← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 211

Sashe 114

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari talata bayan la'asar Hajiya ta iso, Haisam ne yaje ya d'aukko ta a Airport, bayan sun iso gidan gaba d'aya duk suna a part d'in mai jego Hajiya ta nufi can shi kuma Haisam ya nufi part d'inta don ya kai mata kayanta, suna zaune a falo harda mai jego har sunyi wankan yamma tana sanye da half gown ta sabuwar atamfa golden tayi yar kwalliyarta ta fito fess haka yaran ma duk anyi masu wanka an saka masu kaya iri daya light blue abun saidai ace Masha Allah d'aya na hannun k'awar Mom da tazo barka d'ayan kuma na a hannun d'iyarta wadda k'awar Jidderh ce dama tun d'azun aketa zuwa barka harda Abokan Dad ba'a ma dad'e da maido yaran ba daga part d'in Dad d'in harda kyautar kud'i aka yi masu, Hajiya na yin sallama gaba d'aya su twins dasu Yasmeen suka nufota da gudu suna fad'in "Oyoyo Granny" duk suka k'ank'ame ta Jidderh ma ta taso ta nufota tana mata Oyoyo, Hajiyar na dariya tace ma su Twins sai sun karyata tun bata ga sabon angon nata ba salon yace bai sonta duk suka d'ago suna dariya tace su shiga ciki, mik'ewa Mom da Aunty sukai suna mata sannu da zuwa tana amsawa ta nufi kujera ta zauna su twins d'in ma duk suka zauna a kusa da ita sun shishshige mata, zama su Aunty sukai suka shiga gaishe da ita tare da yi mata an zo lafiya K'awar Aunty ma ta gaishe da ita tare da yi mata anzo lafiya haka d'iyarta ma, Mom ce ta amso Babyn hannun Friend d'in tata ta kawo ma Hajiya Jidderh kuma ta amso na hannun d'iyar matar k'awarta ta zo gefen Hajiya dashi tana nuna mata, bin su da kallo Hajiya tay fuskarta d'auke da fara'a ta shiga fad'in Ma sha Allah, mik'ewa K'awar Mom tayi tay masu sallama tare da yi ma Hajiya barka suka tafi Mom ta rakasu, juyawa Hajiya tayi ta kalli Fatuu dake d'an murmushi tace "Sannu da kokari Fateema, sannu kin dai yi aiki ba kad'an ba wllh yara haka Tubarkallah, to Allah ubangiji ya raya mana ya Albarkaci rayuwar su kema ya k'ara maki lafiyar shayarwa" gaba d'aya harda su twins suka had'a baki wurin amsawa da Amin,

"To ni bansan wanene sabon Angon ba bansan waye kuma d'an ba a cikin su a bambance man" Hajiya ta fad'a da fara'a, gaba d'aya su Jidderh suka zuba masu ido suna kokarin bambanta mata saidai duk sun kasa Saboda duk bacci jariran ke yi balle su bambance su ta ido sai faman canki canka suke abun ma sai ya zama abun nishad'i Aunty nata dariya don ita tasan kowanne Saboda tare da Mom suka kaisu wurin Dad haka lokacin da za'a maido su ita Dad ya kira taje ta amso su tare da Yasmeen lokacin Jidderh bata a d'akin tun lokacin ta ruk'e Adam aka ba k'awar Mom sai d'iyarta aka bata Aliyun, ita kanta Yasmeen da suka amso su tare duk ta rud'e ta kasa bambanta su, Hajiya sai faman dariya take tana fad'in lalle ashe aiki ne tantance su, Haisam ne ya shigo Hajiya ta d'aga kai ta kalle shi tace "to kai Baban su sai kazo ka bambanta man su tunda duk sun kasa" murmushi yay kawai ya nemi kujera ya zauna tace ya zai zauna ko shima bazai iya banbance su bane ya d'aga mata kai alamar eh kafin cikin cool voice d'in shi yace duk suna bacci dama ta ido ake gane su, jinjina kai Hajiya tayi tace shima kenan sai ta idon zai iya gane su ya d'aga mata kai,

Aunty dake ta dariya tace to a tambayi Mom d'in su k'ilan ita ta gane su duk aka maida kallon kan Fatuu dake murmushi Hajiya tace tazo ta bambance mata su, mik'ewa tay ta matsa kusa dasu ta d'an sunkuya tana kallonsu, ta d'an d'auki lokaci kafin ta d'aga yatsa ta nuna na hannun Hajiya tace shine Hajiyar ta tambayi shine wa tana yar dariya tace Angonta,

"To wa zai tabbatar mana in daidai ta canka" Hajiya ta tambaya tana dariya Aunty tace daidai ta canka shine Hassan d'in don ta ruk'e tunda suka kaisu wurin Dad, da sauri Jidderh tace "Sis Fatuu ya akai kike gane su don Allah?" gaba d'aya akai dariya Hajiya tace tunda koda yaushe tana tare dasu tana k'are masu kallo dama zata iya samun abunda zata rink'a banbance su, duk su Yasmeen suka hau rok'on ta nuna masu yadda suma zasu rink'a gane su, nuna masu girar Adam d'in tayi tace tanan ta gane shi don zanen tashi ya d'an fi lankwasawa kad'an aikuwa duk suka maida idanun nasu kan su harda Hajiya Aunty ma ta taso daga kujerar ta tazo don ta gani sai gashi sun ga hakanne amman sai mutum ya natsu sosae zai gane, Mom ce ta dawo d'akin tana d'auke da madaidaicin tray an d'auro ruwa da lemu da glass cup Dad na biye da ita, ganin suna ta dariya yasa ta tambayi ya akai Aunty ta bata labari Dad yay dariya yace shima in dai ba idon su biyu ba bazai gane ba, zama yay kan kujera ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe da Hajiya tare da yi mata anzo lafiya bayan ta amsa yace bai gidanne sun fita tare da bak'i tace ba komai sai kuma tayi mashi barka, saman c-table Mom ta d'aura tray din tace ma Hajiya a kawo Abinci anan ne tace mata a'a bata jin yunwa yanzu, hira suka shiga yi cike da nishad'i ana haka jariran suka farka daga bacci nan suka k'ara tantance su ta idon su, sai da akayi sallar Magrib sannan duk suka tashi don zuwa yin salla.

Washe gari wuraren k'arfe sha biyu na rana Fanan ta iso tare da Nameer suma Haisam ne yaje ya d'aukko su daga Airport tana sanye cikin brown coat dress tasa yar bak'ar himar sosae tayi kyau Nameer ma na sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt, gaba d'aya Fanan a k'agare take da taga jariran da suna hanyar zuwa gidan sai faman zumud'i take tana ma Haisam tambayoyi game dasu Nameer nata mata dariya, lokacin da suka isa ma'aikatan gidanne suka zo suka d'auki kayan su tare da yi masu sannu da zuwa suka nufi ciki, ba kowa parlon Fanan ta tambayi Haisam inda Fatun take ya nuna mata ta nufi part d'in da sauri shi kuma Haisam da Nameer suka tsaya don ganin an shiga da kayan nasu, lokacin da ta shiga parlon ba kowa hakan yasa ta nufi Bedroom d'in, Mom da Aunty sai Hajiya ne a ciki yaran gidan duk suna Makaranta Fatuu na a zaune tsakiyar gado tana sanye da doguwar rigar shadda tayi daurin kallabi mai kyau haka yaran ma suna sanye da fararen kaya suna bacci daga gefenta, da Sallama ta shiga duk suka kai idanun su kanta ta shiga ganin itace yasa gaba d'aya suka shiga yin murmushi harda Fatuu ta nufi gadon da sauri ta zauna a baki idonta akan yaran ta shiga sakin faffad'an Murmushin dad'i harda d'an yarfa hannu, saida ta gama kallon su sannan ta juyo tana gaishe dasu Mom Hajiya tace wato saboda zumud'in ganin yaranta sai yanzu zatai lokacin su tana yar dariya tace a'a, anzo lafiya suka yi mata ta amsa kafin duk suka yi mata barka tana ta washe baki idonta akan yaran take amsawa Fatuu ma ta gaishe da ita ta kalleta bayan ta amsa tace "Sannu sis, sannu da k'ok'ari don Allah. Look at them, very cute wllh" dariya kawai Fatun ke yi haka su Mom don gaba d'aya ta rud'e da ganin yaran, su Haisam ne suka shigo Nameer ya nufi gefen Hajiya ya zauna tare da gaishe da ita ta dafa Shoulder d'inshi tana mashi an zo lafiya bayan ya amsa ya gaishe dasu Mom suma duk suka yi mashi anzo lafiya, Hajiya ce tace mashi shi bai ga yaran nashi ba ya juya yana kallon su fuskar shi d'auke da Murmushi yace "Ma sha Allah, Allah ya raya mana su" gaba d'aya aka amsa da Amin, ganin yadda Fanan ta tsura masu ido yasa Hajiya tace to ta d'auke su mana da sauri tace "No, suna hutawa a k'yale su suyi baccin su in sun tashi na d'auke su suga Mom d'in su" Hajiyar tace to mai y'ay'a duk akai dariya, shiru Fatuu tay kamar mai tunanin wani abu idonta akan Fanan dake ta kallon yaran tana murmushi can ta kai hannu ta d'aukko Aliyu wato Hussein dake a kusa da ita hakan yasa Fanan kallonta kawai sai gani tay ta Mik'o mata shi tana d'an murmushi, kallon rashin fahimta ta bita da shi haka ma su Hajiya duk idanun su na akan su,

"Aunty Fanan gashi, na baki shi ",
da k'yar ta furta Maganar, d'an yamutsa fuska Fanan tay cikin d'aurewar kai tace "I..I don't understand you Sis Zarah", saida Fatuu ta had'iyi abu kafin tace "dama na fad'i ma Ya Haisam cewa in na haihu zan baki Babyn koda kuwa d'aya ne sai gashi Allah yasa na haifi biyu shine na baki d'in, Aunty Fanan wllh na baki shi har abada ga su Hajiya nan inason su zama shaida shiyasa nayi hakan a gaban su" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda karyewar da muryarta tayi, hannu Fanan ta kai da sauri ta rufe bakinta alamar Al'ajabin Maganar don abu ne da bata tsammaci ji ba, bin juna sukai da kallo ita da Fatun lokaci guda idanun Fanan suka ciko da k'walla cikin rawar murya ta furta "Yanzu Sis Zarah kina nufin duk wahalar da kika sha ta rainon cikin shi da kuma haifuwar shi kin bani shi ya zama nawa har abada?" Kai Fatuu ta jinjina mata itama idanunta sun ciko da k'walla kawai sai ji sukai Fanan d'in ta fashe da kuka itama Fatun k'wallan ne suka fara zubo mata gaba d'aya sun karya ma kowa zuciya can Fanan ta kai hannu ta karbe shi ta bishi da kallo tana murmushi,
Chapter 114 · 0% Book details