Sashe 172
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nutse Salma ta fito haraban gidan, lokaci guda bugun da ƙirjinta ke yi ya ƙaru, sosai ta tsorata da mutanen da ke a gefe da gefen motar, ganin irin suffar su da shigar da suka yi, sai dai kuma ta gane bodyguards ne don a hotunan Deen na dinner wasu akwai su a gefen shi, a ɗarare ta ƙarasa wurin motan, mutumin 6angaren da ta ke ya ɗan sunkuya mata kai alamar gaisuwa kafin ya kai hannu ya buɗe mata ƙofar back seat, sai da Salma ta haɗiyi wani yawu kafin ta fara ƙoƙarin shiga, bayan ta shiga aka rufe motar, tana shiga idanunta suka sauka akan Deen da ke hakimce ɗayan gefen ya ɗan kwantar da jikinsa yana latsa waya, yana sanye da ƙananun kaya da suka matuƙar amsar jikinsa, kansa ya faka sumarsa ƙasa, ga wani irin ƙamshi mai narkar da zuciya da yake saki, gaba ɗaya cikin motan ya karaɗe da ƙamshin haɗe da sanyin Ac masu tsuma zuciya, sauke idonta ta yi bugun zuciyarta ya ƙara tsananta sakamakon ganin Deen, a hankali ta ɗago daidai ya janye idonsa daga kan wayan da yake latsawa suka haɗa ido, motsa baki ta shiga yi kaman mai tattaro abun da zata faɗa, da kyar ta ce, "Ya Deen... sannu da zuwa, ina yini." Yay nod kansa fuskarsa a sake yana ta kallon ta don ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, kasa jure ma kallon shi ta yi ta maida kanta kasa, sosai ta ga ya ƙara yin wani irin kyau fiye da wancan zuwan da ya yi, Basma ce ta faɗo mata a rai, sai daga baya ta gane ita ce wadda ta ta6a ganin hoton ta a wayarsa har ya ce mata cousin ɗinsa ce kuma a gidan su yake zaune, idan har da gaske ita fiancee ɗin sa ce ta san mawuyacin abu ne bai aure ta ba, to ita anya kuwa Deen zai aure ta, don koda shi yana son ta dangin shi za su iya ƙin amincewa da ita saboda Basma, gashi ganin shi da ta yi yanzu wani irin sabon son shi ta ji ya mamaye mata zuciya, "Salmerh." Ya kira sunanta a hankali, ta ɗago ido ta kalle shi tana ƙoƙarin danne damuwar da ke a ranta, a hankali ta amsa, ya yi shiru yana kallonta can ya ce, "What's wrong, ko baki farin cikin zuwa na ba?" Da sauri ta girgiza masa kai tana ɗan murmushi ta ce, "A'a...ya Deen na yi farin ciki." Shiru ya yi yana ta kallonta kaman mai nazarin abu, "Mi yake damun ki ne?" Da sauri ta girgiza masa kai tana sauke idonta, daga yanayin ta ya so ya fahimci abu na damunta, saboda a ɗan sabawar da ya yi da ita wanccan karon a Funtua ya fahimci tana da ɗan yawan fara'a, in dai kuna magana za tai ta murmushi, yanzu kuma da ya kamata ya ga hakan koma fin yadda take yi a baya sai bai gani ba, dama tun lokacin da ya kira ta ya ce zai zo ya fahimci kaman tana cikin damuwa, calmly ya ce "Why kike boye mani abun da yake damun ki?" Dan kallon shi ta yi tana kikkafta idanu ta ɗan girgiza masa kai, duk yadda take son danne damuwarta zuciyarta ta ƙi bata goyon baya, in dai ba jin tsakanin shi da Basma da kuma matsayinta a wurin shi ta yi ba hankalinta ba zai kwanta ba, sigh ya yi ya ce, "I think zan koma ne idan ba zaki faɗi mani mi yake damun ki ba." Da sauri ta kalle shi tare da ɗan girgiza mashi kai cikin marairaicewa ta ce, "A'a ya Deen pls kada ka tafi." Gyara zama ya yi ya ce, "Ok, tell me mi yake faruwa?" Motsa baki ta shiga yi ta rasa ta yadda zata yi mashi magana, da ƙyar gabanta na faɗuwa da yar in ina ta ce, "D...dama kana da wadda zaka aura?" Tana yin maganar ta yi saurin sauke idonta ƙasa, Deen ya yi ta kallonta, sam bai yi tunanin wannan ne abun da yake damun ta ba, jin ya yi shiru ta ɗan ɗago kai ta kalle shi suka hada ido, janye idon shi ya yi ya koma yana kallon gaban shi, ya ce, "She is my cousin, akwai maganan aure tsakanin mu." Salma tai ta kallon shi yayin da bugun zuciyarta ya ƙara tsananta, zuciyarta ta shiga azalzalarta kan son sanin matsayinta a wurin shi, "Ni... ke nan ba aure na zaka yi ba..." tana yin maganar ta sauke idonta don ita kanta bata san lokacin da ta furta hakan ba, a hankali ya juyo fuskarsa ya kalle ta kaman ba zai ce komai, can ta ji ya ce, "Zan aure ta, ke ma haka..." Salma ta ɗaga ido tana kallon shi yayin da shima idanunsa ke akanta, "But ban san ko zaki iya aure na da wani matan ba." Salma ta ɗan yi shiru tana sauke idonta, ganin yana ta kallon ta alamar kamar amsarta yake jira, cikin yar rawan murya ta ce, "Zan aure ka...amman ita ban san ko zata amince ka aure ni ba." Ɗan murmushin gefe ta ga ya yi ya ce ba ita ce zata yanke masa haka ba, Jingina ya yi da seat yana kallonta, sam bai yi mamakin jin tsakanin shi da Basma ne damuwar ta ba, don ba ita kaɗai ba mata masu son shi duk sai da suka nuna mashi damuwar su game da hakan, har da wanda sukai mashi kuka jin cewa Basma fiencee ɗin shi ce. Sosai Salma ta ji sanyi a ranta duk da tana jin sauran zullumi don bata san ko family din shi za su yarda ya aure ta ba, ɗan juyawa ta yi ta kalle shi suka haɗa ido ta ɗan yi mashi murmushi, slowly ya ce mata damuwan ya tafi ke nan, da sauri ta kife fuskarta a jikinta alamar kunya, bayan ta ɗago ta sake kallon shi, ya yi ɗan murmushi ta ji ya ce, "Ko da wani damuwan?" Ta yi saurin girgiza masa kai, shiru ya ɗan yi kafin ya ce to ta bashi labari ya yi maganar yana maida idonsa kan waya, ɗan shiru ta yi tana tunanin wani labarin zata bashi, ta ce, "Na tura maka saƙo har biyu tun lokacin da kuka dawo world cup amman baka duba ba." Shiru ya yi yana daddana wayarsa, ta ji ya ce gashi ya ga ya duba saƙon farko na biyun bai ma gan shi ba sai yanzu, ɗago kai ya yi suka haɗa ido ya yi ƙasa da murya ya ce, "A yi hakuri idan na yi laifi." ta ɗan buɗa ido sai kuma ta yi murmushi tare da girgiza masa kai, daga yadda yake yin magana da ita zaka fahimci ba mai yawan magana bane, kuma da gani bai saba hirar soyayya ba, bayan ɗan shiru Salma na kallon shi da ɗan murmushi ta ce, "Kun sha dinner, ta yi kyau sosai." Idon shi akan waya ya ce, "Ke kuma kin sha kuka zaki rasa ni ko?" Ta ɗan buɗa ido sai kuma ta yi yar dariya, ya ɗago yana murmushi ya tambaye ta haka ne, sauke idon ta ta yi a sanyaye ta ce, "Na dai shiga damuwa sosai da na ga an ce fiancee ɗin ka ce ita...na yi tunanin ni ka fasa...so na." A hankali ta ɗago ta kalle shi jin ya yi shiru ta ga ita yake kallo, calmly ya ce mata ya so yai inviting nata dinner ɗin, sai ya yi tunani idan ta je zata zama uncomfortable saboda duk bata san su ba, tana ta kallon shi yana maganar, bayan ya gama ta ce, "Ni na yi zaton ma ko ka manta da ni ne, da na ga an ɗauki lokaci baka kira ni ba, har ka zo kuma ka tafi." Ya yi shiru yana kallonta, itama kallon nashi take tana yi tana sauke idonta, ƙasa da murya ta ji ya ce, "How can I forget someone who keeps appearing in my dreams...." Salma ta yi saurin kallon shi, janye idon ta ta yi don ta kasa jure ma kallon da yake mata, slowly ya tambayi shima tana yin mafarkin shi, ta ɗago ta kalle shi, lecture ɗin aunty Kubra ta shiga dawo mata a kai, cike da dakewa looking at him in the eyes ta ce, "You are in my dreams and in my heart always.." Ya yi shiru yana mata wani kallan kallo, duk yadda ta so ta jure ma kallon shi kasawa ta yi, ta ji kallon da yake mata na neman haifar mata da kasala hakan ya sa ta saurin sauke idonta, bayan ɗan shiru na wani lokaci ta ji ya ce, "Baki tambayi Fahad ba." Ita sham tama manta da wani Fahad sai yanzu da ya ambace shi, ta ɗan kalle shi ta yi murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba, ya sake ce mata ina Sageer, ta ce "Yana nan, yana Funtua shine ma yanzu ke kula da aikin da ka bani, shima kwanaki ya ce mani ko ya tura maka saƙo baka reply, amman komai ake buƙata yana ma hajiya magana." Ya ɗan jinjina kai, "Ke kin dawo nan ke nan, ba zaki koma Funtua ba?" ta ce, "Eh a nan zan yi karatu sai dai in rinƙa zuwa idan mun samu hutu." Ya ɗan yi shiru can ya je, "Ba zaki yi karatun a London ba?" Ta yi saurin kallon shi ba ta ce komai ba don bata fahimci inda maganar tashi ta dosa ba, "Ko you are not ready ki koma can?" Dan murmushi ta yi ta sauke idonta, a hankali ta ce, "Waye zai kai ni." Ya bata amsa da shi, ta kalle shi sai kuma ta yi saurin saka tafin hannunta ta rufe fuska don ta fahimci abun da yake nufi, Deen ya yi murmushi don kunyarta na burge shi sosai, ba kamar Basma ba da sam bata nuna masa kunya a abun da ya shafi soyayyar su, yanzu haka ma cikin takura masa ta ke koda yaushe kan ya yi ma dad ɗinta magana cewa ya shirya auren ta, saboda har yanzu Maleek ya ƙi amincewa da maganar auren su biyun, a tunaninta idan shi