Sashe 3
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sai bayan da aka yi isha sannan Haisam ya dawo lokacin suma sun dawo cikin parlon, Fatuu na ganin shi ta gane yaje part d'in su don har ya canzo kaya, har ya k'araso idon shi na akan Fatuu da tunda ta kalle shi ta maida idon ta akan Tv, Fanan ce tay mashi sannu da zuwa da murmushi ya amsa mata Fatuu tay d'an jimm zuciyar ta ta raya mata itama tace mashi mana, da k'yar ta d'an kalle shi da yake Facing d'in su yake murya na d'an rawa tace mashi sannu da zuwan ya jinjina mata kai kawae ya zuba mata ido da sauri ta maida nata kan Tv, wani abu take ji mai kamar haushin shi a ranta, bai dad'e da zama ba Saude tazo ta sanar dasu ta shirya Table, Hajiya ce ta fara mik'ewa tace masu su taso, bayan duk sun zauna Saude na niyyar Serving nasu bayan ta gama da Hajiya tace mata taje kawae, kallon Fatuu tay tace ta tashi tay Serving bak'inta ta d'aga mata kai, Haisam ta fara zuba mawa tana yi tana tambayar shi in yayi ya kafeta da kaifafan idanuwan shi da suke a d'an lumshe dasu yake bata amsa ko da kai gaba d'aya yana neman rikita ta, bayan ta gama ta juya kan Fanan itama ta zuba mata saidae d'an kad'an tasa ta zuba mata, zubawa itama tayi bada yawa sosae ba duk suka fara ci a nutse, baka jin komai sai k'arar cokulla, duk in ta saci kallon Haisam sai taga ita yake kallo yanayin fuskarta kamar a d'aure, tana lura da Fanan sam bata wani cin Abincin juya cokali ya fi yawa sai an d'auki lokaci take d'an d'iba ta kai baki tay ta taunar shi sai kaga kaman tana ci, duk Fatuu sai taji ba dad'i don gani take itace silar damuwar ta, can dae tay k'arfin hali murya na d'an rawa tace "A...unty Fanan baki ci sosae" da sauri Fanan d'in ta kalleta tay mata murmushi murya k'asa k'asa tace mata tana ci mana, Hajiya da ta d'ago ta kalli Fanan d'in da d'an murmushi tace an sha tafiya ko gajiya ce tasa ta kasa ci sosae in tana son wani abu ta fad'i sai a had'a mata, d'an girgiza ma Hajiyar kai tay tace wannan ma lafiya lou, kad'an ta k'ara ta mik'e duk suka kalleta tana murmushi tace ta k'oshi bata da appetite ne zata k'ara da tea daga haka ta fita daga cikin Kujerar ta nufi hanyar Bedroom idon Haisam a kanta ita kuma Fatuu lokacin ta samu damar kallonshi sosae bata Ankara ba ya juyo suka had'a ido, kayataccen murmushi taga ya sakar mata ta bishi da ido kawae, kaman daga sama suka ji muryar Hajiya tana fad'in suyi sauri su gama ba sai suje suji dad'in kallon Junan ba, sosae kunya ta kama Fatuu ta sunkuyar da kai, da k'yar ta cinye Abincin ta mik'e tace ma Hajiya saida safe ta kalleta tace to Allah ya basu Alkhairi,
bayan ta fita daga cikin Kujerun Hajiya ta tsaida ita tace taje suyi sallama da Yayar ta tace to ta nufi hanyar Corridor tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, d'an jimm tay a bakin kopar visitor room d'in gabanta na d'an fad'uwa hakanan fargabar shiga take ji, can dai ta tura kopar a hankali tare da yin yar sallama, a kwance ta hangota ta kife fuska a jikin pillow kai da gani kasan da wuya in ba kuka take ba, bugun k'irjin Fatuu ne ya k'aru da sauri ta juya zata fita don ta lura kaman bata ji sallamar data yi ba, har zata fita taji Muryar ta ta kira Sunanta, juyowa Fatuu tay ta kalle ta taga ta tashi zaune, a sanyaye ta nufi gadon ta nuna mata gefen ta alamar ta zauna Fatuu na kallon idonta ta gane kuka take duk da goge idon da ta yi, shiru suka d'an yi kafin Fanan d'in tace mata har ta gama cin Abincin ta d'aga mata kai ta jinjina nata itama, shiru suka k'ara yi idanun Fatuu a k'asa wani irin tausayin Fanan d'in take ji can ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da k'walla cikin karyayyar murya tace "Aunty Fanan don Allah kiyi hak'uri wllh ban ta6a nuna mashi ina son shi ba, ko wannan sak'on da kika gani bani na tura mashi ba wllh k'awata ce kuma sai da na nuna mata ban ji dad'i ba daga baya ma na goge shi ko tambayar shi zaki ko ki duba zaki ga an goge" idanun Fanan d'in suma cike tabb da k'walla take kallon ta harda Murmushin k'arfin hali har ta gama sannan ta kai hannu ta janyota ta kwantar da kanta a saman shoulder d'inta cikin sanyin murya tace 'its okey Zaraah I understand everything, kema bake kika d'aura ma kan ki ba, komai da yake Faruwa akan mutum was already written, Allah ya bamu ikon ruk'e Amanar juna and am sorry for what u'r going through itama Friend d'in tak'i taga kina wahala ne yasa ta yanke turo sak'on" shiru Fatuu tay wani irin tausayin Fanan ya mamaye mata zuciya, can ta d'ago daga kan kafad'ar tata ta kalleta a sanyaye tace mata to don Allah ta daina yin kuka bata jin dad'in ganin ta haka sai taita ganin kaman Saboda ita ne, da sauri ta girgiza mata kai tace ta bar sama ranta hakan kawai abunne gaba d'aya yazo mata a bazata so dole sai a hankali zata washe nan ta sanar mata da bata san komai ba sai da aka turo sak'on ita ta fara gani, sosae Fatuu taji ba dad'i Fuskarta a yamutse take kallonta can Fanan d'in tace mata ta k'ara girma sosae tana murmushi harda tambayar ta ta kai 20yrs ne yanzu, Fatun tace mata a'a 19 take ta jinjina kai tace tana da jiki mai kyau ita dai d'an murmushi kawai tayi sai kuma tace mata itama ai tana da kyaun jiki ga tsawo ita kuwa gajera ce har saida tasa Fanan d'in yar dariya,
tambayarta karatun ta tayi tace ta kusa gamawa ko, ta bata amsa da yanzu zasu kama nursing 2 sai su shiga 3 daga nan zasu gama, jinjina kai tayi tace Allah ya basu sa'a bayan Fatuu ta amsa tace "in kika gama nasan U.S zaki dawo sai kiyi Medicine ki zama likita da kike buri" yar dariya Fatun tayi kawai, suna haka aka turo kopar d'akin duk suka kai idanunsa wurin, Haisam ne ya shigo hannun shi ruk'e da tea cup asaman saucer, har saida gaban Fatuu ya d'an fad'i ganin shi, ciki ya shigo ya nufo wurin su,a gaban Fanan ya tsaya idonta akan shi da d'an murmushi ya mik'a mata cup d'in tea d'in ta amsa a hankali ta furta mashi thanks Fuskar shi a sake ya jinjina mata kai, d'agowa yay idon shi akan Fatuu da ke kallon k'asa sai taji duk ta takura, mik'ewa tay ta kalli Fanan tace mata saida safe tace ta tsaya su sha tea d'in mana da d'an murmushi ta girgiza mata kai tace taci Abinci sosae dama saida safen ta shigo yi mata, godiya tayi mata tace sai sun had'u da safe daga haka Fatun ta juya ba tare data kalli inda yake ba ta nufi k'opa ta fuce. Tana tafiya tana ta zancen zuci har ta k'araso part d'in su, tun a parlor ta gasgata Haisam ya shigo jin k'amshin turaren shi,