Sashe 91
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abun da ya ke so, ai shi ya san yadda ake komai." Dad ya yi saurin cewa, "Ni ina ganin zai fi ya je ɗin komai sai ya fi yuwuwa cikin sauƙi ba kamar tun da shi kusan ko ina yana da alfarma." Deen ya ce mata zai samu lokaci ya je, ba don ta so ba ta ce Allah Ya sa kada ya bar Omar ɗin ya yi ta jira, bayan buƙatar mota ya sake cewa yana son ya canza mashi iphone nashi zuwa latest one da kuma laptop ɗin sa, wani kallon baka da tausayi Leemarh ta yi mashi ba ta dai ce komai ba, Deen ya jinjina mashi kai alamar zai yi masa hakan, "Leemarh, you..." Deen ya faɗa bayan ya maida idanunsa a kanta, murmushi ta yi ta ce, "No, I don't need anything ya Deen, wannan da ka siya mani sun isa na gode Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara maka ɗaukaka." Dad da ya ji daɗin yadda ta yi maganar hankali ya amsa mata da, "Ameen.." Mom wani kallo ta yi mata ta ce, "Ke baki son a can za maki phone en na ki?" Dan yamutsa fuska Leemarh ta yi ta ce, "No, wannan nawa ɗin ya isa, sabuwan ma bata da wani bambanci sosai da wannan duk wasting kuɗi ne." Wani kallon ƙasan ido Omar ya yi mata dama ita ke bi masa sun cika ƴar tsama, fuska a ɗaure ya ce, "Wai ke don a ce kina da hankali ko, ai dai suna da bambancin kuma kowa na son ci gaba ba ai ta barin sa a baya ba, ƴar ƙauye kawai." Harararsa Leemarh ta yi a tsiwace ta ce, "Eeeeh ɗin, na ji ƴar ƙauyen ne ni, kuma su masu kamfanin iphone ɗin sune ke ci gaba suna ƙaruwa da mu shiyasa duk shekara suke yin sabo, mu kuma mu yi ta kwasar kuɗi muna siya instead of muma mu yi investing kuɗin mu ta yadda zuwa wani shekaran mu samu riba, ai rubibin siyan iphone ɗin ma shine ƙauyancin idan baka sani ba." Faffaɗan murmushi ne akan fuskar dad ɗin su sosai ta burge shi da zurfin tunaninta, fuskar mom ɗin su a ɗan tamke tana mata wani kallo ta ce, "Ai There is nothing wrong with mutum ya siya abun da ransa ke so idan yana da hali, hakan zai sa a rinƙa ganin kana ci gaba." Ɗan ta6e baki Leemarh ta yi dama ta san ba zata goyi bayan maganarta ba, wani lokacin har tunani Leemarh ta ke yi anya mom ɗin su na tausayin yaya Deen kuwa yadda take yawan faɗa masa buƙatu tana amsar maƙudan kuɗaɗe a hannunsa, "Ki faɗa masa abun da kike so bani son munafurci." mom ta faɗa da yar tsawa, yamutsa baki Leemarh ta yi, "To ni mom na faɗa bani buƙatan komai." Harara ta wurga mata ta ce, "Kina mace kuma budurwa zaki ce baki buƙatan komai!" Shiru Leemarh ta yi tana ɗan tura mata baki, dad ya ce tun da ta ce bata buƙatan komai ta ƙyale ta, duk da haka sai da ta ce ma Deen ya bada kuɗi ta ƙara ma gold din Leemarh girma ya ce to, shiru kawai dad ya yi shi kan shi yana ganin rashin tausayi a al'amurranta game da Deen, da aka zo kan Sultan shi cewa ya yi so yake a canza mashi ipad ɗin sa, shi dama bai da damuwa in dai zai yi games, lokacin da aka zo kan Batool tana dariya ta ce, "Labubu nike so zan saka shi a school bag ena." Ta faɗa tana noƙe kai, kallonta dad ya yi ya ce miye kuma lanbubu, duk suka ɗan yi dariya jin bai faɗa sunan yadda Batool ta faɗa ba, Leemarh ta ce masu teddy ne, wani kallo suka yi ma Batool, Omar yana ƴar dariya ya ce duk ta rasa abun da zata ce tana so sai teddy, dad ma ya ce ba akwai teddies a gidan ba, mom ta ce a ƙyale ta tun da shi ranta ke so, Leemarh ta yi saurin cewa, "Tsada ma gare shi fa akwai har na 250k." Ɗan wara ido dad ya yi ya ce teddyn ne ke dubu ɗari biyu har da hamsin! ta ce eh kuma salon ma a siya mata ya faɗi ko a ɗauke, mom ta ce a dai kyale ta tun da tana so, ta ƙara ce ma Deen itama sai ya bada kuɗi ta canza mata gold nan ma ya ɗaga mata kai alamar toh, ko da ya tambayi mom ɗin ita mi take so, wani murmushi ta yi ta ce ita ya bari za su yi magana daga baya, a cikin rai Leemarh ta ce, "Allah Ya cece ka ya Deen.." Ko da ya tambayi dad ɗin su shim bun da yake so, da sauri ya ce, "Ah ni bana son komai son, abubuwan da ka je ka yi a garina sun wakilci duk wani abun da nike so.." Tarar hanzarin sa mom ta yi ta ce, "Ya je dai ya yi bannar kuɗi kuma kana goya masa baya, yanzu ina amfanin wani club da ya je ya buɗe a wannan ƙauyen? Ina wani riban da zai samu a nan, maimakon in ma club ɗin yake son ya buɗe ya je Kano in da yake birni kuma harkar take da ƙarfi zai samu riba sosai, kuma ga Bashir shima ɗan ƙwallo ne sosai a can ko ba komai zai kula masa da club din ba tare da wata matsala ba." Duk kowa ya yi shiru bayan ta gama, sigh dad ya yi ya ce a can ɗin ma in sha Allah za a samu abun da ake buƙata, shiru ta yi ta ɗan tabe baki tare da kawar da kanta gefe, bayan shiru na ɗan lokaci Deen ya yi deciding sanar da su game da asibitin da za su buɗe da Fahad kamar yadda daddy Sa'ad ya ce masa ya yi, sosai dad ɗin su ya bayyana farin ciki da goyon bayansa, bayan ya sanar da su dad ya ce hakan tunani ne mai kyau da za su haɗa hannu wurin ginin asibitin, ita kuwa mom wani kallo ta bishi da shi lokacin da ya sanar da su, wani baƙin ciki ta ji ya zo mata wuya ba kamar da Deen ya ce daddy Sa'ad ya ce ya sanar da su, ke nan da ba lalle ya sanar da su ba? Ina! Sam basu isa su mallake mata yaro ba zata nuna masu iyakar su, dad ɗinsu na rufe baki a kausashe ta ce, "Ni ban goyi baya ba, ban kuma amince ba!" Kallon mamaki dad da Deen har da Leemarh suka yi mata, "Amman na ga abu ne mai kyau wannan suke da niyyar yi, asibiti ne fa za su yi haɗin gwiwa su gina." A fusace ta ce, "Shine abun da ban amince ɗin ba! If he wants to build a hospital, miyasa ba zai yi abun shi shi ƙaɗai ba, ai yana da halin da zai yi, kuma dole sai a can, komai su zai tare yana yi mawa ke nan, ya gina nashi a nan mana, akwai in da ya kai gina private hospital a Abuja ne, wace riba zai samu idan ya gina asibiti a ƙauye?" Sunkuyar da kai Deen ya yi ba tare da ya ce komai ba, Leemarh wani kallo take jifar mom ɗin nata da shi, Omar da Sultan da Batool su dai sauraro kawai suke, dad ɗinsu ma kallonta kawai ya ke har ta gama zazzaga masifar tata, ƴar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce, "Yanzu miye laifi ko illa don ya haɗa hannu da ɗan'uwansa sun yi abun ci gaba, kuma a bayanin da ya yi su ba ribar da za su samu ta kuɗi suke hanga ba, suna kwaɗayin samun lada ne ta hanyar sauƙaƙa ma al'umma." Wani kallo take bin dad ɗin da shi, bayan ya gama magana ta ce, "Kai kana tunanin idan suka haɗa hannun hakan ba shi da wata illa? Ni na san cutar shi kawai za a yi kamar yadda aka saba ya kasa fahimta, ina Fahad yake da wani halin da zai iya haɗa hannu su gina asibiti da Deen? Don haka a matsayina na mahaifiyarsa ban amince ba wllh." Wannan karon ta fara ƙular da dad, fuska ɗaure ya ce, "Shi Fahad laifi ya yi maki ne ko kuwa baki ɗauke shi naki ba shi ya sa kike tunanin zai cuci Deen? Ina ce yanzu kika gama magana akan club kina cewa maimakon ya je ya buɗe a Kano Bash ya kula masa saboda yana harkar, shi baki tunanin zai iya cutar shi ba ko a samu matsala sai Fahad? Idan kin ce shi Bash yana harkar ƙwallo shima Fahad likitanci ne profession ɗinsa, kuma ba wanda ba zai iya cutar da shi ba a cikin su biyun, haka idan ma wani baren ya ɗauka ya saka a harkar babu tabbacin ba za a cuce shi ba, don haka gara ya kasance na jikinsa ne ko da ma za a cuce shi hakan zai iya zuwa da sauƙi, wanda bana ma tunani za a iya haɗa kai da Fahad a cuci Deen balle kuma a ce shi da kansa ne zai yi hakan, maganar hali kuma dama ba lalle percentage ɗin ya zama ɗaya ba, sai dai kowa a cikin su akwai 6angaren gudunmawar da zai bada da zata fi ta ɗaya, idan shi Deen ya fi hali shi kuma Fahad ya fi shi ilimi da experience a harkar lafiyan. Yakamata ki rinƙa yin tunani kafin ki yi magana, irin waɗannan maganganun da kike yi za su sa yaran ki su fahimci abun da bai kamata su fahimta ba, kawai ki yi mashi fatan alkhairi." Da alama dad ya kashe mata baki, wani kallo ta shiga bin shi da shi wanda ke bayyana ranta ya 6aci sosai da kalamansa, Leemarh kuwa ɗan murmushin jin daɗin taka mata burkin da dad ya yi mata ta shiga saki, shi dai Deen kansa na ƙasa, sam bai ji daɗin exchanging words din da suke yi da juna ba, wani shu'umin murmushin gefe mom ta saki tare da miƙewa tsaye, duk suka kai idanunsu kan ta, tana