Sashe 13
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan ya tsagaita yin dariyar yace "ni yaushe za'a canza man suna ne" d'age mashi gira tay "kana so ne?" da murmushi ya d'aga mata kai, tace "to wane suna kake so?" wani kallo yay mata mai kaman harara yace shi zai fad'i mata shi da ya canza mata ita ta fad'i mashi, d'an jimm tay ta kanne ido guda alamar tunani can tace "To Sweetheart?" shiru ya d'an yi sai kuma ya girgiza mata kai yace bai son shi ai dama tana ce mashi haka tace to ai da hakanan take ce mashi ko yanzu kuma da dalili yace to ai shiyasa yake son a canza, jimm ta k'ara yi tace to tunda shi yana da jinin larabawa bari ta rink'a ce mashi Habiby waro ido yay jin irin sunan da Mom d'in shi ke fad'a mashi ne ya girgiza mata kai yace a canza wani tace to Honey, wannan karon yar dariya yay yace to ai duk kusan d'aya ne da Sweetheart d'in, d'an yamutsa fuska tay ta d'an Jujjuya jiki cike da shagwaba tace to ita ta rud'e ta rasa wanda zata za6o yay shiru dae yana bin ta da ido da murmushi can tace "Yauwa to Hubby" Dariya yay kawai bata san shi yadda take mashi Maganar bane yake burgeshi shiyasa yake ta jan abun, tambayar shi tay yayi ya d'aga mata kai harda d'an d'aga hannuwa ta jinjina su alamar jin dad'i, shiru sukai suna ta kallon juna kowanne face d'in shi d'auke da Murmushi can yace mata mi ta zauna yi k'asa ne bata je Parlor ba ko ta hau gado tace mashi Sallah tayi da ta gama Addu'a sai kuma tayi zaune, tambayar ta yay Addu'ar mi tayi tace da yawa, hannu ya kai ya kama hannunta ya d'agata ta zauna sosae suna kallon juna yace to ta fad'a mashi Addu'o'in da ta yi,
"Nayi ma mamana na rok'i Allah ya jaddada rahama a gare ta da sauran wanda suka rasu...." jinjina kai yay Slowly ya furta "Ameen" cigaba tayi "Sai Baffana da gwaggo harda Hajiya na rok'i Allah ya k'ara masu lafiya da nisan kwana mai Albarka" lumshe ido yay, ta sake cewa "Aunty Fanan ma nayi mata Allah ya bata lafiya ya kuma had'a kan mu, sai su Kawu Amadu da sauran yan'uwa harda k'awaye na su Fauzy na rok'i Allah itama ya bata Miji na gari wanda zai sota tsakani da Allah ya riketa da Amana harda su Mino ma" jinjina mata kai yay a hankali yace Allah ya amsa, shiru tay yace Shikenan ta d'aga mashi kai, wani kallo yay mata mai kaman harara tana ganin haka tasa dariya tace "to ai kai fa na fara yi mawa Allah, na rok'i Allah ya k'ara ma rayuwar ka Albarka yasa ka gama da iyayen ka lafiya ya k'ara maka lafiya da Arziki mai Albarka ya biya maka dukkan bukatunka na Alkhairi yasa ka dawwama a cikin farinciki ya kuma bani ikon yi maka biyayya" lumshe ido yay ya saki k'ayataccen murmushi sosae yaji dadin Addu'oin ya amsa mata da Amin, ce mata yay ita bata ma kanta bane tace tayi yace to ta fad'i mashi wacce tayi ma kanta wani kallo tay mashi tana dariya da alamun kunyar fad'i take ji yace yana jin ta, cikin jin kunya tace "Na rok'i Allah yasa....in samu ciki in haiho yaro mai kama da kai sak" da k'yar ta k'arasa Maganar tana rufe fuskarta da hannunta d'aya, yana murmushi yace bata son mai kama da ita ta d'aga mashi kai, tambayar ta yay miyasa take son mai kama da shi tace "Saboda nasan ba kowane lokaci zamu kasan ce a tare ba kaga in na haifi mai kama da kai ko baka nan zan rage kewar ka in ta kallon fuskar shi" tana yar dariya ta k'arasa Maganar, jinjina kai yay ya d'an kalli gefe alamar tunani kafin ya juyo yace mata to taji wani alama, ta d'an bud'a ido tace alamar mi, wani kallo yay mata da sauri ta maida fuskarta gefe, ce mata yay ta bashi amsa ba tare data kalle shi ba a shagwabe tace ita ya za'ai ta gane,
"But, did you feel anything last time?" Yay tambayar ya kafeta da ido, d'an jimm tay sai kuma ta yarfa hannu cike da kunya tace itafa bata fahimci komai ba lokacin, yace "Ok I forgot, u were in severe pain lokacin ba zaki fahimta ba" ita dai shiru tayi taga ya mik'e, Hijab d'in jikinta ya cire da kan shi ya kaita wardrobe tana ta kallon bayan shi, dawowa yayi ya duk'a a gabanta yasa hannu ya duk'o da kanta saman chest din shi ya kai hannu ya cire mata necklace d'inta bayan ya dagota ya had'a da earrings d'in gaba d'aya jewellery d'in ya cire ya kai saman dressing mirror, saida yaje ya sa ma kopar Bedroom d'in key sannan ya dawo wurinta gaba d'aya ya ciccibo ta yana fad'in Let them try their luck now.........
*ASM 076*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Gab da kiran sallar Magrib Haisam tsaye a gaban mirror ya gama shiryawa cikin jallabiya, bai dad'e da ya fito daga wanka ba bayan ya tashi bacci, gado ya nufa ya hau ya matsa kusa da Fatuu dake lullu6e da duvet tana ta shan bacci, hannu ya kai ya shafi fuskarta tare da kiran sunanta, ganin tak'i tashi yasa shi d'an bubbuga fuskar a hankali yadda bazata ji zafi ba, motsi ta fara yi kafin ta fara bud'e idanun tana yi tana lumshe su har ta bud'e su gaba d'aya sun d'an yi ja, bin juna sukai da kallo Haisam na d'an murmushi yace "My Lazy Wife" jin haka yasa ta tura mashi baki a shagwabe tace itace lazy d'in ya d'aga mata gira alamar eh, k'ok'arin rufe fuskarta da duvet ta shiga yi ta d'an d'aure ta ita ala dole tayi fushi, da sauri ya ruk'e Duvet d'in yace mata wasa yake mata ita ba lazy bace shi shaida ne, ganin irin kallon da yake mata yasa ta d'an juyar da fuskar ta tana yar dariya, ce mata yay ta tashi taje tayi wanka lokacin salla ya yi ta d'aga mashi kai, hannu ya kai zai d'ago da ita da sauri ta k'ank'ame duvet d'in tace yaje zata tashi yanzu, murmushi kawai yay ya juya ya saukko daga kan gadon, tanata kallon bayan shi har ya bud'e k'opa ya fita, lumshe ido tay tana ta sakin k'ayataccen murmushi da alama itama ta zaucen, daga baya ta saukko ta nufi toilet.
Bayan ta gama sallar Magrib mik'ewa tay ta d'aukko wayarta ta dawo kan prayer mat d'in ta zauna ta shiga kiran Fauzy, tana fara ringing ta d'auka suka gaisa tace mata ya School Fauzyn tace ta manta Weekend ne tana gida ai, d'an shiru Fatun tayi jin haka yasa Fauzy tambayar ta lafiya, tace "kin san Fauzy Ya Haisam fa ya dawo" da alamun mamaki tace mata da gaske Fatun tace mata "Eh, kuma harda Aunty Fanan ma, ashe wannan sak'on da kika tura sun gani kuma lokacin daya shiga ma ita ta fara gani wayar na a hannunta" wani uban salati Fauzy ta buga har saida ta kusa sa Fatuu fashewa da dariya don a matuk'ar razane ta yi shi, a rud'e ta shiga tambayar ta yanzu ya akai, mi ya faru, da alamun damuwa Fatun tace mata bata yarda ba rigima tasa wai sai an sake ta shine suka taho, wani salatin Fauzy ta k'ara saki, a iya muryarta zaka shaida ba K'aramin tashi hankalinta yay ba, a kid'ime tace ma Fatun to shi ya Haisam d'in miya ce, don kada taci gaba da tada mata da hankali tasan hakan bashi da kyau yasa ta saki dariya tace "sorry k'awata ina tsokanar ki ne amman da gaske ya dawo kuma taren suka zo sannan da gaske ita ta fara ganin sak'on" da sauri Fauzy tace "to yanzu miya faru don Allah??" Fatuu na murmushi tace mata Alkhairi, nan ta kwashe yadda komai ya faru harda bayyana mata da ya Haisam yayi yana son ta shima, wata uwar k'arar murna Fauzy ta saki Fatuu nata dariya tana jiyo ta tana k'wala ma Aunty Mareeya kira tana fad'in the long expected day has come, d'akin Aunty Mareeyar ta nufa dama tare suke suna kallo a parlor ta tashi taje ta dawo, a daidai bakin k'opar bedroom d'in nata sukai kacibus don ta jiyo k'wala mata kiran da take, cike da farinciki ta hau bata labarin abunda ya faru tun kafin ta k'arasa ta mik'a hannu ta amshi wayar dama duk Fatun na jin su, tana amsa cike da Farinciki harta kasa rufe baki ta kira sunan Fatun itama tanata murmushi ta amsa mata kafin ta gaishe da ita, Cike da tsantsar farinciki tace "ashe wai haka abu ya kasance, shima bawan Allah ashe ashe yana ta gurzuwa" yar dariya Fatun tay tace mata eh,
"Kai jama'a! Wannan cutar kai har ina kana son abu kuma abun nan ya zama mallakin ka Saboda tsabar cutar miskilanci ka tauye ma kan ka hakki" cike da jin kunya Fatun ta fad'i mata dalilin shi na yana son sai dangin shi sun sani, cikin washe baki tace "duk da yana da dalili amman ai da sai ya maki bayani ko yanzu da yasa zuciyar ki ta buga fa d'an bantan uba da yafi kowa shiga hali kuwa k'ilan ma tashi itama ta buga don na lura irin soyayyar laila da majnun kuke ma juna an sha yan ciwoce ciwoce" dariya Fatuun take ta yi Aunty Mareeyar ta shiga taya ta murna ta kuma yaba ma Fanan tace gaskiya tayi namijin k'ok'arin da ba kowace mace zata iya ba don ita kanta Maganar gaskiya bazata iya ba, daga baya kuma tace to kuma irin haka in har mutum ya fito ya bayyana maka in baka amince ba kai kanka ba samun kwanciyar hankali zaka yi ba, k'arshe kuma tace Allah ma kada ya kawo wacce zata siye mata zuciyar miji haka Fatuu dai sai dariya take, yar Nasiha ta d'an yi mata ta kuma ja hankalinta kan kula da miji dasu kwalliya tace sai sun had'u zata mata karatu sosae,