← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 197

Sashe 99

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

"How are you?"

Ta ce, "Alhamdulillah." Shiru ya yi, ta ce, "Dama tun jiya na kira in yi maka ya ka isa sai baka ɗauka ba, shine dama yanzu na sake kira." Ta faɗa tana ƴan kame-kame, calmly ya ce, "Ok, I'm sorry bana ɗaukan bakon no, na isa lafiya. Thank you." Shiru ta yi tana ci gaba da yin ɗan murmushi tare da ɗan wasa da yatsun hannunta wanda ba da shi ta riƙe wayar ba, "Any problem?" Ta ji ya tambaya, da sauri ta girgiza kai ta ce, "A'a dama shike nan." Tambayar ta ya yi layin ta ne wannan don wayar da ya bata babu layi, ta amsa mashi da a'a ɗayan na innarsu ne ta bata take amfani da shi, ya ce ok zai iya saving nashi ta ce eh da shi zata rinƙa amfani, bayan ya amsa mata da ok ya ce mata za su yi magana ya gaji ne sosai don har ma ya fara yin bacci, da sauri ta ce mashi to tare da yi masa sai da safe, bin wayar ta yi da kallo bayan ta cire ta daga kunnanta, haka nan take jin wani nishaɗi wayar da ta yi da shi don ita komai da ke faruwa tsakanin su ɗaukar shi take a matsayin alfarma yake mata sanin ya fi ƙarfin hakan da ita.
Chapter 99 · 0% Book details