Sashe 127
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
....Da ƙyar Basma ta jawo kayanta ta fara sakawa, saukowa ta yi daga saman gadon har lokacin jikinta kerma yake sosai, tsaye ta yi ƙwalla na ci gaba da zubowa daga idanunta, tana son tabi bayan dad ɗinta sai dai tsoro da fargaba sun cika zuciyarta, ta ɗauki lokaci a tsaye tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, da ƙyar ta yi ƙarfin halin nufar ƙofa ta fita, a hankali take yin tafiya kamar mai yin sanɗa, kana ganinta ka san a matuƙar tsorace take, bugun da ƙirjinta ke yi yana ƙara tsananta yayin da take ta ƴan waige-waige, bakin bene ta iso ta tsaya tana kallo cikin ƙaton falon ƙasan bata ga kowa a ciki ba, ɗago idonta da ya yi sharkaf da ƙwalla ta yi ta kallo 6angaren dad ɗinta da ke a saman benen, jim ta yi tana ta kallon wurin, can ta fara tafiya a hankali ta nufi part ɗin, tana isa bakin ƙofar shiga ta tsaya sakamakon hango Maleek da ta yi ta cikin ƙofar wadda take ta glass, zaune yake a saman kujera ya sadda kansa ƙasa yayin da yasa duka hannuwansa ya tallabe kansa, ko takalman ƙafarsa bai iya ya cire ba, wasu sabbin hawaye ne suka fara zubo mata, ta yi takaicin yadda ta saka dad ɗinta mai matuƙar ƙaunarta a cikin damuwa haka, a karon farko a rayuwarta da ta ji tana tsoron kusantar mahaifin nata, summoning every ounce of courage she had ta shiga ciki, har ta kai tsakiyar falon bai ɗago ba da alama ma bai san ta shigo ba, can nesa da shi ta tsaya tare da duƙawa ƙasa, cikin rawan murya ta fara magana, "Dad, please I'm sorry… I swear it was a mistake, I was not thinking please forgive me..." Shiru bai ko motsa ba yana a yadda yake, ƙwalla ne suke ta malala daga idanuwanta, "Don Allah dad...na san na yi abu mara kyau, It was the devil's work...Dad please… i promise it will never happen again." Ta faɗa tare da haɗe hannuwanta pleadingly, Still ba alamar zai ɗago balle ya tanka mata, haka ta ci gaba da roƙonsa, bayan wani lokaci ta ga ya ɗago kan sa ya kalle ta, abun da ta gani a fuskarsa ya matuƙar ƙara tayar mata da hankali, dad ɗinta yau ke zubar da ƙwalla, wanda tun da take bata ta6a ganin hakan ba, ko lokacin da mahaifiyarsa ta rasu bata ga ya yi kuka ba duk da tarin damuwar da ya shiga a lokacin, yau ita ce ta saka dad ɗinta mai ƙaunarta kuka, subhanAllah!
"Basma...." Ya kira sunanta da yanayin tsoro da rashin yarda muryarsa na karyewa, kallon da yake mata shi kaɗai ya isa ya karya dukkan ƙarfin gwiwar ta, haɗe hannuwanta ta yi tana ci gaba da yin kuka tana bashi haƙuri tare da faɗin kuskure ne, "I can't believe what my eyes just saw...what have you done Basma?" Ya faɗa yana yi mata kallo mai cike da shakku, "Dad don Allah ka yafe ni… wallahi kuskure ne, ban san me nake yi ba. Ka yafe ni don Allah!†idanunsa jiƙe da hawaye ya furta, "Kuskure? Kina kiran wannan kuskure? Kin san abin da wannan yake nufi a addini? A al'ada? A cikin sunan iyalin nan?" shiru bata ce komai ba tana ta haɗe hannuwanta tana ci gaba da yin kuka, maida kallonsa ya yi gefe, idanuwansa har sun yi ja, cikin ɗan jinjina kai ya furta, "This kind of thing under my roof! After all the love and trust we gave you..." Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba muryarsa ta yi rauni sosai, magiya Basma ke ta ci gaba da yi masa kan ya yi haƙuri ya yafe mata tare da alƙawarin bazata sake aikata hakan ba, wayar sa dake yashe gefe ce ta fara ringing, sai da ya ga kiran James sannan ya tuna da ya barsa a waje za su koma office, saidai a halin da yake ciki bai jin zai iya komawa wurin aikin, ɗaukar wayar ya yi cikin ƙoƙarin daidaita muryarsa ya sanar da James cewa ya je kawai shi ba zai samu komawa office ɗin ba, shiru ya yi bayan ya gama wayan yana kallon gefe, akwai maganganun da yake son yi amman saboda ɗacin da yake ji a bakinsa ya kasa, a cikin ransa yake ta faman jinjina al'amarin wanda yake gani tamkar mafarki, tabbas ƙaddara bata kara, duk yadda ya kasance yana mai kula sosai kan tarbiyyar Basma hakan bai hana wannan mummunan ƙaddarar samun su ba, tunaninsa yadda akai ta koyi wannan mummunan ɗabi'ar, ko hakan yana da nasaba da wani sakaci nasu? A hankali ya kai idanunsa kan Basma dake ta shar6ar kuka jin furucin da take na roƙon kada ya sanar ma mom ɗinta, janye idanunsa ya yi a ransa yana mai tunanin idan Sapna ta ji wannan labarin ya san har matsala zata iya samu a zuciyarta idan ma bata samu attack ba,