Sashe 25
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan taje Makarantar sosae Fauzy ta shiga tsokanar ta tana fad'in lalle da gani ba k'aramar soyewa sukai ba shiyasa ma ko tunawa da ita bata yi ba ace cikin kwana biyu ta k'ara canzawa har haske ta k'ara harda cewa Allah yasa hasken na rabo ne ita dai Fatuu dariya kawae take. Bayan an tashe su shi yazo ya dauke ta suka biya aka d'auki Mino tana ta murnar ganin Adda d'inta data kwana biyu bata gani ba, gidan Hajiya suka wuce don ya lura a G.r.a bazata yi karatun jarabawar ba sosae. Bayan komawar su sosae yake d'aga mata k'afa don tayi karatun yana kuma taimaka mata wurin k'ara yi mata bayanin wani abun da bata gane ba, a kwana a tashi ba wuya tuni sun fara jarabawar har ya rage saura yan kwana ki su gama, bayan sun fara da sati guda ne Haisam ya tafi Lagos wurin Fanan kwanan shi hud'u ya dawo, Ana saura kwana biyu su gama ranar laraba ya gama yi masu shirin zuwa Abuja harda Hajiya za'a tafi da sun gama jarabawar da kwana d'aya wato ranar Juma'a har su gwaggo sun san da zancen tafiyar don har an buga IV na programs d'in da za'ayi an aiko masu da shi IV d'in mai shegen kyau date d'in da za'ayi ya kama bayan gama jarabawar Fatuu da sati d'aya wato ranar Juma'a ta sama, cikin sa'a su Fatuu suka gama jarabawar sai farinciki suke lokacin Fauzy ke mata Maganar anko tace ta bari zata ma Jidderh magana in sun fiddo sai ta turo hoton shi, a ranar bayan Haisam yazo ya d'auketa sun koma gida ba K'aramin faranta ma juna sukai ba, da daddare ya d'auketa suka fita, shagon Kb mai d'inki suka fara zuwa ya amshi d'inkin dandatsetsen lace d'in daya bada a d'inka mata ita da Hajiya wanda ko ita Fatun bata san daya bada ba, sosae tayi murnar d'inkin gashi an mata Fav d'inkin ta wato straight skirt da riga fefflon irin mai bud'ewa daga k'asa yar daidai daidai hannun ma wani irin style akai mashi gwanin burgewa Hajiya ma riga Boubou akai mata harda kwalliyar bakin lace, sosae Fatuu tay murnar d'inkin abun yazo mata a surprise, bayan sun bar nan shagon Zee Collections suka wuce dama a wurinta ya siya leshin lokacin data kawo ba Jaka da takalma da gyalen da zasu hau dashi tace zata kawo mashi, cikin faran faran kaman ko yaushe ta tarbe su bayan sun zauna harda ita suka gaggaisa cike da nuna farinciki tace ma Fatuu ashe dai fatan su ya tabbata tace tayi murna sosae wllh data ji zancen Auren nasu, ita dai Fatuu murmushi kawae take Zee d'in tace ai in sha Allahu zata je Abujar, daga baya ta d'aukko mashi sak'on sukai sallama ta rako su waje. Saida suka tsaya wani Eatery ya siya mata kayan kwalama sannan suka wuce gida. Ranar Friday bayan gama sallar Juma'a suka hau shirin tafiya, sabon lace d'in wanda red color ne da torch d'in ash Fatuu ta saka sosae yay kyau d'inkin ya hau dashi Over, light make up tayi ta parker gashinta ta k'asa da ribbon dark ash, d'aurin kallabi Zarah buhari tayi ta yadda tulin gashinta ya lek'o ta k'asa, gaba d'aya jewellery d'in da ta saka silver ne suma sababbi ne masu tsada, bayan ta gama ta d'aukko takalman wanda ankle strap ne irin masu igiya da tsini sosae sai purse d'in su mai d'aukar ido gaba d'aya ash ne kalar kwalliyar lace d'in, Haisam bai nan ya tafi G.r.a ya dawo tuni shima ya gama shiryawa da ya dawo tafiya zasu yi, bayan ta gama shirin hanyar fita ta nufa jin ta take tamkar wata sarauniya sai faman murmushi take, tana shigowa cikin parlor Mino ta shigo tazo yin rakiya su sai cikin sati mai zuwa zasu je, waro ido tay ganin ta haka da mamaki ta "Furta Adda Fatuu kece haka!" Dariya kawae Fatun take ta taho da d'an gudu gudu tana zuwa ta rungumeta tana fad'in wllh tayi kyau sosae, part d'in Hajiya tace mata suje Minon tace dama gwaggo ma na can itama tazo yi masu rakiya Airport, lokacin da suka je itama Hajiya ta shirya cikin nata lace d'in duk suna zaune a parlorn harda Saude da Tk nan fa aka hau yabon gayun Fatun har Hajiya na fad'in wato Saboda son kai na Haisam shine ita akai mata d'inki mai kyau ita kuma akai mata burgujejiyar riga ai da itama sai ayi mata irin na Fateemar ta cakare duk suka sa dariya, a gefen gwaggo ta zauna suka gaisa, bata dad'e da zuwa ba Haisam d'in ya dawo yana sanye da farin danyen voile haka takalman shi da agogon shi duk farare ne, gaisawa sukai yace ma Hajiya in sun gama zasu iya tafiya tace to duk suka mik'e idon shi akan Fatuu dake sakar mashi murmushi, a gaban shi ta tsaya bayan duk sun tafi ya lumshe ido Slowly ya furta tayi kyau tace ai shi yasa tayi kyaun, tambayarta yay an fiddo kayan su tace a'a yace Ok suje suka nufi hanyar fita, bayan sun fito Tk yace ma ya biyo shi suka nufi part d'in nasu, basu d'auki lokaci ba suka dawo Tk na janye da trolley d'in Fatuu da wata jaka Haisam ma na janye da madaidaicin trolley, a boot aka saka su, Hajiya da gwaggo da Saude suka shiga Jeep Tk ne zai ja sai Mino da Fatuu da Haisam suka shiga k'aramar Mota Officer ne zai ja su, bayan duk sun shiga Motocin suka tunkari gate, bayan sun fito a daidai shagon Amadu Tk ya tsaya don shima yace mashi zai yi rakiyar, fitowa yayi bayan ya kulle shagon ya shiga gaban Motar sannan suka tafi, suna hanya Fauzy ta kira Fatuu ta tambayi sun fito tace mata eh tace to su had'e a Airport d'in, basu dad'e da isa ba Fauzy ta k'araso nan aka hau yin sallama yau su yar Fillo za'a hau Jirgi..........
*ASM 079*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........A business class na jirgi Suke kowa da kujerar shi ta Fatuu na kusa data Haisam sai Hajiya na daga d'an can gefe da yake kujerun ba had'e suke da juna ba saidae ta Haisam data Fatuu gab d'in su kad'an ne, in ka kalleta bazaka ta6a cewa hawa jirginta na farko bane don bata nuna wani k'auyanci ba amman fa gaba d'aya a tsorace take tun farkon ganin jirgin kafin su shigo yadda ta ganshi wani gingimeme dashi bata zaci haka yake ba don bata ta6a ganin shi a fili ba sai a sama kuma bai kai girman haka ba take ganin shi, sai faman d'an wuwwurga ido take tana k'are ma wurin kallo ta yadda baza'a ga k'auyancin ta ba dama kuma basu da yawa a class d'in kowa kuma harkar gaban shi yake, hannu Haisam ya kai ya kamo hannun ta da sauri ta kalleshi yay mata murmushi itama ta mayar mashi, nuna mata yadda zata saka seat belt in an sanar da ayi hakan ya shiga yi bayan ya gama yace tasa ya gani hannunta har d'an rawa yake ta shiga sakawa bayan ta gama ta kalle shi, murmushi yay mata ya jinjina mata kai had'i da d'an lumshe ido a hankali yace ta cire, ba'a dad'e ba aka sanar ai fastening seat belt ba 6ata lokaci Fatuu tasa har saida ta kalli Haisam yay mata murmushi, lokacin da jirgin ya fara tafiya wani irin bugu k'irjinta ya fara yi da zai d'aga sama ba shiri ta sauke kanta ta runtse idanunta da k'arfi Haisam ya kai hannu ya ruk'e nata da k'arfi, bayan ya kai kololuwa ya mik'i hanya ta bud'e idon ta juya ta kalle shi slowly ya furta "Are u okey?" Kai ta d'aga mashi ta d'an tsuke baki da d'an waro ido hakan har saida yasa shi yin yar dariya, daga baya sai gashi ta saki jiki taci gaba da yin kallo ma ita kuwa Hajiya ma d'an kishingid'awa tay idanunta a rufe da alama bacci take, Lokacin da suka iso bayan an sanar sun maida seat belt tun kan su k'araso yadda tayi da zai tashi haka ta k'ara yi da zasu sauka saidae na yanzu ma yafi don kamar zata sa kuka jikinta har rawa yake Haisam d'in ya k'ara ruk'e hannunta gam har jirgin ya tsaya sannan yace ta Kantar da hankalinta sun iso ta bud'e idanun tana numfarfashi, shi ya cire mata seat belt d'in tana mik'ewa tace mashi juwa take gani ya maida ta kan seat ya zaunar da ita Hajiya ta matso tana tambayar Yaya ko amai take ji yace mata a'a she feels dizzy, sannu Hajiyar tayi mata tace ai tama yi kokari tunda boarding d'in ta na farko ne wasu da zasu yi ta amai wasu harda bayan gida, bayan d'an lokaci ta mik'e cike da kulawa Haisam d'in yace mata zata iya tafiya tana murmushi ta d'aga mashi kai Hajiya sai sannu take mata,