← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 197

Sashe 86

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Salma ta isa gida, ɗakin su Sagir da ke a cikin zaure ta nufa jin sautin waƙa na tashi, daga bakin kofa ta yi sallama ba a amsa ba, sai da ta ƙara yi sannan cikin ɗaga murya Sagir ya ce, "Waye?" Ta bashi amsa da ita ce, tasowa ya yi ya leƙo yana ganinta ya fara dariya cike da zolaya ya ce, "Budurwar Deen Jr...ya har kin yi nasarar sa shi ya kware makin?" Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba, tana niyyar juyawa ya ce mata miye a ledan ta ce mashi ina ruwan shi, hannu ya kawo zai warci ledar ta yi saurin shigewa cikin gida da ɗan gudu, innarsu da ke zaune a cikin baranda har lokacin ta ɗago tana kallon ta, ganin ta shigo da guda ta tambayi lafiya, tana ƴar dariya ta ce ba wancan Sagir ɗin bane, wurin innar tasu ta nufa ko zama bata yi ba sai ga Sagir ɗin ya biyo bayanta yana faɗin bata isa ba sai ya ga ko minene aka bata a cikin ledar, da sauri ta miƙa ma innar tasu ledan tana dariya ta ce idan ya isa ya kar6a a wurin innar tasu, riƙe ledar innarsu ta yi tana kallon Sagir da murmushi ta ce ina ruwansa da ko minene a ciki tun da ba shi aka bamawa ba, Sagir ya ce, "Innarmu ko ba ni aka ba ba, tun da gidanmu aka kawo ai dole in gani." Miƙa ma Salma ledar ta yi ta ce ta amshi abun ta, tana ta murmushi ta ce ma innar tasu ta buɗe ta gani, buɗewa ta yi ta ciro kwalin da ke ciki, bin hoton wayar da ke a jiki ta yi da kallo, da sauri Sagir ya miƙo hannu ya ce ya gani, jujjuya kwalin wayar ƙirar samsung ya shiga yi tare da ɗan waro ido, kallon Salma ya yi ya ce, "Wayan waye?" Tana murmushi ta ce tata ce, "Kina nufin Deen ɗin ya baki?" Ta ɗaga masa kai alamar eh, "Ke! Kin san kuwa wannan ba ƙaraman waya bace, akan mi zai baki wannan babbar wayan?" Dariya maganar tasa ta ba Salma, ta ɗage masa gira ta ce ba ta faɗa masa son ta yake ba ya ƙi yarda, wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce shi fa ba zai ta6a yarda ba, ta ce to shike nan, kallon innarsu ya yi ya ce, "Innarmu kin ji wai shi ya bata, kuma kin san mi wannan wayar wllh ta kusa miliyan ko bata ida ba kaɗan ke babu." Daga innar tasu har Salma duk suka zaro idanu jin abun da ya ce, da sauri innarsu ta maimaita abun da ya ce ya tabbatar mata da hakan, kallon Salma ta yi ta ce, "Ya akai ya baki wannan wayan?" Da ɗan ruɗewa ta ce, "Ni dai kawai cewa ya yi gashi nan da ita zamu rinƙa magana kan aikin da ya bani don kada a takura ma Sagir." Mamaki ne duk ya bayyana akan fuskokinsu Sagir na dariya ya ce, "Shi bai san ni son ya rinƙa kiran wayan tawa nike ba." Ita dai innarsu ta yi zuru da alama ta rasa abun cewa jin kuɗin wayar da aka faɗa, "Kuma ya ce wai dubu hamsin zai rinƙa biyana duk wata kuɗin aikin." Duk suka ƙara waro idanu suna kallonta, "Wane aikin ne za a biya ki dubu hamsin?" Sagir ya tambaya da mamaki, ta ce mashi wanda ya ce zata rinƙa mashi, dariya ya yi ya ce, "Lalle Deen bai ɗauki kuɗi wani abu ba, yanzu har wani aiki ne wannan da zai rinƙa baki har 50k! Kawai saka ido bama da ke za a rinƙa dafa abincin ba, sai in kin ji wani na cikin matsala sosai ki sanar masa, shike nan aikin amman zai rinƙa biyan ki kuɗi har haka" Innarsu ta ce, "Amman Salma wannan kuɗin ai sun yi yawa a wannan aikin, ko dai gaba ɗaya har da na dahuwar yake nufi?" Ta ɗan girgiza mata kai ta ce, "Ai wannan ba cewa ya yi hajiya zata rinƙa badawa ba har da kayan abincin da za a rinƙa amfani." Shiru innarsu ta yi da alama abun ya fi ƙarfinta, tambayar Salmar ta yi ko ita ce ta ce ya rinƙa bata hakan, da sauri ta ce mata a'a wllh nan ta faɗi mata duk yadda suka yi da shi, wani sabon mamakin ne ya bayyana kan fuskar innarsu jin wai da dubu ɗari zai rinƙa bata, Sagir ya ce, "Ba fa ma wani abun mamaki bane ko dubu ɗarin ya rinƙa bata, wannan da kuke gani ba ƙananun kuɗi yake samu ba, na gaya maku duk sati miliyoyin kuɗaɗe ake biyan shi ban da wanda yake samu a wasu harkokin, ke kawai kakar ki ta yanke saƙa kin zama babbar yarinya, dubu hamsin duk wata ba wani nauyi a kan ki, lalle nan gaba kaɗan ba lalle ma ki rinƙa ganin girman mu ba, dama yanzun ma ya aka cika." Ita dai Salma kallon shi take kawai tana dariya, innarsu da ta yi jigum ta ɗan yi murmushi ta ce ai ya san ba haka take ba kuɗi ba za su canza ta ba, Sagir da ke dariya ya ce, "Pls ki bar man ita mu yi musanya in baki tawa don na san ke ƴar ƙauye ce ba lalle ki iya amfani ma da ita ba." Ƴar hararsa ta yi ta ce a cin zalinta da yake zata bashi, ita dai innarsu murmushi kawai take amman a can ƙasan ranta kokonton yakamata a amshi wayan take. A ranar ma basu yi niyyar yin awara ba, amman saboda tafiyar da Deen zai yi Salma ta roƙi innarsu a yi, bayan sallar magrib babansu ya dawo har da Auwalu, suma sun jinjina wayar da aka ba Salma da kuma albashin da aka ce za a rinƙa bata, ita dai innarsu ta nuna a mayar masa da wayar a ce ya canza mata wadda bata kai wannan ba, shima baban ya goyi bayan hakan, amman Auwalu da Sagir suka nuna basu goyi bayan hakan ba tare da nuna ma iyayen nasu shi fa a wurin shi wannan ba wani abu bane, da yawa ma haka nan yake masu alkhairin da ya fi wannan ita kuma aiki ne zata mashi, ƙarshe iyayen nasu suka amince tare da yin addu'a da kuma fatan alkhairi, har da nasiha baban nasu ya yi ma Salma kan ta zamo mai gaskiya da amana a aikin kuma ta kula da kanta ta guji aikata duk wani abu da ta san ba daidai bane, ka da ta bari zuciya ruɗe ta kan duk abun da ba daidai ba, daga ƙarshe ya haɗa su duka ya yi masu nasiha tare da basu misali da wannan alkhairin da ya samu Salma yana da nasaba da taimakon da take yi, ya ja hankalinsu da su zamo masu zuciyar taimako, itama innarsu ta yi mata yar nasiha, ƴan'uwanta duk suka yi mata addu'a da fatan alkhairi. Bayan sallar issha ta tafi kai ma Deen awaran, yau ma tana shiga gate ta hango shi zaune da mutane za su kai biyar, ɗauke kai ta yi ta nufi hanyar shiga cikin gida, tana cikin tafiya ta ji muryar Deen ya kira sunanta, dakatawa ta yi ta juya tana kallon in da suke, ya yi mata alamar ta je, tunkarar su ta yi ta sauke kanta ƙasa, daga ɗan gefen su ta tsaya ta ɗago ta gaishe su duka, lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi sakamakon haɗa ido da ta yi da Fahad wanda shi kaɗai ne bai amsa gaisuwar da ta yi ba, sauran mutanen guda ukku wanda duk abokan su ne suma duk hutu ya zauna masu sai ƙamshi ke tashi wurin, duk suka amsa mata gaisuwarta, Deen ya ce mata hajiya bata jin daɗi ta sha magani ta kwanta yana tunanin yanzu tana bacci, a hankali ta ce to ta ɗan yi shiru duk ta kama kanta, ganin idanun sauran mutanen na akanta idan ka cire Fahad dake kallon direction daban, ɗan matsawa ta yi daga inda Deen yake ta miƙa masa ledan ta ce gashi, kai ya ɗaga ya ce ta kai mashi ciki tare da yin godiya, juyawa ta yi ta wuce cikin gidan ƙafafunta har ɗan harɗewa suke, bada jimawa ba sai ga ta ta fito ko kallom inda suke bata yi ba ta nufi gate, "Deen wannan fa?" Ɗaya daga cikin abokan nasu ya tambaya bayan Salma ta fita daga gate, ya bashi amsa da a makwabta take, "Amman dai she is beautiful gaskiya, ban yi tunanin a area irin wannan ana samun beb mai kyau haka ba." Sauran abokan biyu ma duk suka yaba da kyawun Salma, ɗaya cikin su ya ce da gani kuma tana da natsuwa da wayewa, na farko da ya fara magana ya ce shi ya ji ma ta yi masa anya ba zai neme ta ba, sai lokacin Fahad ya saka baki ya ce mashi kar ya fara yarinyar bata da kunya, kallon Fahad ya yi ya ce, "Da gaske?" Kafin Fahad ya bashi amsa Deen na ɗan murmushi ya ce mashi ya ɗan samu misunderstanding da ita amman yarinyar tana da hali mai kyau ba yadda Fahad ke tunani ba, Fahad ya ce ai halin mutum da ya bayyana da shi ake shaidar shi, Deen bai sake cewa komai ba haka shima abokin nasu don ya fahimci kamar Fahad bai yin yarinyar. Bayan komawar Salma gida aka kira Aunty Kubra aka sanar mata game da waya da aikin da Deen ya bata, sosai ta yi farin ciki tana faɗin ita dama ta san ta yi sa'ar ɗiya akwai alkhairi tattare da rayuwarta wasu nasarorin ma na zuwa in sha Allah, da innarsu Salma ta sanar mata game da diramar da Salma ta yi da Sagir har da alwashin da ya sha, sai da aunty Kubra ta sa aka ba Sagir waya ta ce, "Sagir raina ɗiyar tawa ka yi da kake tunanin ba zai iya son ta ba? Kai ma ka san wllh Salma ba daga baya ba, kuma shi so ba ruwan shi tsaf sai ka ga Salma ta siye zuciyarsa cikin sauƙi." Yana dariya
Chapter 86 · 0% Book details