Sashe 94
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune dad ya yi shi kaɗai a falon ya ɗage kan sa sama, ya gaji da halin Jameela gashi ya rasa ta yadda zai yi maganinta, yanzu ya san wannan fushin da ta yi haka zata yi ta gasa masa aya a hannu, sanin shi zai cutu ya sa shi fara tunanin ta hanyar da zai bi ya shawo kan ta cikin lalama har ta amince da buƙatar Deen, bayan wani ɗan lokaci ya fara sakin ɗan murmushi da alama ya samu mafita, miƙewa ya yi ya nufi hanyar 6angarenta. Deen zaune a bakin gadonsa yana riƙe da ɗayar wayarsa da ya bari a nan ɗaki lokacin da ya zo yin alwala, duk missed calls da ya iske yana da saving contacts ɗin banda baƙuwar lamba ɗaya da ya gani, a ƙa'ida baya ɗaga baƙon kira idan ba ya san da za a kira sa ba hakan ya sa bai bi kiran ba. Dad na shiga cikin ɗakin mom ɗin su Deen ya hango ta zaune a gaban dressing mirror tana mulke jikinta da mai, da alama wanka ta yi ta saka yar yaloluwar doguwar rigar bacci mai siraran hannuwa, sumarta a warware ta yi mata rumfa har tsakiyar bayanta, jin motsi ya sa ta ɗan waigawa don gashinta bai bari ta ga bayanta, tana yin arba da dad ta wani tamke fuska tare da juyowa tana ci gaba da abun da take yi, tsaye ya yi daga ɗan nesa da ita yana kallonta, bayan ta gama shafa man ta shafa roll on sannan ta shiga fesa turarurruka kamar da gayya, bayan ta shafa ma gashinta wasu mayuka ta feshe shi da hair spray kafin ta tattare shi ta tufke, ɗaukar wayarta dake ajiye a gefen madubin ta yi ta juya ta nufi gado tana latsa ta, yadda take tafiya jikinta na juyi zaka san da gayya take yin hakan, saman gadon ta haye ta tada kanta da pillow tana ci gaba da lallatsa wayarta, nannauyar ajiyar zuciya dad da ke a tsaye kaman an dasa shi ya sauke still idanunsa na akanta, "Jameela..." Calmly ya kira sunanta, ko kallo bai ishe ta ba tana ci gaba da ta6a wayar, ɗan jim ya yi kafin jiki a sanyaye ya zagaya ta gefen inda take ya zauna a bakin gadon, "Jameela baki gan ni bane?" Sai lokacin ta yi mashi wani matsiyacin kallo a ɗan harzuƙe ta ce, "Idan na ganka goya ka kake son na yi?" Shiru ya yi kawai yana kallonta ta ɗauke idanunta, a nutse ya fara magana, "Yanzu a cikin maganganun da na yi miye abun bacin rai Jameela?" Kamar tana jira ta yunƙura ta tashi zaune a masiface ta ce, "Taya zaka ga abun 6acin rai a ciki Ibraheem!" Har saida fuskarsa ta kasa 6oye mamaki jin yadda ta kira sunansa gatsau, duk da ba wannan ne karo na farko ba, idan ya yi mata abu ranta ya baci sosai kiran sunansa take kai tsaye, a tausashe ya ce, "Ni ban yi maganar da na yi ba don na 6ata maki rai, baki fahimce bane, ina ƙoƙarin nusar dake irin yadda wasu lokuttan kike wasu maganganun akan abun da ya shafi relatives ɗin yaran nan bai kamata ba, za su iya fahimtar kamar kina yin bangare ɗaya kawai which hakan ba zai masu daɗi ba ko kuma ya haifar da matsala a zumuncin su." Wani kallon ɗibar albarka take bin shi da shi har ya gama, tana yamutsa fuska ta ce, "Shine zaka zauna a gaban yara ka ci mani fuska, idan fahimtar da ni kake son yi tun da bani da fahimta a gaban su yakamata ka yi mani magana? Dama ai ba yanzu ka fara nuna mani iyakata ba akan dangin ka, shine shima Deen ɗin kake ƙoƙarin koya masa hakan, kuma abun da ba zai yiwu ba ke nan matuƙar ni ce na haife shi dole ne na yi iko da shi akan abun da bani so ko na hango zai iya cutar da shi, ba wanda ya isa ya hana ni! Ai ina da dalilin yin maganar da na yi, akan mi zai tare can ya yi ta masu bauta, wasu abubuwan ma da ya je ya yi gwamnati ce yakamata a ce ta yi amma bata yi ba, sai shi da bai san ciwon kan sa ba ya je yana 6arnatar da kuɗin da yake wahala kafin ya samu, da yake garin ka ne yake ma bauta naka za su amfana ai shi ya sa baka ganin hakan a ba daidai ba kake goya masa baya, ni kuma ba zan zauna in zuba ido ba wllh tun da ba su na haifa ma shi ba." Ta ƙarasa tana mai tabbatar da abun da ta faɗa, shiru dad ya yi kawai yana ta kallon ta, can ya ɗan girgiza kan shi, bayan ya sauke yar gajerar ajiyar zuciya cikin kwantar da murya ya fara magana, "Baki fahimce ni bane Jameela, bani da wata manufa wai ta koya ma Deen ko ya raina ki ya ƙi jin maganar ki akan abun da ya shafi dangina, a wuri na da naki dangin da nawa ba wani bambanci tun da ni da ke mun riga mun zama abu ɗaya, sannan koda kika ga ina goya masa baya akan duk abubuwan da yake yi a can saboda hakan abu ne mai kyau, kuma shi taimako ko da a wuri ɗaya mutum ke yi ba laifi bane in dai ana da buƙatar hakan kuma zai samu lada, sannan kuma da na yi wani dogon tunani ta wani 6angaren muma hakan amfanin kan mu ne Jameela." Wani kallon ban gane me kake nufi da hakan ba ta jefa masa, gyara zaman shi ya yi ya ci gaba da magana, "Ke kike ta ƙarfafa mani guiwa tun da daɗewa kan kina son na fito takarar kujerar gwamnan jahata, sai nike ganin wannan abubuwan da Deen ke yi tamkar sharar fage ne yake yi mana, yanzu baki ganin idan na fito takara waɗannan ayyukan alherin da yake yi a jahata za su yi matuƙar yin tasiri wurin kai ni ga yin nasara ehem?" Jim ta yi idonta a kansa ya ɗan jinjina mata kai alamar ta yi tunani, juyar da fuskarta ta yi zuwa ga duban wani direction daban da alama nazarin maganarsa take, wani murmushin nasara dad ya shiga saki a fakaice, dama ya san haɗamarta akan mulki shi ya sa tunanin shawo kanta ta wannan hanyar ya zo masa a rai ya san tabbas zai yi nasara a kanta, slowly ya kai hannu ya dafa cinyarta da rigar jikinta ta lafe a kai, juyowa ta yi ta kalle shi ya ɗan sakar mata murmushi ya ce, "Ke ya kika gani game da hakan?" Ɗan juya idanunta ta yi ba tare da ta ce komai ba, ɗan cije lebanta na ƙasa ta yi ta ce, "Amman ai da sai ka fahimtar da ni daga ni sai kai ba a gaban yara ba." Da sauri ya ce, "Ok na kar6i kuskure na, I'm sorry my queen ba za a ƙara irin haka ba." Wani kallo mai kaman harara ta wurga masa ya saki ƴar dariya, ƙoƙarin ƙarasa hayewa saman gadon ya fara ta yi masa wani kallo ta ce ina zai je, a ɗan marairaice ya ce to ba sun sasanta ba ta haƙura, tana yatsina ta ce suka yi da shi ta haƙura, ya ƙara marairaice mata, sai da ta mula sannan ta ce a haka zai hau mata gado ba tare da ya freshen up ba, ya ce mata duk zumuɗin gimbiyarsa ta haƙura ne, saukowa ya yi daga saman gadon yana faɗin bari ma kawai ya yi using toilet ɗin ta, ya nufi hanyar toilet ɗin a ransa yana faɗin, "Jameela zuma, ga daɗi ga harbi..." zuba ma wuri guda ido ta yi tana ƙara nazarin maganarsa da kyau, ya akai ita sam wannan tunanin bai zo mata a rai ba, tabbas kuwa ayyukan alkhairin da Deen ke yi ba ƙaramin taimaka masu zai yi ba idan dad ɗin nasu ya tsaya takarar gwamna, yanzu tamkar campaign ne yake masu, dole kam ta rinƙa kauda kai akan wasu abubuwan ko da ranta bai so, wani shu'umin murmushi ta shiga saki yayin da zuciyarta ke hasko mata ta zama first lady ɗin Katsina, gyara kwanciyarta ta yi ta ɗan tada kanta a ranta tana raya ba ma iya first lady ɗin Katsina ba, burinta ta zama har first lady ɗin Nigeria kuma sai ta yi duk yadda zata yi gurin ganin haƙarta ta cim ma ruwa. Tun Salma tana saka ran Deen zai biyo kiranta har dai ta fidda rai ganin an ɗauki lokaci, bayan ta kwanta tunani iri iri suka shiga zuwa mata a rai game da dalilin ƙin biyo kiran da bai yi ba, a ƙarshe ta bar ma ranta wataƙil wani uzurin ne ya hana sa kiran nata. Washe gari a hanyar su Deen ta dawowa daga sallar asuba dad ɗin sa ya sanar da shi ya kwantar da hankalinsa su ci gaba da shirin su na gina asibitin ya shawo masa kan mom ɗin su, sosai Deen ya ji hankalinsa ya kwanta don dama bai san ta ya zai fara sanar da su Fahad cewa ya fasa haɗin gwiwar ba dole za su zargi ƙin amince masa aka yi. Deen da kansa ya kai su Leemarh school a ranar ya yi masu bankwanar tafiya Kano da zai yi suka yi mashi Allah Ya tsare da fatan dawowa lafiya. Misalin ƙarfe sha ɗaya na safiyar ranar Deen ya sauka a Kano, kyakkyawar tarba ya samu daga manyan masu ruwa a harkar ƙwallon ƙafan jahar tare da manya da ƙananun ƴan'kwallo da kuma fans ɗin shi ciki har da jaruman fina-finai, an cika arrivals hall ɗin don welcoming ɗin sa, bayan gama gaishe gaishe da ɗauke ɗauken hotuna kai tsaye suka wuce da shi babban hotel ɗin da suka yi masa masauki don ya huta kafin lokacin da za su fara gasar da aka shirya wadda wasu kamfanoni a jahar suka ɗauki nauyi. Deen na kwance saman gado a ƙayataccen ɗakin da aka kama masa yana yin bacci, ringing ɗin wayar sa ne ya tashe shi, duba mai kiran ya yi ya ga mom ɗin sa