Sashe 189
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ce kada ya damu duk a ƙoshe suke sun ci abinci a can gida kafin su taho, baban su Salma ya ce duk da haka nan ma yakamata su ci tun da saboda su aka yi, aunty ta yi saurin cewa a zuba masu sai su tafi da shi, innarsu Salma ta yi saurin miƙewa ta nufi kitchen, baban Salma ya ce to su ɗebi goron da aka kawo wanda za su yi amfani da shi, Sageer da Auwalu ne suka kai masu goron da abincin da aka zuba masu a coolers masu kyau zuwa mota, koda baban su Salma ya yi masu magana kan su ɗauki wani abu cikin kuɗin da aka kawo suka ce a'a wannan nasu ne su yi amfani da su wurin fara shirye shiryen bikin, aunty tace bikin da an ce ba a buƙatar komai, alhaji Sani na murmushi ya ce dole ai za a yi wasu hidindimun na kuɗi, da ƙyar suka amshi wani abu a cikin kuɗin matsayin na sauran abubuwan saka rana da za a siya, aka rako su har waje ana ƙara masu godiya suka tafi....bayan sun dawo cikin gida, cikin wasa baban su ya ɗan ɗaga murya yana faɗin, "Ina amaryar tamu ta shige ne?" Duk aka yi dariya, "Mamana kina ina?" Ya faɗa idonsa akan ƙofar ɗakin innarsu don ya san tana ciki, fitowa Salma ta yi kanta a ƙasa tana ɗan murmushi, ta tsaya daga gaban baban nasu ba tare da ta kalle shi ba, ya kai hannu ya matso da ita ya ɗan yi mata side hug, ya ce, "Duk kunya ce mamana." Salma ta noƙe kai bata ce komai ba, "Na taya mu murna sosai, Allah Ya sa alkhairi, Allah Ya nuna mana." Duk aka amsa da amin, ya kalli innarsu ya ce, "A kawo masu abinci suma tun da suka zo ko ruwa basu sha ba." Ta yi saurin amsawa tare da nufar kitchen aunty tana faɗin ai da yake ma ba wata yunwa suke ji ba, ya nuna ma Salma wuri ya ce ta zauna su ci abinci, yana ta kallonta ta nufi gefen aunty ta zauna, "Amman Kubra mi kike ba ɗiyar nan taki ne haka, ma sha Allah ta canza sosai, har girma ta ƙara." Aunty ta saka dariya kafin ta ce wani abu Imrana ya yi saurin cewa, "Fuskarta ma har ƙyalli ƙyalli take yi." Hamza ya ce kuma ta saka kaya irin na an indiyawa, duk aka saka dariya, aunty ta ce wannan duk aikin kayan gyaran fatan da angon nata ya kawo mata ne har da rigan ma, nan aka jere masu kayan lafiyayyan abincin da aka yi, farar shinkafa da lafiyayyan miya da ta ji nama, sai coleslaw da kuma peppered chicken har da lafiyayyan kunun aya da lemunan roba....bayan sun gama cin abincin aunty ta fiddo masu da tsaraban da suka yi kafin ta saka aka kai masu kayan su ɗakin Salma da tuni innarsu ta gyara shi, dama duk aunty ta zo a ɗakin babyn nata take sauka...haka iyalin suka kasance cikin farinciki sosai a wannan rana, da daddare bayan sallan issha nan suka baje cikin baranda har da baban su Salma da ya dawo da wuri ana ta hira cikin nishaɗi suna ciye ciye, Sageer sai cin goron saka ranar yake yana faɗin duk da baya cin goro ya zama dole ya ci wannan don na musamman ne, aunty da ke zaune jikinta sanye da doguwar rigar shan iska da hula itama goron take ta ci duk da bata ci tana faɗin ai cin wannan goro a gare ta ya zama wajibi, baban su Salma ya ce masu ɗazun bayan sallan magrib ya je gidan hajiyar ambasada ya yi mata godiya, aunty ta ce itama kuwa yakamata ta je, baban ya ce har kuwa tana tambayar Salma ya sanar mata da sun zo, aunty ta ce bari sai su je tare, Salma ta miƙe itama tana sanye da doguwar rigar bacci ta nufi ɗakinta, bada daɗewa ba ta fito hannunta riƙe da abu ta nufi innarsu ta zauna a gefenta, da murmushi ta ce, "Innarmu gashi, dama ke ce baki da waya android." Innarsu ta amshi wayan wadda tsohuwar samsung ɗin Salma ce da bata yi komai ba kamar sabuwa, tana murmushi ta kalli Salma ta ce to ta gode Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara ma rayuwa albarka, Sageer ya yi saurin cewa, "Amman dai kin san ni yakamata ki ba wayar nan, don tun lokacin da aka baki na nuna ina son ta." Aunty ta ce baƙin ciki zai ma innar tasu shi bai siya mata ba kuma an bata zai ce shi yakamata a ba, Sageer na dariya ya ce ba baƙin ciki zai mata ba yana nufin shi a bashi wannan sai ita ya bata tashi, Salma ta ɗan harare shi ta ce mi zata yi da wannan tsohowan wayar tashi da ta gama jin jiki, hannu ya kai zai rankwashe ta, da sauri aunty ta ce, "Wllh ahir ɗin ka Sageer, yanzu ba da bane, ka san dai waye zata aura in ka ci masa zalin mata ba ƙyale ka zai yi ba duk da kana yayanta, dama gashi yana da wasu gabza gabzan bodyguards da ni kai na lokacin da ya zo sai da na tsorata da na gan su." Duk aka yi dariya, baban su ya ce, "Ato kuma mu ba ruwan mu, ban da ma kuɗin yin belin ka idan aka kama ka." Sageer dai ya yi shiru yana kallon su yana dariya, a cikin ransa yana jinjina irin yadda Allah Ya ɗaukaka kanwar tasa, abun ka da uwa, innarsu tana murmushi ta miƙa ma Sageer wayan ta ce mashi gata ta bashi sai ya bata tashi ɗin, da sauri ya girgiza kai ya ce mata wasa fa yake, cikin kwantar da murya ta ce, "To ka amsa, ai ni na ce na baka, sai ka bani takan." Duk idanun kowa na akan Sageer da ke girgiza mata kai alamar ba zai amsa ba, aunty Kubra ta ce, "Koda yake ka ma cancanci a baka fa, don kai ne ka ɗaura hoton da ya yi silar ƙulla soyayyan." Sageer ya saki dariya don Salma ta faɗa mashi hakan, kuma ya gane hoton, shine ya yi mata shi kuma ba tare da saninta ba, lokacin innarsu ta gama taya ta tsafe mata kai an sharce shi, yana zaune gefe yana latsa waya ya yi mata hoton, shima lokacin hoton ya yi masa kyau sosai shine har ya ɗaura a status...sai da innarsu ta matsa masa duk su aunty suka saka baki sannan ya amsa tare da yi mata godiya, aunty ta amshi wayar shi tana dubawa ta ce, "Wayan taka ma ai ba wani tsufa ta yi ba, kawai glass ɗinta ne da ya ɗan tsattsage, kuma ai kaman ma akwai screen guard ko?" Sageer ya ce mata eh, dama ba ainihin wayan shi bace, wannan bai daɗe sosai da canza ta ba, kuma Salma ta san ba waccan tashin bace kawai sharrin ta ne data ce wayan tsohuwa ce, aunty ta ce gobe idan Allah Ya kaimu zata bashi kuɗi sai ya je a cire wannan screen guard ɗin a saka mata wani, sannan ya canza mata cover don wannan ta jiki innar tasu ba lalle ta ji daɗin amfani da wayan da shi ba, Sageer ya ce a'a lafiya lau ba sai ta bashi kuɗi ba zai kai a yi duk abun da ta ce, wayar Salma ce ta fara yin ringing duk suka kai idanunsu kanta, ta sadda kai tana kallon wayan wanda Deen ne ke kiran ta, "Mamana ba kiran ki ake yi ba?" Baban su ya faɗa, ta kasa bashi amsa kuma bata ɗago ba, aunty na murmushi ta ce, "Hala angon ne?" Salma ta ƙara sunne kai, baban su ya yi murmushi ya ce to ta ɗauka mana, ƙoƙarin miƙewa ta fara yi cike da jin kunya zata wuce ɗaki, Sageer ya kai hannu ya ɗan buge ta a jiki yana faɗin gulmamma wai su zata nuna ma ita mai kunya ce, baban su ya ce mashi ba dai zai kiyaye ba ko, aunty ta ɗan ɗaga murya tana ce ma Salma ta faɗa ma Deen cin zalin da Sageer yake mata, ita dai ta nufi ɗakinta ta shige....ba ƙaramar soyayya suka sha ba ta waya ita da Deen, sosai ta saki jiki har sai da ta ji inama ta janyo wata biyun bikin su.....