana wasa da ƙawa ne"

Gwaggo ta faɗa tana yar dariya Hajiyar tace wai ta hana uwar yin aiki ne shine ta riƙe mata ita take mata wayo duk su kai yar dariya, shiru Gwaggo tayi ta rasa ta ina zata fara yi mata Maganar data kawo ta don sai kuma taji tana jin nauyi,

"Ya akai Amaryar Mani kinyi shiru koda wani abune?" Hajiya ta faɗa idonta akan Gwaggon tana murmushi itama murmushin take mata tace eh,

"sai kuma ki kama kiyi shiru koda yake mufa yanzu surukai ne ko, to ina jin ki ya akai ne Allah yasa in ji Alkhairi" yar dariya Gwaggo tayi jin abunda Hajiyar tace na su surukai ne, a nutse ta fara faɗi mata tiryan tiryan yadda Kamal yay da Farha Hajiya ta ɗan ta6e baki tana murmushi take sauraronta har ta gama,

"To Ke Dije Matar Mani ina ruwan ki da shiga harkar yara irin haka, ta bayyana mashi tana son shi in shima yana sonta sai kiyi masu fatan alkhairi ba shikenan ba" shiru Gwaggo ta ɗanyi kafin tace "Dama ni kawai ina gudun abunda zaije ya dawo ne shiyasa",

"Mi zai je ya dawon?" ta tambaya ta kafeta da ido da ƙyar Gwaggon tace mata can bangaren iyayen Farhar kar azo hakan bai masu daɗi ba ƙarshe abun yazo ya haifar da bacin rai,
Chapter 181 · 0% Book details