Sashe 95
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce, ɗauka ya yi ya kai kunne tare da yin sallama, ta amsa masa kafin ta yi masa ya isa lafiya, ya ce Alhamdulillah, "Ina ka sauka ne? Yanzu muka yi waya da Ammi ta ce mani sun ga ka isa garin amman ba can ka je ba." Shiru ya ɗan yi kafin ya bata amsa da yana a hotel, ta ce, "To miye na kama hotel room ba sai ka sauka a can ba tun da dai akwai wadataccen wuri." Ya ce mata football officials na nan ne suka kama masa, "Ok, yanzu sai yaushe zaka je can don sun ƙagara su ganka kada su ga kaman kana ta ja masu rai tun da suna ganin kana zuwa wurare." Amsa ya bata da idan aka yi sallar azahar zai je, ta ce to amman a can zai kwana ko, ya bata amsa da a'a don za su fara tournament da aka gayyace shi kuma tun yamma za su fara har zuwa dare, "Ka ce dama dai zuwa Kanon ma ba don su ka yi ba ke nan." Ya ce, "No, na zo gaba ɗaya ne." Shiru ta ɗan yi tana ƙoƙarin dannar zuciyarta kada ta cika yi masa ƙorafi kamar yadda ta tsara, ta ce, "To ka dai daure pls ka je kuma ka basu lokaci sosai ka ji buƙatun su ka biya masu." Ya amsa mata da in sha Allah, daga haka suka yi sallama, duba agogon wayarsa ya yi ya ga azahar ɗin ma ta kusa, yana son ya je gym na cikin hotel ɗin ya ɗan motsa jikin shi duk da a can Abuja kafin ya taso ya yi, saukowa ya yi daga saman gadon ya nufi toilet, bayan ɗan lokaci ya fito ya ɗauki abun da zai ɗauka dama kayan shan iska ne a jikinsa ya nufi kofa ya fita. Bayan sallar azahar ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya ɗaure sumarsa ta baya sai sakin ƙamshi yake, abincin rana aka kawo masa ya zauna cikin falo ya ci, bayan ya gama ya fito harabar hotel ɗin dama already ya sanar da driver da aka sa zai rinƙa tuƙa shi za su fita, har da jami'ai da za su bashi kariya aka haɗa shi tun da ya zo, bayan ya shiga cikin motar mai kyaun gaske ya sanar da driver anguwar da zai kai shi suka tafi motar da jami'an ke ciki ta bi su a baya, bayan sun iso layin da gidan yake, wani babban flat Deen ya nuna ma driver ɗin ya ce nan za su shiga, karya kan motar ya yi tare da yin horn sau biyu sannan wani mutumi da gani mai gadi ne ya leƙo, driver ya yi mashi bayanin wanda ya zo yana jin haka cikin rawar jiki ya shiga wage masu gate ɗin motar ta kutsa ciki tare da ta jami'an, bayan sun tsaya a cikin harabar wani a cikin jami'an ya fito ya buɗe ma Deen ƙofa, zuro ƙafarsa dake a cikin haɗaɗɗun takalma ya fara yi kafin ya ƙarasa fitowa, fuskarsa ta yi wani fresh sai sakin annuri take yi, mai gadi na ganinsa ya durƙushe ƙasa yana yi masa sannu da zuwa kai kawai Deen ke ɗaga masa, ya ce ma jami'an da driver sai ya fito suka amsa masa, mai gadin ya yi gaba da sauri ya nufi cikin gidan don ya je ya sanar masu isowar Deen, a daidai bakin main kofar shiga cikin gidan wani matashi ya fito kana ganin fuskarsa ka san ya girmi Deen don zai kai shekaru talatin da ɗoriya, fari ne sosai sai dai fuskarsa duk ta yi ƴan tabbuna tabbuna sannan la66ansa sun nuna alamar yana shaye-shaye, yana da tsawo da kuma ɗan kaurin jikin, akwai yanayin kammani da mom din su Deen akan fuskarsa, cikin washe baki ya tarbi Deen tare da miƙa masa hannu suka gaisa, da ƴar buɗaɗɗiyar muryarsa ya ce, "Ai tun ɗazun muke ta dakon zuwanka, na so zuwa tarbar ka airport wani uzuri ya sa na makara ban samu zuwa lokacin da ka iso ba." Ɗan murmushi ne akan fuskar Deen yayin da yake sauraron uncle ɗin nasa wato Bashir, jagora ya yi masa suka shiga cikin gidan wanda kana gani ka san akwai ƙarancin tsafta a tattare da shi, Ammi da abban su mom ɗin shi ne suka tarbe shi cike da nuna farin ciki bayan sun ƙarasa cikin falon, kujerun cikin falon manyan leathers ne amman duk sun fita hayyacin su da datti, haka dakakken carpet ɗin da ke a shimfiɗe shima dai duk ya yi datti, bangon falon kuwa da ya sha wallpaper itama duk tayi dabbare dabbaren dauɗa da su jirwaye wani wurin ma ta babbako daga jikin bangon, haka nan dai Deen ya zauna asaman ɗaya daga cikin kujerun, cikin natsuwa da ladabi ya gaishe da kakannin nasa suka amsa masa cikin washe baki suna ƙara masa sannu da zuwa, "Ai mun yi zaton nan zaka fara sauka tun bayan da Jameela ta sanar da mu tahowarka muka shirya ma tarbar ka, amman sai Bash ke sanar da mu wai a hotel ka sauka." Ammi ce ta yi maganar, ya ce mata eh can aka sauke shi, ta gyaɗa kai, Bash da ke ta washe baki yana ɗaukar Deen bidiyo a kaikaice don ya yaɗa, dama ba ƙaramin tutiya yake ba da kasancewar matsayin Deen a wurinsa, "Deeni ya can ƙasar taku, ai muna ganin irin kokarin da kake yi wllh..." Abban su mom ɗin sa ya faɗa yana washe baki da haƙoransa tuni sun gama fita hayyacin su da dattin taba da goro, amsa mashi ya yi da Alhamdulillah, ya ce "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara taimako ya sa kafi haka." Deen ya amsa da Amin, fitowa Ammi ta yi ɗauke da tray a sama an ɗaura lemun kwali da glass cup sai robar ruwa, a saman center table da duk glass ɗin sama ya tsattsage ta ɗaura ta maido shi gaban Deen tana faɗin ga lemu ya sha kafin a kawo abinci ya yi mata godiya, "Wai ina Aseey ba na ga bata je makaranta ba?" Bash ya tambaya yana kallon Ammi ta ce, "Eh, tun ɗazu take ta zaman jiran zuwan Deen, daga baya da ta ji ba a nan zai sauka ba shine ta ɗan fita na san ba da daɗewa ba zaka ganta, koma bara na kira ta na sanar da ita ya zo." Ta ƙarasa tana laluban wayarta a gefe, "Deen ka sha lemun mana, ko in zo in zuba maka ne, ka san fa kai babba ne." Bash ne ya yi maganar yana washe baki, ɗan murmushi Deen ya yi kawai ya ɗauki lemun gudun ya ce ba zai sha ba hakan ya zama wani issue, in da so samu ne ma ya sha a cikin kwalin ba sai ya yi amfani da cup ɗin ba don shi yadda ya ga gidan har ɗan kyankyami ya kama shi, a can ƙasan ransa kuwa mamaki yake yadda akai gidan ya kasance haka wanda ya san ba a jima ba mom ɗin sa ta amshi kuɗi masu yawa cewa su Ammin za su yi gyaran gida, sai dai bai ga alamun an yi wani gyara ba a gidan, "Salaamm.." Muryar mace ta furta, da sauri ta ƙaraso cikin falon tana washe baki idonta akan Deen, Aseeya ce wadda a shekaru ta kusa talatin, itama tubarkallah jajir take tana da kyau ba laifi sai dai sam bata kai kyawun mom ɗin su Deen ba, sanye take da wata straight gown da ta yi matuƙar kama jikinta, kai kace idan ta yi kwakkwaran nishi rigan zata iya yagewa, kanta ta tsigara ɗaurin kallabi da ya bayyanar da yalwatacciyar baƙar sumarta da ke fake a baya, daga gaban rigan kusan rabin ƙirjinta a waje yake fatar wurin ta fito fari fat da ita, nufo inda Deen ya ke ta yi tana ci gaba da washe baki ta wurga yar jakar da take rike da a wata kujera, ta zame ɗan ziririn gyalen da ke rataye a kan kafaɗarta guda, zama ta yi a kujerar da ke kusa da ta Deen cike da zumuɗi ta ce, "Welcome ɗana, ai tun ɗazun na yi ta zaman jiran ka sai baka zo ba." Dan kallon fuskarta ya yi ba tare da ya yarda idanunsa sun sake kallon jikinta ba, murmushi ya yi mata ya ce, "Thank you, ya karatu?" Ta amsa masa da Alhamdulillah ta ce ai yau saboda zuwan sa ma ta ƙi zuwa makaranta tana son ganin sa don ya daɗe bai zo ba sun yi missing nasa." Shi dai ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, sam bai yi mamakin ganin irin dressing ɗin jikinta ba sanin irin halin sakaci da rashin kula na iyayen su, "Aseey ki shirya ma ɗan naki abinci." Ta amsa ma Ammi da to tare da miƙewa da sauri, Deen kamar ya ce a bar shi amman ya san sai sun yi tsegumi idan ya ƙi cin abincin, dawowa Aseey ta yi ɗauke da wani babban tray an ɗauro warmers babba da ƙaramarta sai plates da cukulla, a saman center teble ɗin ta ɗaura da yake yana da faɗi, serving nashi abincin ta fara yi wanda farar shinkafa ce da miya ta sha naman kaza sai coleslaw, "Deeni ga abinci nan, an so ma a yi maka fin haka to mai aikin tamu ce ta je gida wai mamanta bata lafiya, nima kuma ba isassar lafiyan ce da ni ba, wannan ma ɗin duk kusan Aseeya ce ta yi." Ammi ta faɗa, godiya ya yi mata tare da addu'ar Allah Ya bata lafiya, sai da Aseey ta ƙara masa magana game da cin abincin ganin ya ƙi fara ci, sannan ya kai hannu ya ɗauki spoon ya fara ci.....