← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 197

Sashe 149

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren la'asar su Leemarh suka iso Abuja, lokacin da suka isa gida, cike da farin ciki su Batool da Sultan har da daddyn su suka tarbe su a haraban gidan, ciki suka nufa daddy na yi ma Fahad ya hanya, su Batool sun kakkama Leemarh sosai suke ta murnar dawowar ta, a nan cikin babban falon suka zauna daddy na faffaɗan murmushi idonsa akan Leemarh ya ce, "Leemarh ƴan hutu, hankali ya kwanta ko an sha hutu a Funtua." Murmushi kawai ta yi masa, Batool ta ce, "Yaya Leemarh da muka dawo daga Kano saida muma muka ce muna son zuwa Funtua wurin ki momy ta ce bamu zuwa." Daddy ya yi saurin cewa, "Ai saboda hutun ya kusa ƙarewa ne, ku ma zaku je idan aka ƙara yi maku hutu." Leemarh dai ta yi shiru a ranta tana tunanin yadda itama za su ƙare da mom ɗin idan aka ƙara yin wani hutu ta ce zata Funtua, bayan ɗan lokaci ta tambayi Batool ina mom bata ganta ba ta ce mata tana part ɗinta, shiru Leemarh ta yi tana tunanin bata san ta dawo bane da bata zo ta tarbe ta ba, dad ya ce ma Leemarh ta je ta yi ma chef Alima magana ta shirya abinci ba a san ko Fahad na jin yunwa ba, Fahad na ɗan murmushi ya ce ai baya jin yunwa, miƙewa Leemarh ta yi ta nufi kitchen, cikin fara'a su chef Alima suka tarbi Leemarh tare da yi mata an dawo lafiya, bayan ta sanar da su a kai abinci dining ta fito ta wuce bedroom ɗin mom ɗinta, kwance ta iske ta hannunta riƙe da wayarta tana amsa kira wanda aka yi mata ya tashe ta daga baccin da take yi, tsayawa gefe Leemarh ta yi tana jiran ta gama, bayan dan lokaci ta gama yin wayar ta ɗaga ido ta kalle ta kafin ta janye idanun nata, bayan ta ajiye wayar ta maida kanta saman pillow ta kwanta, jikin Leemarh ne ya yi sanyi ganin halin ko in kulan da ta nuna mata, kamar ta juya ta fito daga ɗakin sai kuma a sanyaye ta ce, "Mom baki ga na dawo ba?" Ɗago ido ta yi ta watsa mata wani kallo ta ce, "To idan na ga kin dawo sai in yi maki mi? Ai da kin zauna can kawai ba sai kin dawo ba." Leemarh ta yi shiru tana bin ta da kallo can ta ce, "Ki yi haƙuri." Shiru bata ce mata komai ba, jiki a sanyaye Leemarh ta nufi barin ɗakin, mom ta yi ƙwafa rai 6ace ta ce, "Zan ɗauki mataki ne, ba zan zuba ido duk a mallake mani ko ba da kowa idan ya je sai ya samu wuri bai sai dawowa, don munafunci yaushe kika ta6a zuwa Kano hutu kika zauna haka." Duk Leemarh na jinta har ta ƙarasa ƙofa ta fita, lokacin da ta dawo falo Batool kawai ta iske ta sanar da ita cewa su dad sun tafi salla, itama Leemarh ta wuce zuwa ɗakinta, jikinta duk ya yi sanyi duk da ta san halin mom ɗin nasu amman bata ji daɗin abun da ta yi mata ba. Bayan sun dawo daga masallacin ta fito suka zauna cin abinci tare da Fahad, kaitsaye 6angaren mom dad ya nufa, har lokacin tana a kwance amman ba bacci take ba, ta ɗaga ido ta kalli dad da ya shigo kafin ta janye idanunta, daga bakin gadon ya tsaya ya ce, "Ashe idanun ki biyu, baki ga lokacin salla ya yi bane." Shiru bata ce masa komai, ya ce, "Ga su Leemarh sun iso tun ɗazu, yakamata ki fito ku gaisa da Fahad." Nan ma bata tanka sa ba, sai da ya ƙara ce mata bata ji yana magana ba sannan ta wurga masa wani kallo ta ce Fahad ɗin wani babban baƙo ne da dole sai ta taso sun gaisa, shiru dad ya yi fuskarsa ta nuna alamun 6acin rai, ganin haka ta sake cewa, "Ba yana a gidan ba ko yanzu zai tafi, idan na fito mun gaisa." Shiru bai ce mata komai ba sai ma ya juya ya nufi barin ɗakin ta bi sa da wani kallo. Da daddare bayan dad sun dawo daga sallar magrib tare da Fahad, a nan main falo suka zauna dad ya kira Leemarh ta waya ya ce ta je ta gyara ma Fahad part ɗin Deen, koda Leemarh ta je a kulle ta iske part ɗin, ta dawo wurin dad ta sanar masa, da ɗan alamun mamaki dad ya ce waye ya rufe part ɗin ta ce itama bata sani ba, ya ce ta je ta tambayi mom ɗinsu ko makullin part ɗin na wurinta, bayan Leemarh ta iske ta a ɗakinta ta tambaye ta, fuska a haɗe ta ce bata san inda yake ba, shiru Leemarh ta yi tana kallonta kafin ta juya ta tafi a cikin ranta tana mai zargin ita ce ta rufe part ɗin ta 6oye makullan, koda ta koma ta sanar ma dad shima shiru ya yi a ransa yana zargin mom ɗin ce zata dauke makullan don in ba ita ba waye zai aikata hakan, Fahad da ke zaune ya ce ma dad lafiya lau zai yi amfani da part ɗin baƙi tun da ba ga keys ɗin ba, shiru kawai dad ya yi ya san ko ya je ya yi mata magana ba bada makullan zata yi ba. Bayan sallar isha suka zauna cin abinci har da dad amman ban da mom da har lokacin bata zo sun gaisa da Fahad ba, bayan sun gama Fahad ya wuce part ɗin baƙi da dad ya sa an gyara masa. Bayan Leemarh ta gama yin shirin kwanciya ta ji tana son zuwa wurin Fahad su yi hira don gobe da safe zai wuce, fitowa ta yi zata je wurinsa sai kuma ta tuna da yana shan baƙin shayi duk dare, don da tana Funtua ma ita ce ke haɗa masa, kitchen ta wuce ta fara haɗa masa, bayan ta gama ta zuba a cikin wani ɗan madaidaicin flask ta daura a saman tray ɗinsa ta haɗa da cup da spoon sai sugar, tana riƙe da tray ɗin jikinta sanye da doguwar rigar bacci ta yafa gyale a a saman kai ta fito ta nufi ƙofar da zata fita baya, tana kusa kaiwa kofar ta ji muryar mom ɗinsu tana tsaida ita, juyowa ta yi tana kallon mom da ta nufo ta jikinta sanye da riga da wando na bacci, wani kallo ta jefa mata bayan ta iso gabanta ta ce mata ina zata je, Leemarh ta ce, "Zan kai ma yaya Fahad ne." mom ta ɗaure fuska ta ce, "Dama aikin ki ne hakan idan aka yi baƙo?" Ɗan ɗaure fuska Leemarh ta yi ta ce, "To ai shi ba baƙo bane ko." Mom ta watsa mata wani kallo ta ce, "Idan ba baƙo bane shi minene? Ko nan ɗin gidansu ne?" Leemarh ta yi ɗan kasa da murya ta ce eh ai nan kaman gidan su ne, "Idan sai ke ce zaki kai masa sai dai idan kada ya sha, je ki maida su kitchen!" Tura baki Leemarh ta yi zata yi magana mom ta kwatsa mata tsawa tare da nuna mata hanyar kitchen, tsaye mom ta yi a bakin ƙofar kitchen ɗin har saida ta je ta ajiye kayan ta fito, bayan ta fito fuska a ɗaure ta wuce ba tare da ta kalli mom ɗin ba ta nufi komawa ɗakinta, mom ta ɗaga murya tana faɗin, "Wllh idan kika je kai masa abun nan ranki sai ya 6aci." Leemarh bata ce mata komai ba bata kuma juyo ba, bayan ta koma ɗakinta a bakin gado ta zauna ranta a 6ace, har cikin ranta tana son ta je wurin shi su yi hira ba kamar da zai tafi gobe, ta ɗauki ɗan lokaci a haka, can ta kai hannu ta janyo wayarta, kiran sa ta yi bai ɗaga ba har ta tsinke, sai gashi ya biyo kiran, bayan ta ɗauka ya ce, "Leemarh..." A sanyaye ta amsa, "Baki yi bacci ba?" Ta ce masa eh, ya ce, "Yakamata zuwa yanzu kin yi bacci don ki ƙara hutawa sosai, ga gobe zaku yi resuming school." Shiru ta ɗan yi sai kuma ta ce, "Kawai bana jin baccin ne, ina tuna da a Funtua ne yanzu muna tare muna hira, ko kana aiki ina taya ka zama muna yin hira." Tana jiyo ɗan murmushin da ya yi ya ce, "Ko har kin fara missing hakan ne?" A hankali ta ce eh, "Idan kina so sai in zo mu yi hiran." Har sai da ta ɗan buɗa ido alamar jin daɗi ta ce masa ba abun da yake yi ne, ya bata amsa da eh kawai yana kallo ne, ta ce to idan bata takura mashi ba, bayan sun gama ta miƙe fuskarta da murmushi ta nufi ƙofa ta fita, tana zuwa cikin babban falon sai gashi ya shigo ta kofar baya jikinsa sanye da pajamas, murmushi suka shiga sakar ma juna har ya ƙaraso inda take ya zauna akan kujera, ta ce bari ta kawo masa shayi ya ɗaga mata kai, bayan ta dawo a saman table ta ɗaura ta haɗa masa don har yanayin yadda yake son sugar ta sani, itama ta haɗa wani ta zauna a kusa da shi a saman 2 seater da yake zaune, a nutse suke shan shayin su suna ɗan yin hira, after a while sai ga mom ta shigo cikin falon, tsayawa ta yi daga bakin part ɗinta tana bin su da kallo da alamun mamaki da kuma 6acin rai, wato Leemarh ta raina ta har haka, data hana ta kai mashi shine ta kira shi nan, gashi kana ganin a yadda suke zaune dole ma ka zargi akwai soyayya a tsakanin su, aikuwa zata nuna ma Leemarh iyakarta, a fusace ta nufo su tana kusa zuwa inda suke Leemarh ta lura da ita nan take ta sha jinin jikinta, ganin in da Leemarh ke kallo da yadda yanayin fuskarta ya sauya ya sa Fahad juyawa suka haɗa ido da mom wadda tun da ya zo sai yanzu ya ganta, daidai tana zuwa in da suke dad ya shigo cikin falon dama fita
Chapter 149 · 0% Book details