← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 197

Sashe 170

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata da, "Fine." "Ina mom ɗin ki?" aunty ta tambaya bayan ta zauna a kusa da ita, saukowa ta yi daga kujeran ta ce bari ta je ta kira ta, tare suka dawo da sis Naja'atu ta nufo aunty tana faffaɗan murmushi, bayan ta zauna kusa da aunty ta ce, "Ƙawata an dawo." aunty ta amsa mata, "Baby dazun ta ce kin wuce kasuwa, ina tsaraba na?" aunty na dariya ta ce mata tana boot idan sun fita zata bata, kafin ta ce,"Babyn fa?" sis Naja'atu ta bata amsa da tana ɗaki ta je yin salla, "Har an gama gyaran jikin?" aunty ta tambaya, ta bata amsa da eh basu daɗe da gamawa ba, "Mu je ciki ke ma ki yi sallan ko." Sis ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa, aunty na murmushi ta ce mata tata ta riga ta kai, sis Naja'atu ta koma ta zauna jin abun da ta ce, hira suka shiga yi irin ta manyan abokai, bayan ɗan lokaci Salma ta shigo cikin falon ta zo kusa da aunty tana murmushi, aunty dake kallon ta ta kama hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita tana murmushi ta ce, "Ma sha Allah, gyaran jiki ya yi kyau, ji yadda face din ta ke wani glowing." Sis da itama take kallon Salma ta ce, "Ai skin dinta yana da kyau yana ɗaukar gyara sosai." aunty ta ɗaga kai, "Sai ma an yi na gobe za ki ga yadda skin ɗin nata zai ƙara sheƙi sosai, ban da kai za a gyara mata ne?" aunty ta ce oh ta manta har da shi fa, sis ta ce ai kawai wanke shi za ai ai setting ko don ta san ba a ƙona gashinta, aunty ta ce eh, "Ko za a turara mata shi?" sis ta tambaya, aunty ta yi wani murmushi ta ce, "Wannan sai Allah ya kaimu gyaran aure." Sis ta tambayi to shi wannan gyaran na miye ko haka nan, idon aunty akan Salma ta ce, "Na tarbar surukin mu ne." Sis ta ɗan wara ido sai kuma ta yi dariya ta ce, "Ma sha Allah, ki ce mu fara shiri mun kusa shan biki." aunty ta jinjina kai ta ce shiri sosai kuwa don biki mai sunan biki za su sha, "Ɗaga ina surukin namu zai zo ne?" Aunty ta bata amsa da Abuja, jinjina kai sis ta yi cike da zolaya ta ce Allah Ya sa babban kifi ne ta kamo masu, aunty ta saka dariya ta ce ƙundumeme ma kuwa, Salma ta 6oye fuska a jikin aunty, sis na dariya ta ce, "Su Kubra girma ya zo, da an yi auren nan da ɗan lokaci zaki gan ki da jika." Aunty da itama ke dariya ta ce, "Bari ƙawata, ai rayuwan nan na gudu ba kaɗan ba, wai baby ce har ta isa aure." Sis Naja'atu ta ce, "Ai abun sai dai addu'a kawai Allah Ya sa mu dace. Allah Ya sa ana yin auren 9 months mu samu jikoki twins kin ga sai a baki raino." aunty ta juya tana kallon Salma da ta rufe fuska a jikinta ta ce, "Baby zaki bani?" Miƙewa Salma ta yi zata ruga ɗaki, aunty ta ɗaga murya tana ce mata ina zata je tafiya za su yi, hakan ya sa Salma nufar ƙofar fita suka bita da kallo suna dariya. Bayan sun koma gida, tun a daren aunty ta fara yin wasu ayyukan abincin tarbar Deen, washe gari cikin sa'a off take, bayan sun gama yin breakfast ta ɗauki Salma ta kaita gidan sis Naja'atu don a ƙarasa yi mata gyaran jikin, har da lalle za a yi mata dama akwai mai yi nan kusa da gidan sis ɗin idan aka zo gyaran jiki wurin sis ana son lalle ita take kira ta yi. Bayan aunty ta kai Salma kai tsaye cikin gari ta wuce don akwai abubuwan da take son siyo ma Salma, daga can gida ta dawo ta ci gaba da yin ayyuka, sai yamma taje ta ɗauko Salma, idan ka ganta sai ka ce wata amarya, fuskarta sai wani sheƙi take ga wani ƙamshi mai daɗi da jikinta ke saki, a hannuwanta an yi mata jan zanen lalle mai kyau ba mai hayaniya ba, sumarta an gyara mata daga gaban kanta ta kwanta luff luff. Da daddare aunty sai da ta kammala duk wani abu da zata iya yi na abinci kafin gobe. Washe gari tun ana gama sallan asuba aunty ta fito ta fara gyaran falo, har labulaye ta canza ta saka wasu tsadaddu masu kyau, da yake dama ita irin matan nan marasa son jiki, duk da tana da ɗan jiki amman hakan bai hanata kazar kazar, bayan ta share falon ta goge komai na falon su windows, kayan kallo, frames, har da kujeru ta goggoge, sannan kuma ta yi mopping tiles, lokacin da Salma ta fito sosai ta yi mamakin ganin yadda falon ya sha uban gyara ya yi kyau ko ina nata ƙyalli, bayan ta yi ma aunty sannu ta ce ai da ta kira ta ta taya ta, koda ta ce zata haɗa masu breakfast farko hana ta aunty ta yi, sai da ta takura sannan ta barta ta ce amman kada ta yi amfani da ruwa sosai don kada lallen ta ya zube.... Bayan sun gama yin breakfast a nan falo suka zauna, aunty ta ce ma Salma sun yi magana da Deen ne ya faɗi mata lokacin da zai zo ta ce mata a'a tun da suka yi waya ya ce zai zo basu sake yin magana ba, aunty ta ce ai yakamata ta kira shi da nufin yi mashi ya hanya, Salma ta ce to tare da ɗaukar wayarta ta kira Deen gabanta har ɗan faɗuwa yake, har kiran ya yanke bai ɗaga ba, aunty ta ce ƙilan yana hanya duk da ta san idan ma a mota zai zo ba lalle shine zai driving ba, after few seconds sai gashi ya kira, a nutse Salma ta ɗauka ta gaishe shi, ta ce dama ta kira ne don ta yi masa ya hanya, bayan ya yi mata magana ta furta ok daga haka suka gama wayan, aunty da ke kallon ta ta ce, "Wai baby haka kike yin waya da shi sai ka ce har yanzu ba wani abu a tsakanin ku?" Salma da ke kallon aunty ta yi murmushi kawai, "Kina waya da shi kamar mai jin tsoro, ba zaki saki jiki ki yi mashi magana yadda ake ma masoyi ba." Salma ta yi dariya tare da sunne kai, aunty ta ci gaba, "Ba wai ina nufin ki zaƙe ba, amman yakamata yadda kike waya da shi da ya bambanta da yanzu." Tambayarta ta yi ya suka yi, Salma ta sanar mata ya ce ta yi expecting nashi after asr, aunty ta ce yauwa zuwa lokacin an gama komai, nan ta shiga koya ma Salma yadda zata rinƙa magana da shi, daga baya ta ɗauki wayarta ta kira wani Isyaku wanda wani matashin saurayi ne a nan unguwar, shi take aike ko ta saka shi ya yi mata wani aiki, magana suka yi ta ce idan yana nan ya zo tana son ganin shi, ba a jima ba sai gashi don bai wasa da kiran aunty Kubra saboda yana samun alkhairi daga wurinta, aunty ta ce mashi compound ɗin gidan take son ya share mata ya ce to, ita kuma ta wuce kitchen don ta ƙarasa harhaɗa abincin tarbar Deen. Lokacin zuwan Deen na matsowa yayin da zullumi ke ƙara cika Salma, duk yadda take jin farin cikin zuwan nashi da ta tuna da batun Basma sai jikinta ya yi sanyi...wajen ƙarfe ukku aunty ta gama komai har falon ta ƙara gyarawa ƙamshin turaren wuta mai daɗi ya karaɗe ko ina na gidan. Ana gama sallan la'asar aunty ta shigo cikin ɗakin Salma tana riƙe da wani ƙaton jaka mai tambari a jiki, Salma da ke zaune ta gama yin salla ta juya tana kallon aunty, "Baby kin gama sallan?" Ta ɗaga mata kai alamar eh, "To taso." Ta faɗa tana nufar dressing mirror, sawa ta yi Salma ta cire hijab ɗin jikinta ta ce ta zauna a saman stool ɗin gaban mirror, makeup aunty ta shiga yi mata ta ƙara gyara mata gashi, ba ƙaramin kyau Salma ta yi ba duk da ba wata kwalliya mai yawa aunty ta yi mata ba ɗan light makeup ne amman sosai ta yi kyau, jakan da ta shigo da ita ta buɗe ta fiddo wasu kaya da aka yi packaging nasu, buɗe ledan da suke ciki ta yi ta fiddo kayan nan da nan ƙamshin da kayan ke yi ya baza wurin , Salma tai ta kallon tamfatsetsiyan applique atamfan da aka rubuta farashin kayan a jikin ledan har naira 250k, sosai jikinta ya yi sanyi, ita dai bata san wani irin so aunty Kubra ke yi mata ba, warware kayan aunty ta yi wanda doguwar riga ce, ba wani kwalliya daban aka saka ma ɗinkin ba, da kwalliyan atamfan aka yi amfani amman fa ɗinkin ya tsaru ba ƙarya, dama Kaduna kankat ne wurin iya tsara ɗinki, aunty ta miƙa ma Salma rigan da ta yi zuru don farashin kayan ya girgiza ta ta ce ta saka, bayan ta gama sakawa sosai rigan ta amshi jikinta kuma ta yi mata daidai, aunty ta yi mata ɗaurin kallabi mai kyau, sarka da yan kunnenta na zinari ta saka ma Salma don ita iya ƴan kunne da zoben zinari kawai gare ta, wata hadaddiyar agogo ta ɗaura mata ta sa Salma ta ɗauko zobunanta guda biyu na zinari ta saka, aunty ta riƙe ƙugu tana kallon Salma ta ce, "Wow...Ka ga zakanyan zakin wasannin ƙasan hausa...." Salma ta saka dariya jin maganan aunty, "Ma sha Allah, baby kin gan ki kuwa, ni na san ta ko ina na gama yin dacen ɗiya wllh...." Salma ta kasa magana sai dariya take tana kallon kanta a cikin madubi, ita kanta ta ga kyaun da ta yi sosai,
Chapter 170 · 0% Book details