Sashe 162
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar da duniya ke dakon jira ta zo. A yau, ƙasashe biyu wato Nigeria da Netherlands ne suka tsayawa juna a wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya, duniya ta tsaya cak, gaba ɗaya hankali ya dawo birnin NEOM in da a nan za a fafata a wannan dare, babban filin da za a yi wasan ya yi kama da abin da aka ƙirƙira a mafarki saboda haɗuwar sa, a cikin filin musulmai har da ƴan wasan suka gabatar da sallar isha da raka'a biyu ta nafila don roƙon sa'ar kammala wasan lafiya, bayan gama yin salla aka shiga shirye shiryen fara wasan, su Deen da abokan karawar su sun tsaya a layin gaba, duk suna sanye da jerseys na team ɗin ƙasar su, a damtsen hannun Deen ya saka armband launin green da babbar farar C da ke nuna shine captain a tawagar ta su, yayin da sumar kansa ke dauke da manyan kitso, sosai ya yi kyau idan ba ka san game da asalinsa ba da wuya a yarda shi ɗan Nigeria ne, hannuwan kowannan su na a ƙirji yayin da aka fara rera taken Nigeria.....wasan ya fara da ƙarfi, kowanne 6angare yana buga ƙwallon da ƙarfin zuciya, mutane na kallon Netherlands na da dabaru yayin da Najeriya ke da zafi, da gaske Deen ke buga wasan da duk wata ƙwarewarsa...iya bakin ƙoƙarinsa yake yi wurin ganin sun ci da kuma hana abokan karawar tasu zura ƙwallo....gaba ɗaya ya zama tauraro da ake ji da shi, hargowar magoya baya da masu sharhi ta cika filin, ko ta ina sunan Deen Jr ke tashi....gaba ɗaya yan wasa sun jigata, kowannen su ya jiƙe da zufa, duk da ƙarfafa gwiwa da canjin ƴan wasa a haka har aka tafi hutun rabin lokaci ba wanda ya yi nasarar zura ƙwallo a raga...A Nigeria ko ina ya yi tsit, kallo ya koma kusan ko wane gida, haka gidajen kallo sun cika maƙil da jama'a kowa yana jira ya ga yadda zata kaya, su Sageer ƴan gani kashe nin Deen ana gidan kallon kwallo an kasa an tsare anata addu'ar samun nasara....A Kaduna ma Salma tare da Aunty Kubra suna zaune a falo suna kallon wasan....Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, wasan ya ci gaba da zafi fiye da baya, al'umma sun cika da fargabar su wa za su samu nasara, fili ya cika da waƙe waƙen ƙarfafa gwiwa daga magoya baya anata ɗaga tutocin ƙasashen biyu, cikin sa'a Netherlands ta samu zura ƙwallo a ragar Nijeriya, sai dai bayan wasu ƴan mintuna Deen ya rama ma Nigeria sakamako ya kama 1-1, hakan kuma ya ƙara jefa mutane cikin tsananin fargaba da zullumi ganin lokaci nata tafiya....Salon wasa ya canza, kowane 6angare da zafin nama yake buga wasan, filin NEOM ya cika da sautin ƙwallon da a ke bugawa, hayaniyar magoya baya ta cika sararin samaniya.....hajiyar Ambasada ta kai hannu ta dafa kujera tana ƙoƙarin miƙewa, Balaraba dake zaune suna kallon ƙwallon tare a falo ta ɗaga kai ta kalle ta, ganin zata bar falon cikin girmamawa ta ce, "Hajiya baza ki ƙarasa kallo ba?" hajiya ta ɗan girgiza kai fuskarta a jagule ta ce, "Ba zan iya ma fargabar nan ba Balaraba, kin ji yadda ƙirjina ke faɗuwa, ƙilan shiyasa ma ake cewa kwallo bata da kyau saboda yadda take tada hankali...kuma babu kyau tada hankalin musulmi ...ina jin ma sai na kai ga shan magani, don da ƙyar in ba jinin nawa ya hau ba, na samu kwana biyu ya daidaita.." Har sai da Balaraba ta ɗan yi murmushi jin maganganun hajiya da ta nufi hanyar ɗakinta tana faɗin Allah Ya ba masu rabo sa'a.
Lokacin da ya rage saura mintuna goma kacal a wasan ƙarshe, Deen ya karɓi ƙwallo daga gefen hagu, ya ƙetare ƴan baya biyu, yana nufar ragar Netherlands cike da zafin nama, amma kafin ya kai tauraron dutch team ɗin ya shiga da ƙarfi ƙafafunsu suka yi wata irin haɗuwa, nan take ƙwallon ta watse, Deen ya faɗi ƙasa da ƙarfi ɗayan ɗan wasan ya faɗa saman shi, shiru ya mamaye filin, komai ya tsaya cak, babu ƙwallo, babu kaɗe kaɗe, babu hargowar magoya baya, Deen na kwance a ƙasa ya dafe kansa da hannunsa yayin da idanunsa ke rufe, kamar duniya ta tsaya cak, nan take referee ya dakatar da wasan, a cikin kujeru magoya bayan Najeriya duk suka mimmiƙe wasu sun dafe kai da hannayen su yayin da wasu har sun fara hawaye suna kiran sunan Allah, nan da nan aka zagaye Deen likitoci suka shigo filin da gudu suka fara duba shi. Ƴan mintunan da suka ɗauka suna duba shi a wurin mutane tamkar sa'o'i ne...gaba ɗaya duniya ta ƙosa da son sanin halin da yake ciki, ganin an shigo da stretcher cikin filin wato irin abun ɗaukar mara lafiya hakan ba ƙaramin tsinka zuciyar mutane ya yi ba, aka fara tunanin ko ya haɗu da wani mummunan haɗari ne, lokaci guda magoya baya suka sare, a Najeriya halin da Deen ya shiga ba ƙaramin jefa mutane cikin tsananin tashin hankali ya yi ba, mutane sai addu'ar Allah Ya sa ba wani mummunan abu ya same shi ba, su Leemarh da ke cikin ƴan kwallo tuni sun fara kuka, ita mom da karfin hali ma cikin filin ta fara ƙokarin zata je amman su dad suka hana ta....Salma da tashin hankali ya bayyana a fuskarta, har bata san lokacin da ta ɗaura hannu a saman kai ba tana faɗin, "Innalillahi...wayyo ya Deen, Allah Ya sa dai ba wani mummunan abu ya same shi ba..." Aunty Kubra da itama hankalinta ya tashi tana kallon ta ta ce, "In sha Allahu ba abun da ya same shi." Balaraba da ta ci gaba da yin kallon ita kaɗai, itama ba ƙaramin tashin hankalin ganin abun da ya samu Deen ta shiga ba, a ranta take ayyana gara ma da hajiya bata nan hakan ta faru, ta san da ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba...kowa dai ya shiga tashin hankali da zullumi. Ana ƙoƙarin ɗaukar Deen ya fara motsi, a hankali idanunsa suka buɗe, kokarin tashi ya fara yi amma likitoci suka hana shi saboda ba ƙaramar buguwa ya yi ba a kai, hannunsa guda na dafe da kansa yayin da ya miƙar da ɗayan hannun sama yana nuna alamar yana nan...nan take filin ya fashe da ihu, farin ciki ya bayyana a saman fuskokin mutane, cikin ƙaraji wasu cikin magoya bayan Nigeria larabawa suka shiga faɗin, "_Deen for life_..." aikuwa sai duk mutane aka ɗauka ana faɗin hakan, hada masu tsalle da yin rawa, farin cikin ba a iya filin ya tsaya ba, har da masu kallo na waje...cikin tsananin farin ciki Salma ta faɗa jikin aunty Kubra da itama ke ta sakin faffaɗan murmushi, a gidan kallon ƙwallo da su Sageer suke nan ma ihunsu ne ya karaɗe wurin kamar za su fasa bangon wurin, suma suka shiga fadin abun da magoya baya na cikin tv ke faɗi wato Deen for life. Likitoci sun yi ƙoƙarin hana Deen ci gaba da buga wasan, a cewar su yana buƙatar ya huta, amman Deen ya dage akan zai iya dole aka barshi, wasan ya ci gaba bayan referee ya ƙara mintuna goma matsayin injury time, kana ganin Deen kan san ƙarfin hali yake yana buga wasan don karsashinsa ya ragu ba kamar a baya ba, yana buga wasan wani lokacin yana kai hannu kansa, a haka dai har lokaci ya cika ba wanda ya ƙara ci, hakan ya sa aka ƙara extra time na mintuna talatin...haka dai aka ci gaba da fafatawa mai cike da ƙalubale da zullumi....sai da ya rage bai fi saura mintuna ukku ba lokacin da aka ƙara ya ƙare Netherlands ta samu bugun gefe, ƙwallo ta biyo iska ta shige ragar Nigeria, nan take shiru ya mamaye filin na ɗan lokaci, kafin allon sakamako ya nuna 2-1 daidai nan kuma lokaci ya cika, muryar stadium announcer ta karaɗe ilahirin filin da faɗin, "_Ladies and gentlemen, the moment you’ve all been waiting for… After an intense battle on the pitch, the winner of this edition of the World Cup is… the Netherlands! Congratulations to the Dutch team on their incredible victory....!_" Ihun magoya baya ya cika wajen, ƴan wasan Netherlands suka cika da tsananin farin cikin samun rabon da suka daɗe suna jira, yayin da ƴan wasan Nijeriya suka yi tsaitsaye, wasu suna ɗan murmushi wasu kuma sun ɗaura hannuwa a saman kai, Deen ya duƙe a ƙasa tare da saka hannuwansa ya rufe fuskarsa, ƴan'uwansa ƴan wasa suka ƙaraso wurin shi suma duk suka duƙa tare da kai hannu suka cire hannuwansa da ya rufe fuska, hawaye haɗi da kuma murmushi ne suka bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, suma duk suka shiga sakin murmushi tare da haɗe kawunan su, koda ba su suka yi nasara ba sun san cewa sun ɗaga Najeriya sama, sun kaita wani mataki da bata ta6a kaiwa ba a tarihin ƙwallo, sun san hakan ma babbar nasara ce, kuma kasancewar Morocco ta ukku hakan ma abun alfaharin Africa ne na kaiwa wani mataki da nahiyar bata ta6a kaiwa ba a tarihi. Bayan kammala gasar aka shiga gudanar da closing ceremony, shagali ne mai tsuma zuciya da saka wanda ba ya a wurin jin tamkar ya yi tsuntsuwa ya gansa a wurin....Bayan da aka bada trophy da gold medals ga ƴan wasan da suka zo na ɗaya, Netherlands ta ɗaga shi, amma Nigeria ce ta ɗauki zuciyar duniya, su Deen da suka zo 2nd place suma aka saka masu silver medals a wuya, Marocco da suka zo 3rd place aka saka masu bronze medals, bayan medal Deen kuma ya samu kyautar Golden Ball, wato kyautar da ake bayarwa ga wanda ya kasance mashahurin ɗan wasa na gasar, haka kuma ya samu yabo da jinjina daga manyan mutane da shugabbanin ƙasashen duniya wanda suka hallaci wasan ƙarshen, ciki har da shugaban ƙasan Nigeria wanda shima ya je kallon final ɗin tare da wasu muƙarrabansa, ana ta gaisawa da Deen wasu suna rungumarsa, crown prince na nan Saudiyya har da wata haɗaɗɗar alkyabba ya saka mashi tare da rumgume shi, sai suka yi kaman jinsi ɗaya.....