← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 211

Sashe 138

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

sosae yaji dad'in yadda ya nuna damuwa don ya gane bai koma bacci ba, bayan yayi picking tambayar shi halin da ake ciki yay ya sanar mashi da an samu Doctor din gata can tana treating nata Haisam ya furta Alhamdulillah in sha Allah zata samu sauk'i kada ya damu shima sun samu Kusan irin problem d'in da second wife en shi Sameer ya furta Ok, cike da tsokana yace mashi amman wai shi ya akai ya bari har hakan ta faru ma yana wani irin murmushi yace shi da yake da aure ma ya bari hakan ya faru balle shi da wannan ne first time en shi, yar dariya Haisam yay yace kawai dai ya fad'i mashi he lost control ya d'age gira yana murmushin gefe yace he never thought haka abun yake, dariya mai sauti Haisam yay kafin yace ai da ya tsaya yana ta cutar kanshi Sameer d'in ya furta wllh sukai dariya, kafin suyi sallama yace mashi pls ya lalla6ata sosae ya furta Ok, duk yadda likitar taso Fauzy ta zauna ruwan abun yaci tura sai faman koke koke take tana fad'in zafi bazata iya ba sai fama take da ita, jin kukanta yayi yawa ya sashi dawowa cikin toilet d'in ya tambayi ya akai likitar tayi mashi bayanin tak'i ta zauna ruwan ne yadda yakamata da bud'ar bakin shi sai cewa yay to dole sai ta zauna ne, ba don shine yayi Maganar ba daya samu amsa daidai dashi dama ya bata haushi yadda taga yayi ma Yarinyar, amsa ta bashi da eh Saboda ta samu rauni ne dole sai tana zama ruwan ne zata warke ya jinjina kai alamar gamsuwa kafin ya maida idon shi kan Fauzy da ta d'an d'osana ta zauna a bakin bathtub tana ta jan majina tare da yar sheshsheka, tambayar likitan yay daga zaman ruwan zafin sai mi tace tana buk'atar taci Abinci sai tasha pain relievers, tambayarta yay tazo da magungunan tace eh akwai wasu da zata bata yace Ok taje kawai ta aje mashi su nan zai sakata a ruwan tace Ok amman yanzu wannan tasan yasha iska akwae buk'atar a canza wani yace Ok ta canza, har ta juya ya tambayi tsawon lokacin da zata yi a ruwan ta fad'i mashi kafin tace ya bita a hankali yadda ruwan zai shigeta yadda ake so yace Ok, da biyu ta fad'i hakan don a tunaninta yana iya cewa ya gwada mata k'arfi, bayan fitar likitan rarrashin Fauzy ya shiga yi cikin kwantar da murya kai kace bai iya hakan ba, kuka taci gaba da yi tana cewa ita dai bazata iya shiga ba zafi yake k'ara mata, shiru yayi ya rasa yadda zai yi mata idon shi akanta sai faman juye juyen ciwo take, k'arshe dai dole saidai k'arfin ya gwada mata ya d'auketa cak tana ta kuka kamar za'a ma k'aramar yarinya wanka, daga baya da ruwan ya shigeta sosae ta d'an d'auki lokaci a ciki sai gashi ta fara jin dad'in shi ta saki jiki, bayan ta d'auki lokacin da aka fad'i mashi ya canza ruwan ya shiga yi mata wanka bata yi yunk'urin hana shi ba don tasan ba lalle ya k'yaleta ba gashi dama gaba d'aya ba k'arfi a jikinta saidai kawai ta runtse idanunta, bayan ya gama yi mata yace mata tayi na tsarki yana tsaye tayi ta gama ya d'aukko babban towel ya rufa mata ya sake d'aukko wani short ya lulluba mata a kai ya kara d'aukkota suka fito cikin d'akin, a saman gado ya d'aurata ya mik'e ya nufi wurin dressing mirror, mai da yake amfani dashi ya d'aukko yazo ya shafa mata yana ta kallonta har lokacin idanunta a rufe suke, bayan ya maida mai d'in wurin press d'in shi ya nufa ya bud'e yay d'an jimm yana tunanin kayan da zai d'aukko mata tasa kafin zuwa da safe, wasu riga da wando masu taushi ya d'aukko mata duk da yasan zasu yi mata yawa sosae amman zata fi jin dad'in su, shi ya saka mata kayan ganin kanta ya tsane yasa bai yi tunanin a busar dashi ba, ana gama saka kayan ta kwanta duk wannan abun bata bari ta had'a ido dashi ba, ganin yadda ta takure ya ja mata Duvet tare da mik'ewa ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin, lamo Fauzy tay duk ta damu tunaninta yanzu taya zata je wurin su Aunty Mareeya a haka ta fara yin gyangyad'i, ya d'an d'auki lokaci sannan ya dawo yana d'auke da wani madaidaicin tray ya aje a saman table, cup d'in tea ne mai k'auri sai bread da wainar kwai Kitchen yaje yasa aka had'o mashi, wurinta ya nufa har tayi bacci kana ganin yanayin da take yin shi zaka gane shi is not alright, bai sha wahalar tashinta ba don baccin ba wani mai nauyi bane, farko nunawa tayi ta k'oshi kaman zata yi kuka da yayi mata Maganar Abincin saida ya rarrasheta sannan da kanshi ya fara bata, ba laifi ta d'an ci da yawa don wani irin fayau cikin ta yay mata, bayan ta nuna ta k'oshi tana niyyar kwanciya da sauri yace ta bari tasha magani sai ta kwanta, a saman nightstand ya d'aukko su guda biyu ne kowanne an rubuta yadda za'a sha ya 6allo mata da sauran tea din data rage ya bata tasha bayan ta gama fuska a yamutse tace ruwa zata sha da sauri ya furta Ok ya nufi hanyar fita, a hankali ta juya tana kallon bayan shi ganin shi take kamar bashi ba, a parlor ya d'aukko bottle water tare da glass cup ya kawo mata bayan ya bud'e ya zuba mata ya kai bakinta zai bata ta d'aga hannu ta amsa fuskarta na kallon gefe, kaman rabi tasha ta mik'a mashi ya amsa suma ya aje su saman table, zaune tayi bata kwanta ba yay tsaye yana kallonta ya lura da kaman fushi take dashi don tak'i ta ko kalle shi, cike da k'arfin hali ta fara kokarin mikewa yana ganin haka ya tambayeta mi take so ne tace mashi d'akin da suke zata koma da sauri ya matsa ya kamata yana fad'in taya zata koma a wannan halin ta kwanta anan ai lafiya lou zuwa da safe in ta k'ara samun sauk'i sai ta koma, shiru tay dama dai kawai ta fad'a ne amman itama ba son komawa take a wannan halin ba kuma tunda su Aunty suka ga ta dad'e tasan tuni ma sun zargi wani abu, janyewa tayi daga kamatan da yayi ta kwanta yaja mata duvet, d'auke tray d'in yay ya nufi hanyar fita, a parlor ya zauna ya idasa cinye sauran data rage don shima yunwa yake ji bayan ya gama anan ya bar kayan ya dawo cikin bedroom d'in, toilet ya wuce bayan wasu mintuna ya fito k'ugunshi d'aure da towel ya nufi press d'in shi, shima riga da wandon ya d'aukko ya fara sakawa yana yi yana kallon Fauzy bayan ya gama kimtsawa ya nufi gadon saida ya kashe wutar d'akin sannan ya daidaita kwanciyar shi, hannu ya kai zai rungumota jikinshi kawai sai ji yayi ta k'i bari yayi hakan nan ya gane idonta biyu ko kuma baccin bai d'auketa ba sosae, matsawa yay ya had'e jikinsu tana ta son k'wacewa ya kai bakin shi saitin kunnanta cikin magana mai kamar rad'a ya fara magana, "I'm very sorry Wife, I know I hurt you kiyi hak'uri pls bansan ya akai komai ya faru haka ba I don't know what came over me" sheshshekarta da yaji k'asa k'asa yasa shi gane kuka take, k'ok'arin juyo ta ya shiga yi ta dawo suna facing juna da yake a d'an kwai haske ya kai hannu yana goge mata k'wallan yana k'ara bata hak'uri yana bai san ya akai hakan ta faru ba, cikin Muryar kuka tace amman ba saida taita rok'on shi ba kan yayi hak'uri ya k'yaleta ba amman ya k'iya, a rud'e yace mata ya rasa control ne he didn't know that's how it was gaba d'aya tun farko ma baida niyyar wannan, shiru tayi bata ce komai ba ya shiga shafa gefen fuskarta yana fad'in Pls she should forgive her husband yasan yayi mata ba daidai ba, aka ce tsakanin mata da miji sai Allah ce mashi tayi shikenan tayi hak'urin, rungumeta yay sosae yana murmushi yayi mata godiya tare da Fad'in he knows he is blessed daya sameta matsayin mata shiru ta d'an yi sai kuma k'asa k'asa ta furta itama haka ya k'ara k'ank'ameta cike da jin dad'i yace "I Love You so much Babes" yay Maganar tare da pecking kumatunta, rufe ido tayi a ranta ta raya wato dama daya ta6a ce mata ba yanzu zai fad'i mata hakan ba yana nufin sai wannan lokacin kenan, shiru sukai wani irin nishad'i suke ji ba ma dai kamar Sameer ji yake yau is the happiest day of his life, jin saukar numfashinta a nutse yasa shi gane tayi bacci ya gyara masu kwanciya bada jimawa ba shima baccin ya d'auke shi.
Chapter 138 · 0% Book details