Sashe 8
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"I don't know why mom is acting so inappropriately...." Ya faɗa looking worried, shiru Fahad ya yi tare da kauda idanunsa gefe, kasancewar shi mai zuciya ba tun yanzu ba abubuwan da mahaifiyarsu Deen ke yi ma danginsu ke ci masa tuwo a ƙwarya, ba don karfin zumuncin dake tsakaninsu da ƴan'uwansu ba da tuni sai ta fuskanci 6acin ransa kan abubuwan da take yi, duk irin yadda suke janye jiki da gidan gudun wulaƙancinta hakan bai sa sun tsira ba, da alama so take kwata-kwata su daina zuwa gidan wanda hakan abu ne kuma da ba zai yuwu ba, suna ƙaunar junansu shi da sauran ƴan'uwansa, musamman Deen da Fahad akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu tun tasowar su, mahaifin Deen ya so Fahad ya zauna gidan tare da su saboda ganin yadda suke ƙaunar juna, saidai mahaifiyarsa firr ta ƙi amincewa ta nuna bata son ya zauna a gidan, a nan gidan Fahad ya yi karatunsa na secondary cike da ƙyara da kuma hantara daga wurin mom, idan dad baya a gidan haka zata mayar da shi kamar wani yaron gida, shine gyaran gida da su aike duk da a lokacin Deen ba wani girma ne da shi ba, yana nuna mata rashin jin daɗin hakan da take yi amman hakan bai sakawa ta bari, ya sha cewa sai ya faɗi ma Dad abubuwan da take masa amman Fahad ke hana shi ya ce masa in har ya faɗi ma dad to za su 6ata kuma zai tafi ya bar gidan, hakan yasa Deen bai ta6a sanar ma dad ɗin nasu ba, duk da a lokacin shima dad din yana ɗan fahimtar ƙuntatawar da take ma Fahad ɗin, sai dai ko ya yi mata magana sai ta nuna ita mi take yi masa kuma tun da matsayin uwa take a wurin sa ba dole ta rinƙa tsawatar masa ba kan abun da ba daidai ba, kawai dai dad na yin shiru ne don ba wani katabus zai iya yi ba kan hakan amman ya san tana takura masa, hatta iyayen Fahad a lokacin sun fahimci zaman takura yake a gidan ba kamar da suka san halin mom ɗin su Deen na rashin mutunci, saidai ko an tambaye shi kan irin zaman da yake yi idan ya je hutu gidansu sai ya nuna masu lafiya lau yake zaune, a lokacin bai son su san halin da yake ciki ne ba don komai ba sai don ka da su raba shi da Deen sanin ba zai jure hakan ba, wani lokacin idan ta kai Fahad ɗin bango ya gaya mata magana da yake yana da zuciya har bugunsa take. Lokacin da Deen ya gama ƙaramar secondary ne ta matsa kan tana son ta maida shi London wurin ƙanwarta ya ƙarasa karatunsa a can, ba don komai ta yi hakan ba sai don ta raba shi da Fahad wanda a lokacin shi ya kammala karatunsa na Secondary, jin haka yasa dad ɗin Deen ya ce su tafi tare da Fahad sai shima ya ci gaba da karatun nasa a can, aikuwa ta hau sama ta dire kan sam hakan ba zai yuwu ba ya koma gidansu shima mahaifinsa ya nema mashi makarantar da zai ci gaba, lokacin ya so ya kafe kan ra'ayinsa amman sai ta fake da nuna mashi abun zai yi yawa a ce sun je can har su biyu sun zauna a wurin su, ya nuna mata ai ba dole sai su duka sun zauna ba sai shi Fahad ya zauna a makaranta amma ta dage kan ya san dai irin shaƙuwar da suka yi ba yadda za ai suna a ƙasa ɗaya su zauna a wuri daban-daban. Ƙarshe dai sai da ta yi nasarar yadda ta sa shi janye ra'ayin kai Fahad can. Deen ya sha kuka lokacin da za su rabu da Fahad, tare da daddynsu suka raka shi Funtua da zai koma, a can ma ganin yadda Deen ya shiga damuwa kakarsu Hajiyar Ambasada sai da ta ce ma Alhaji Ibrahim mi zai hana a tura su tare da Fahad din amman sai shima ya fake da faɗi mata irin abun da mom ɗin su Deen ta faɗa, a lokacin ta fahimci matarsa ce bata son hakan, da yake ita ba mai shiga ta yi karan tsaye cikin al'amuran ƴaƴanta ba ce, tsakaninta da matayen su sai in abu ya wuce gona da iri take shiga hakan ya sa ta ƙyale su, ƙarshe Deen yana ji yana gani aka raba shi da yayansa da yake matuƙar ƙauna a cikin zuciyarsa suka koma Abuja ba tare da shi ba. Bayan tafiyar Deen London shima Fahad mahaifinsa ya nema masa makaranta a ƙasar Malaysia ya tafi yin karatun likitanci. Duk da sun yi nesa da juna hakan bai sa sun daina zumunci ba, suna ziyartar juna duk suka samu hutu, ba kamar Deen da yake ɗan gatan Maleek ne ba ƙaramin ji yake da shi ba saboda bai da ɗa namiji, duk abun da yake so yana masa hakan yasa duk lokacin da ya nuna yana son zuwa Malaysia wurin Fahad sai ya samu lokaci ya kai shi da kansa, dama kuma akwai kamfanonin da yake yin hulɗar kasuwanci da su a can, hakan ma sai da mom ɗin Deen ta yi ƙoƙarin hana ziyartar junan da suke yi ta hanyar yi ma Maleek magana kan ya daina biye ma Deen, ta ce ko ya ce yana son zuwa wurin Fahad ya daina kai shi, sai dai bata yi nasara ba don Maleek ɗin nuna mata ya yi ai hakan ba wani abu bane kuma abun da suke yi yana da kyau ƙarfafa zumunci ne, da bata yi nasara ta bangaren sa ba sai ta koma kan wadda take da iko da ita wato matarsa ƙanwarta Safna, tsawatar mata ta yi a kan ta hana Maleek kai Deen da yake yi wurin Fahad, a lokacin Safna ta nuna mata zata yi hakan, amman da yake itama tana tsananin son Deen duk abun da yake so tana yi masa bata hana ɗin ba, ƙarshe dai dole mom ɗin ta kyale su ta ƙarata da baƙin cikin hakan.
Juyowa Fahad ya yi ya kalli Deen da har lokacin 6acin rai ke kwance akan fuskarsa, dafa kafaɗarsa ya yi cikin kwantar da murya ya ce, "You shouldn't worry yourself about dat, hakan na faruwa, wasu mutane suna yin abun da ake ganin ba daidai ba, su kuma a wurin su basu ganin hakan a ba daidai ba, so hakan ya daina damun ka." Ɗan yamutsa fuska Deen ya yi, "Amman ita mom ta san abun da take yi ba daidai bane tun da ba kowa take ma hakan ba. Tun ba yanzu ba Ya Fahad bana jin daɗin the way take treating duk dangin daddy, kaman sun mata wani abu?" Ya ƙare fuskarsa a yamutse, ɗan murmushi da ya fi kama da na takaici Fahad ya yi jin har yaranta sun san tana yi ma danginsu ba daidai ba, ƴar ajiyar zuciya Fahad ya sauke,
"Zai iya yuwuwa akwai abun da ya faru da ya sa hakan ke faruwa." Fahad ya faɗa ba don yana zaton hakan bane ya dai ce ne kawai. Duk da yana yaro sosai aka aurota bai tunanin akwai abun da ya ta6a faruwa tsakaninta da danginsu da har ya haifar da hakan, dama can tun da ya taso yake jin ana ƙorafi game da halinta.
"Ya Club É—in na ku, wani wasa zaku buga in ka koma?"
Da murmushi Deen ya faɗi masa ya ce, "Ko ka zama football fan ne? Da fa kana son ƙwallo sosai, ka tuna lokacin da muke yi a cikin compound kai ta fyaɗa ni da ƙasa, in kafe sai na rama ƙarshe da kuka muke gamawa ka dawo kana rarrashi na" Ya ƙarasa yana sakin faffaɗan murmushi, dariya Fahad ɗin ya yi tunowa da lokacin, gyara zama ya yi ta yadda ya ɗan zamo jikinsa ya kwanta kansa a jikin kujerar,
"Yanzu ma ina ɗan kallon wasu match ba sosai ba, amman duk wasan ku ina kallo." Kai Deen ya jinjina, ya yarda da abun da ya faɗa don duk suka yi wasa suka yi nasara sai ya taya shi murna ta chat ko kiran waya, koda basu yi nasara ba sai ya yaba masa tare da ƙara ƙarfafa masa gwuiwa.
"Yanzu na fi kallon boxing sosai." Fahad ya faÉ—a yana É—an shafa sajensa,
"Ka ce ka fi son kallon mugunta, Allah Ya sa ba kana koya bane watarana ka karya ma wani jaw." Dariya sosai Fahad É—in ya yi,