← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 197

Sashe 192

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ba ko don ki faranta masa saboda biyayyar da ya yi maki?" Ta wani kaɗa kai ta ce, "Ko mi zaka ce Ibraheem ba zan amince masa ya auri wannan ƴar matsiyatan ba wllh, ni ce na ɗauki cikin sa, na haife sa kuma na raine sa har ya girma, don haka ina da ikon in ce ga abun da nike so akan sa da wanda ban so musamman abun da nike ganin zai cutar mani da shi..." A ɗan fusace dad ya katse ta da faɗin, "Saboda kema hakan aka yi maki? Ki faɗa mani ke kin ta6a nuna kina son abu aka hana ki?" Ta kaɗa baki ta ce, "Ibraheem, yanzu magana ake ta ɗana, da kuma muradina akan sa." Dad ya ce, "Da kike ta wani maganar ɗan ki, ai ina ce bake ce kaɗai kika haife sa ba, don haka nima a matsayina na mahaifinsa da nike iko da shi ina goyon bayan zabinsa, muddin yana son yarinyar to sai ya aure ta, saboda nima ba a hana ni aure wadda nike so ba." mom Jameela ta saki wata bazawarar dariya ta ce, "Da aka kasa dai yin nasarar hana ka auren wadda kake so, sannan aka amince maka." Dad ya hau ɗan jinjina kai yana mata wani kallo cike da 6acin rai, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, cike da 6acin rai ya ce, "Kin faɗi gaskiya, shima ki jira ki ga yadda hakan zata kasance akan sa, ai dama duk abun da ka yi will definitely come back to you." Yana kai wa nan ya miƙe ya nufi barin ɗakin, mom ta bisa da iso, sosai maganarsa ta ƙarshe ta dake ta, mi yake nufi da hakan? tunanin baya ta shiga yi lokacin da aka hana ya aure ta, yadda suka shiga suka fita har sai da ta aure shi, ke nan hakan zata iya kasancewa akan itama yarinyar, su shiga su fita har sai ta auri Deen, dama tun farko tana zargin cewa ba haka nan suka bar Deen ba, ta hanyar asiri suka yi nasarar saka soyayyarta a zuciyarsa....ina!! Sam bazata sa6u ba bindiga a ruwa, ba zata ta6a yin sakacin da hakan zai faru ba, dole ta nuna masu idan su asubanci suka yi a aikata ma Deen hakan to ita a hanya ta kwana don kare ɗanta, zumbur ta miƙe tare da ɗaukar wayarta ta shiga latsa ta yayin da take nufar wurin closet ɗinta, ta kara wayar a kunne ciki da bada umarni ta furta, "Get ready, we are leaving for Funtua now!" Daga haka ta cire wayan, sake yin wani kiran ta yi nan ma ta bada umarnin a shirya mota za su tafi Funtua yanzun nan...without wasting much time ta gama shiryawa cikin tsadaddan lace, ta zuba gwala gwalai a wuya da hannu ta fito a hamshaƙiyarta..lokacin da ta fito main falo ba kowa a ciki, kai tsaye ta nufi hanyar fita, a daidai gaban entry hall aka faka ƙatuwar baƙar jeep da za su tafi da ita, tana fitowa wani jami'i da ke tsaye a jikin motan ya yi saurin buɗe mata ƙofar baya tare da gaishe da ita, ko kallon sa bata yi ba ta shige, ya maida ƙofar ya rufe sannan ya buɗe front seat ya shiga, daga haka driver da ke zaune a driver seat ya ja motar suka tafi, sam dad bai san da tafiyarta ba, don bayan ya fito daga part ɗinta gidan gaba ɗaya ya bari ya wuce guest house ɗinsa ya je ya taushi zuciyarsa don ba ƙaramin 6ata mashi rai mom ta yi ba. Bayan sun ɗau hanya, gaba ɗaya mom Jameela a ƙagare take da ta gan ta a Funtua, sai ta ga tafiyar ta yi mata nisa, haushin ta da ba a zuwa garin a jirgi....
Chapter 192 · 0% Book details