← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 197

Sashe 134

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*✨A CIKIN RAYUWA✨*

ZAINAB BATURE

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

43

Bayan sun fito a motar Fahad sun hau hanya, a hankali yake ɗaga ido ta cikin madubin gaban motan yana kallon Leemarh da ta mayar da glasses ɗinta tana kallon hanya, sosai ta yi masa kyau har wani girma ya ga ta ɗan ƙara, a hankali ya ga ta juyo ta kalle sa ta cikin glasses ɗin, ɗan juyawa ya yi shima ya kalle ta calmly ya furta, "Kin yi kyau sosai." ta yi murmushi tare da sauke kanta ƙasa, ɗagowa ta yi ta kalle shi ya mayar da idanunsa kan hanya, ta ce, "Kai ma ka yi kyau." Ya ɗan buɗa ido ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Ina wani kyau a wurin wanda ya dawo daga aiki." Tana murmushi ta ce masa ya aikin, ya bata amsa da, "Ba daɗi." ta ce, "Why ka ce haka?" Da ɗan murmushi ya ce "Mutum koda yaushe yana kai da komowa kan hanya, kullum cikin gajiya..." Tana ta kallon shi ta cikin glasses din a hankali ta ce, "Sannu..." Ya ɗan ɗaga kai, sai kuma ya ji ta ƙara cewa, "Idan ka yi aure gajiyan zai ragu." Ya ɗan juyo ya kalle ta ya ce, "Ta yaya?" Ta ɗan yi shiru tana murmushi sai kuma ta ce, "Idan ka dawo daga aiki wife en ka zata taimaka maka, kamar ta haɗa maka ruwan wanka, ta taimaka maka ka shirya, ta shirya maka abinci har ma ta baka da kanta, da sauran abubuwa, kuma sannan ma...zata maka massage don rage gajiyan." Tana ƙarasa maganar ta yi saurin juyar da fuskarta tana kallon gefe, Fahad ya ɗan buɗe ido tare da juyowa ya kalle ta, maida idonsa ya yi kan hanya yana ɗan murmushi, duk da ya san ta isa ta san komai game da aure ya ɗan ji mamakin yadda ta iya faɗa masa hakan. Bayan sun iso, Fahad ya parker motan a gaban ginin, tare suka fito sai lokacin Leemarh ta kalle shi tun bayan da ta yi maganar ɗazun da suna hanya, murmushi suka sakar ma juna ya zagaya inda take tare da yi mata alamar su shiga, sai da ta ɗauko ledan da ta taho da ita a back seat wadda ke dauke da tsaraban da ta yi masu, falon gidan suka shigo wanda yake tsaf sai ƙamshi ke tashi, Khaleel na kwance saman doguwar kujera yana latsa waya basu daɗe da zuwa gidan ba weekend shi da Sadeeya daga makaranta, yana ganin Leemarh ya ɗan buɗa ido tare da tashi zaune, yana mata murmushi ya ce, "A surprise visitor saukan yaushe?" Itama murmushin ne akan fuskarta ta nufo shi, a kusa da shi ta zauna ta ce, "Bamu daɗe da zuwa ba ni da dad." Khaleel ya ce yanzu ko ya ga labarin zuwan dad ɗin ashe tare suke ta ce masa eh kafin ta gaishe da shi, bayan ya amsa ya tambayi sauran yan gidansu ta ce masa suk suna lafiya suna gaishe da su, Binafa ce ta shigo cikin falon ta yi gayun juma'a, tana hango Leemarh ta zaro ido tare da nufo ta da sauri, da mamaki ta furta, "Yaya Lermarh ke ce?" Dariya Leemarh ta yi mata ta ɗaga mata kai, aikuwa ta nufo ta da gudu suka rungume juna, ɗagowa Binafa ta yi still da alamun mamaki akan fuskarta ta ce, "Yaushe kika zo?" Ta bata amsa da yanzu suka zo tare da yaya Fahad daga gidan hajiya, miƙewa ta yi da sauri tana faɗin bari ta je ta gaya ma su mommy ta zo, dawowa ta yi tare da Sadeeq tana faɗin ga momy nan zuwa, Sadeeq ya gaishe da Leemarh yana murmushi, ita ma shine akan fuskarta ta amsa masa tare da tambayar sa ya karatu, momy ce ta shigo cikin falon tana sanye da hadaddan atamfa ɗinkin doguwar riga ta yi ɗaurin kallabi mai kyau da ya bayyanar da tufkar kitsonta dake a naɗe, da faffaɗan murmushi ta nufo Leemarh tana faɗin, "Oyoyo, welcome my daughter..." Leemarh ta miƙe tana murmushi, momy na ƙarasowa wurinta ta rungume ta, ɗago ta ta yi ta ce, "Daughter sannu da zuwa, saukan yaushe?" Leemarh ta bata amsa da basu daɗe da zuwa ba ita da dad, momy ta tambayi sauran yan'uwanta da mom ɗinsu ta ce mata duk suna lafiya suna gaishe da su, momy ta ce ta zauna tare da kallon Binafa ta ce mata ta je kitchen ta sa akawo ma Leemarh abun sha ta amsa tare da nufar kitchen, momy ta zauna tare da kallon Fahad ta yi masa sannu da dawowa ya amsa, ƴar hira ta shiga yi da Leemarh kafin Binafa ta dawo riƙe da tray mai ɗauke da jug da cup a sama, bayan ta ajiye a saman center table ta zuba ma leemarh, momy dake murmushi ta ce ma Leemarh ta sha zobo ta amsa tare da yin godiya, sosai zobon ya yi ma Leemarh daɗi tana murmushi ta kalli momy ta ce mata ya yi daɗi, momy ta ce mata ta ƙara mana dama ba a daɗe da aka haɗa shi ba ta gaji da lemu shine ta saka aka haɗa, bayan Leemarh ta ƙara sha ta juya ta kalli Fahad dake zaune yana ta bin su da ido ta ɗan yi masa murmushi, sai kuma ta zuba zobon ta tashi ta miƙa masa tana faɗin, "Yaya Fahad ga shi kaima ka sha." Amsa ya yi tare da yi mata godiya, momy ta yi murmushi, Sadeeya ce ta shigo falon tana sanye da rigar wanka da hula, lokacin da Binafa ta je sanar mata game da zuwan Leemarh ta shiga wanka, nufo cikin falon ta yi cike da murna cikin ɗan ƙaraji take faɗin, "Oyoyo my namesake..." Miƙewa Leemarh ta yi tana ƴar dariya ta nufe ta suka rungume juna, gyalen rigan Leemarh ya zame ƙasa hakan ya bayyanar da baƙar sumarta da ke a fake an lanƙwashe ta, cikin washe baki Sadeeya ta ɗago ta ce, "Ina wanka ban san kin zo ba, ke da wa kuka zo? Ko ku duka?" Leemarh ta bata amsa da ita da dad ne kawai, Sadeeya ta tambayi dad ɗin ta ce yana gidan hajiya, "Amman na ji daɗin zuwan ki sis irin sosai ɗin nan don an kwana biyu ba a haɗu ba. Ina su Omar su ya basu zo ba, ko baya ƙasar?" Leemarh ta ce, "Ya Omar yana nan ya ce zai zo, su Batool kuma za su je Kano ne da mom, amman suma dad ya ce duk za su zo bada daɗewa ba." Sadeeya ta ɗaga mata kai tana ta mata murmushi kafin ta kuma cewa, "Hope dai hutun kika zo mana kamar yadda yaya Fahad ya faɗa cewa za ki zo nan hutu." Leemarh ta ɗaga mata kai alamar eh, Binafa ta ce, "To ina box en kayan ki?" Leemarh ta ɗan buɗa mata ido ta ce, "Ban zo da su ba, na ki zan rinƙa sakawa." Binafa ta ɗan waro ido sai kuma ta yi dariya ta ce ai kayanta ba zasu yi mata ba sai dai in na yaya Sadeeya suma kuma ba lalle su yi mata ba saboda ta fita jiki, Leemarh ta yi murmushi ta ce mata wasa take kayanta na gidan hajiya, a ɗokance Binafa ta ce to sai su je a ɗauko, Sadeeya ta kama hannun Leemarh ta ce su je ɗakinta ta shirya, momy ta ce ya zata ja ta ko abinci bata ci ba, Sadeeya ta ɗaga mata hannu tana faɗin ai shiryawa kawai zata yi su fito, suna kai wa daidai za su shige inda bedroom suke Leemarh ta juyo da niyyar satar kallon Fahad, idanunsu suka shiga cikin na juna ashe shima bin ta ya yi da kallo, a tare suka sakar ma juna murmushi mai taushi.
Chapter 134 · 0% Book details