← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 197

Sashe 100

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matasa ne guda ukku zaune a saman benci a gaban wani shago wanda rubutun da aka yi a sama ke nuna shagon sayar da provision ne, gaba ɗaya sun cika wurin da hargowa suna hirar gasar da aka yi yau da irin yadda Deen ya iya sarrafa ƙwallo, daga cikin shagon wani matashin saurayi ne jikinsa sanye da ƙananun kaya ya ɗan kwanto saman kantan gaban shagon yana saurarar su, daga yanayin da fuskarsa ta nuna zaka gane yana da interest kan hiran don har ɗan murmushi yake, a kallo ɗaya idan ka yi ma matashin zaka shaida kyakkyawa ne na gaske, launin fatarsa mai matuƙar kyaun gaske wanda ba kasafai aka cika samun mutane masu irinta ba, yana da dogon hanci da madaidaicin baki, idanuwansa na da ɗan girma masu haske da baƙar ƙwaya wuluk, yana da cikar gashin gira wanda zanenta ya fita raɗam da kwantaccen gashi, haka gashin saman kansa ma yana da cika gashi baki mai santsi ya kwanta luf, kana ganinsa zaka iya yanke cewa ba ɗan nan ƙasar bane don daga yanayin fatarsa da kyawun fuskarsa ya fi kama da irin mazan ethiopia, bayan ɗan lokaci samarin suka tashi ɗaya ya ce ma mutumin da ke cikin shagon ya bashi maganin sauro, ɗayan ma ya ce ya bashi indomie manya guda biyu da ƙwai biyu, bayan ya sallame su suka yi ma juna saida safe suka tafi, ɗayan da bai tafi ba ya ƙaraso cikin shagon yana kallon mai shagon ya ce, "Wai Mukhtar mi ya hana ka zuwa kallon gasar ne?" Ɗan murmushi Mukhtar ɗin ya yi ya shafi sumarsa cikin muryarsa mai tattare da natsuwa ya ce, "Ba komai Tasiu, haka nan na ƙi zuwa." Tasi'u ya ce, "Amman kana son ƙwallo balle wannan babbar gasa ce, uwa uba kuma har da ɗan'uwanka wanda duniya ta san da shi a harkar ƙwallo." Shiru Mukhtar ya yi yana kallon Tasi'u kawai, daga yanayin fuskarsa zaka fahimci ɗan yanayin damuwa da ya bayyana, Tasi'u da ya san miye damuwarsa ya ce, "Da nine kai zan je kuma sai na yi yadda na yi na samu yin magana da shi." Wani murmushi wanda ya fi kama da a kira na takaici Mukhtar ya yi ya ce, "In ce masa mi Tasi'u? Mutumin da bai damu da kai ba kamar ma bai san da Allah ya yi ka ba...." Tasi'u ya yi ɗan jim, shi fa a yadda yake ji da shine yake da alaƙa ta jini da Deen wllh duk yadda za ai sai ya samu ya yi magana da shi, amman da yake ya san halin Mukhar mutum ne mai kauda kai hakan ya sa bai ta6a tunanin ya nemi Deen ba tun da shi ma bai neme su ba, Tasiu ya ce, "Amman ni abun nan na ɗaure mani kai wllh, mutumin nan ana yabonsa da halin kirki, amman a ce bai ta6a tunanin ya neme ku ba matsayin ku na danginsa, duk irin alkhairin da ya ke ma mutane wasu ma can bare amman ku bai ta6a yi maku ba, abun nan da mamaki." Shiru Mukhtar ya yi can ya sauke ƴar ajiyar zuciya ya ce, "Wataƙila bai san da mu a matsayin danginsa bane." Tasiu ya yi masa wani kallo ya ce ta ya hakan zai yuwu da mahaifinsu da mahaifin mahaifiyarsa uwa ɗaya uba ɗaya, su fa matsayin cousin ɗin mahaifiyarsa ne amman a ce bai san da su ba a matsayin danginsa, shiru kawai Mukhtar ya yi amman shi ya san dalilin da ya sa ya faɗi hakan wanda abu ne mai sauƙi hakan ta kasance, jin bai ƙara cewa komai ba Tasiu ya ce don Allah gobe ya zo su je tun da ba a gama ba, Mukhtar ya ce masa zai duba yuwuwar hakan, bayan Tasiu ya siya biredi da madara suka yi sallama ya tafi, bayan tafiyarsa zuba ma wuri guda ido Mukhtar ya yi yana tunanin abun da ya faru can baya tsakanin shi da Ammin su mom wanda har ta yi masa iyaka da zuwa gidan su, ranar da abun ya faru ya je unguwar su gidan su wani abokinsa bayan sallar azahar, bayan ya gama ya biya don ya gaishe da ita kamar yadda duk bayan lokaci yake yi, duk da su sam basu yin zumunci da su hakan bai dame shi ba a wurinsa yana yin hakan ne don Allah, kuma halin ko in kulan da suke nuna masu bai dame sa ba, da sallama ya shiga falon Ammi na zaune tana cin abinci ta amsa masa babu yabo babu fallasa, bayan ya zauna kan kujera ya gaishe da ita, shiru ya yi Ammi ta tambayesa ƴan gidan su ya ce mata duk suna lafiya, "Ga shi ka zo abinci ya ƙare ba a san da zuwan ka ba." Ta faɗa tana mashi wani kallon rashin arziƙi, ya yi murmushi ya ce, "Ah ba komai dama zuwa na yi in gaishe ku." Ta ce, "To an gode." Daga haka ta ci gaba da cin abincinta, motsin shigowar da suka ji ya sa duk suka kai idanunsu kan kofar shigowa, Aseeya ce ta shigo cikin falon tana wata irin tafiya jikinta sanye da riga da skirt na lace da suka yi matuƙar matse jikinta, sosai kayan suka fito mata da shape din jikinta tamkar an zana ta, hannunta riƙe da ƴar jakarta da kallabinta, saman kanta wani ɗan yalolon gyale ne mahaɗin kayan sharara da shi hakan ya bayyanar da sumarta dake a baje, bin ta da ido Ammi ta yi har ta ƙaraso ta zauna a kujeran kusa da ita, Ammi ta ce, "Sai yanzu zamu gan ki? Daga zuwa wurin biki shiru tun jiya kin sa hankalin mu duk ya tashi, ga shi anata kiran wayarki tun tana shiga ba a ɗagawa har ta dawo a kashe." Kamar bazata tanka ta ba sai faman wani lumshe ido take, can kamar magana na mata wuya ta ce, "Ba a tashi dinner ɗin da wuri ba, shine kawai muka wuce gidan su amaryan muka kwana." Shiru Ammi ta yi tana kallon ta don ta so fahimtar kamar ƙarya take ba gidan su amaryar ta kwana ba, tun da idan can ta kwana miye na ƙin ɗaga waya kuma ba sai ta kira ta faɗa ba, ganin Mukhtar na a falon ya sa ta yi shiru bata ƙara ce mata komai ba, "Zaki ci abinci ne?" Ammi ta tambaya, ɗan girgiza mata kai ta yi ta ce a ƙoshe take, "Ba ki ga yayan ki Mukhtar ba." Ta wani ɗaga ido ta kalle shi suka haɗa ido, a daƙile ta ce masa sannu ya ɗaga mata kai kawai, wayarta ce ta fara yin ringing ta kai hannu ta buɗe jakarta ta fiddo, lokacin Ammi ta miƙe ta bar falon riƙe da plate ɗin data gama cin abinci, murmushi Aseey ta shiga saki tana amsa wayar, daga yanayin yadda take amsa wayar Mukhtar ya gane koma wanene suke magana ta waya da shi suka kasance duk in da ta kwana, ko nauyin Mukhtar ɗin bata ji ba yadda take yin wayar, sadda kai Mukhtar ya yi jikinsa ya yi sanyi sosai, duk da dama ya san halin da yaran gidan suke ciki amman jin irin maganganun da Aseeya ke yi a gabansa hankalinsa ya tashi sosai, lokaci guda wani 6angare na zuciyarsa ya fara saƙa masa wani abu yayin da ɗayan 6angaren ke gargaɗinsa kan hakan, tunawa ya yi da ita ɗin ƴar'uwarsa ce yana da hakkin da zai yi hakan, bayan ta gama yin wayar miƙewa ta yi ba tare da ta ɗauki gyalenta da ya zame daga kanta ba, iya jakarta kawai ta ɗauka zata nufi ciki, "Aseeya..." Mukhtar ya kira ta yana kallonta, dakatawa ta yi ta juyo tana kallon sa ba tare da ta ce komai ba, "Idan ba damuwa ina son yin magana da ke ne." Tsaye ta yi kamar bazata tanka masa ba, sai kuma ta matso daga gabansa ta ce tana ji, nuna mata kujerar gefensa ya yi ya ce ta zauna, wani kallo ta yi masa sai kuma ta yi yadda ya ce ɗin, duk da yadda gabansa ke ɗan faɗuwa saboda fargabar abun da zai iya biyo baya, amman haka ya tattaro ƙwarin gwiwa cikin kwantar da murya ya fara mata magana, "Aseeya...dama magana ce nike son yi maki ko kuma in ce nasiha da ta shafi rayuwar ki a matsayina na ɗan'uwanki...ina fatan zaki fahimce ni, ina son in ja hankalinki ne Aseeya, kada ki bari ruɗin zamani ya yi tasiri a kan ki, a matsayin ki na mace Allah ya yi maki daraja, kada ki bari wannan darajar ta ki ta zube, mutuncin kowace ƴa mace ɗakin mijinta, yadda kike tubarkalla na san kina da masu son ki da aure, kada ki bari damar ta wuce ki, ki yi aure domin hakan shine zai fi zama alkhairi a rayuwarki, ki rabu da duk wasu maza masu zuwa wurin ki ba da alkhairi ba ko zancen aure, domin da sun samu abun da suke so a wurin ki za su bar ki kuma ba lalle su aure ki ba, shi namji duk abun da ya yi ado ne, ita kuwa mace abu kaɗan ke ta6a matuncin ta...." Tun da ya fara maganar ta ke bin sa da wani kallo irin na mamaki ta ɗan yamutsa baki, can ta katse shi a harzuƙe ta miƙe tana faɗin, "Ban gane inda ka dosa ba Mukhtar, mi kake nufi? Wani abu ka ga na aikata da zaka zauna kana mani waɗannan maganganun, ko kuwa kana son ka ce su iyayena ba su kula da tarbiya ta shine zaka zauna kana mani wani nasiha..." Yadda take yin maganar tana wani fizge fizge sai ka ce Mukhtar ɗin ba matsayin yayanta yake ba, maganganun da take yi ne cikin ɗan ɗaga murya da alama suka jawo hankalin Ammi ta fito, nufo su ta yi tana tambayar mike faruwa, Aseeya ta juya tana faɗa mata maganganun da Mukhtar ɗin ya yi mata, cikin ɗaure fuska Ammi ta juya ta kalli Mukhtar da ya sadda kan sa ƙasa, a harzuƙe ta ce, "Wato dama zuwan da kake yi gidan nan ba don Allah bane da wata manufar ne ke nan." Da sauri
Chapter 100 · 0% Book details