Sashe 156
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba ɗaya hankalin duniya na kan gasar kwallon ƙafa ta cin kofin duniya wato FIFA world cup da ke gabatowa nan da ƴan watanni, wanda a wannan karon ƙasar Saudiyya ce ta ɗauki nauyin shirya gasar. Kasantuwar Deen zai wakilci Nijeriya a gasar hakan ya ƙara saka shi ya zama busy sosai, saboda suna cikin buga Premier League ga kuma wasu daga cikin qualifiers da zai buga ma Nijeriya wato wasannin neman cancanta a gasar cin kofin duniya a lokuttan international break, yanzu gaba ɗaya Salma bata samun lokacinsa, ko ta yi masa saƙo ba ya responding, dama yawanci saƙon gaisuwa ne, sanin cewa zai buga ma Najeriya a gasan world cup ya sa ta yi tunanin shiyasa bai da lokaci, hakan ya sa gaba ɗaya ma ta daina tura masa kowane saƙo, dama yanzu komai na aikin da take masa ya koma hannun Sageer tun da ita bata nan, shima Sagir ɗin ba samun lokacin Deen ɗin yake ba, iyaka dai duk abun da ya shafi aikin abincin da ake yi da har yanzu ana bama mutane hajiyar ambasada ake tuntu6a ita take bada komai. Ranar Juma'a lokacin satin Maleek ɗaya daidai da yin tafiya ya dawo, cike da farin ciki iyalin nasa suka tarbe shi, duk sun sha ado da kayan mu na gida, Sapna ta saka doguwar rigar wani rantsattsen jan leshi da ya bala'in ƙara mata kyau, itama Basma riga da skirt na lace ne a jikinta, su duka ba ƙaramin kyau suka yi a cikin kayan ba, shima Maleek ya nuna farin cikin ganinsu sosai, bayan gama tarbar sa a tare suka zauna cin abinci wanda har da Sapna aka yi aikin girka abinciccikan musamman saboda dawowar tasa. Bayan gama cin abincin part ɗin shi ya wuce tare da Sapna ta taimaka masa ya yi wanka ya kwanta ya huta. Da daddare bayan sallar issha Maleek ya fito daga part ɗin sa jikinsa sanye da farar jallabiya, a bakin bene ya tsaya tare da ɗaura duka hannuwansa ya dafa saman ƙarfen benen da ya zagaye sama, shiru ya yi yana kallon gabansa kana gani ka san tunani yake yi, he stood there for a while his mind elsewhere, can ya ɗan sauke gajerar ajiyar zuciya ya juya, walking slowly ya nufi hanyar part ɗin Basma, bayan ya isa hannu ya kai zai buɗe ƙofar sai kuma ya fasa, knocking ya ɗan yi kusan sau biyu sannan ya tura, Basma dake zaune a saman gado tana latsa wayarta ganin dad ɗinta ne ya sa ta yin saurin gyara zaman ta tare da ajiye wayan, ciki ya nufo ya tsaya ɗan nesa da ita yana kallon ta kamar yadda itama idonta na akan sa, a hankali ta ce, "Dad..." Kai ya ɗaga mata kawai, "Kin yi salla?" Da sauri ta jinjina masa kai alamar eh, shiru ya ɗan yi kafin ya ce, "Is there any problem?" Da sauri ta girgiza maza kai, ya ce, "Ya hutun?" Ɗan murmushi ta yi ta ce lafiya lau, daga haka bai sake ce mata komai ba, a fakaice Maleek ya kai idanunsa yana ɗan kallon wani direction a cikin ɗakin, can ya juya ya kalle ta tare da miƙa mata hannu ya ce ya ga wayarta, Basma ta ɗauka ta miƙa masa, kallo ta bishi da shi yayin da yake tatta6a wayar tata, bayan ɗan lokaci ya miƙa mata, ci gaba da bin sa da kallo ta yi ganin ya yi tsaye kuma bai sake cewa komai ba, can a hankali ya ce mata, "Gud night." itama ta ce masa haka ta bi shi da ido yayin da yake nufar ƙofa har ya fita. Bayan Maleek ya koma part ɗin sa, reading nook dake a cikin babban falon nasa ya nufa ya zauna, bin wata laptop da ke ajiye asaman teburi ya yi da kallo, kana kallon sa zaka fahimci yana zullumin yin wani abu, ya ɗan ɗauki lokaci a haka sosai yake jin fargabar aiwatar da abun da yake niyya, bai so ya ga wani abu da zai zo yai unsettle nasa duk da baya fatan ya ga abu haka, can ya dake ya kai hannu ya buɗe laptop ɗin, daddanata ya shiga yi bayan ya kunna, juyawa ya yi jin motsi, Sapna ce ta shigo cikin falon jikinta sanye da wata haɗaɗɗan doguwar rigar bacci data bi jikinta ta fito da shape ɗinta sosai, bin ta da kallo Maleek ya yi yayin da take ƙarasowa wurin da yake, lokaci guda wurin ya karaɗe da ƙamshin turarenta mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciya, har Maleek bai san lokacin da ya lumshe idanunsa ba, hannu ya miƙa mata tana sakar masa lallausan murmushi ta kama, a saman cinyoyinsa ya yi mata masauki ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannu ya kai cikin dogon sumarta da ta ɗaure ta a baya ba tare data rufe kan nata ba, ta sigar soyayya ya shiga yamutsa gashin nata da shima ya sha gyara yana ta sakin ƙamshi, ɗago ta ya yi tare da tura fuskarsa a tsakankanin wuyanta yana shaƙar ƙamshin da wurin ke saki, can ƙasan maƙoshi ya furta, "My love kin yi kyau..." Tana murmushi idanunta a lumshe a hankali ta furta, "Kai ma haka." Ɗago fuskarsa ya yi idanunsa a ɗan lumshe ya ce, "Wani kyau da wannan jallabiyan da kika saba ganina a cikin shi." Ƴar dariya ta yi bata ce komai ba, yanata bin ta da kallo don sosai ta yi mashi kyau duk da koda yaushe haka take yi masa kyau, "Mi yasa ne ke sam bakya tsufa?" Ta ɗan buɗa ido ta ce, "Tsufa kam ai na fara ɗaukar hanya tun da na wuce 40." Ɗan girgiza kansa ya yi ya ce, "Serious sam bakya tsufa Sapna, ba wanda zai gan ki ya ce ke kika haifi baby idan ba wanda ya sani ba, koda yaushe kina nan a yadda kike sai dai jikin ki kawai ya ɗan canza, kuma wannan ƙara maki kyau yake, kuma ba iya jiki ba still, like...." Shiru ya yi bai ƙarasa ba Sapna ta ɗage masa gira, kai bakinsa ya yi saitin kunnanta ya raɗa mata magana, dariya ta yi ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, "Allah da gaske my love, har yanzu ina mamakin hakan, sai kuma in yi tunanin wataƙila wani siddabarun ne naku na likitoci kika yi shiyasa hakan." Ɗaga ido ta yi ta kalle shi kafin ta sauke ta bi wuri guda da kallo, jin ta yi shiru ya leƙo fuskarta suka haɗa ido, ɗage mata gira ya yi ya ce haka ne ko, ɗan murmushi ta yi ta ce wannan sirrinta ne, ya yi murmushi tare da kai hannu ya ɗan ja dogon hancin ta, ɗagowa ta yi daga jikinsa ta tambaye shi ko aiki ya ke ta bashi space, ya ce sai ka ce wani injin ya dawo daga tafiyar aiki yau kuma ya dasa wani aikin ai suma yakamata su samu lokacin sa kawai ya duba abu ne, hannu ta kai tana shafa gashin gefen fuskar shi ta ce, "Baka bani labarin trip ɗin naka ba." Ya ce ok bari su je bedroom ya bata, daga haka suka miƙe ya duƙa gabanta kamar yadda yake mata idan zai ɗauke ta, hayewa bayan nashi ta yi tana ƴar dariya, daga haka suka nufi bedroom ɗin sa ta kwantar da kanta jikinsa, tare da lumshe idanunta tana jin tsananin ƙaunar mijin nata na ƙara ratsa zuciyarta. Washe gari bayan sun gama yin breakfast Maleek ya koma part ɗin sa ya kwanta don ya ƙara hutawa, sai lokacin salar azahar ya farka daga bacci, bathroom ya shiga ya yi wanka bayan ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya daga haka ya fita zuwa masallaci, ana gama sallan ya dawo gida kai tsaye part ɗinsa ya wuce, duk da fargabar da yake ji haka ya nufi reading nook ɗin ya zauna tare da buɗe laptop ɗin, ƙirjinsa ya shiga faɗuwa with every click, lokacin da zai buɗe abun da yake son dubawa har sai da ya ɗan runtse idanunsa, after gathering all the courage he had ya buɗe idanunsa tare da buɗewa, yadda ƙirjinsa ke ɗagawa a fili zaka fahimci ba ƙaramin tashin hankali yake a ciki ba, bayan ɗan lokaci ya wani zaro idanu tamkar idanun nashi za su faɗo ƙasa, kan ka ce mi jikinsa ya fara yin kakkarwa kamar wanda shock ɗin lantarki yake ja, da sauri hannunsa na rawa ya yi saurin kife laptop ɗin ya rufe ta, kaf, kaf, haka hannunsa da ke dafe da jikin system ɗin ke ta rawa, da ƙyar yake fitar da numfashi yayin da bakin sa ke ɗan rawa ya runtse idanunsa gam, a cikin ransa ba abun da yake maimatawa face "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun...." Ya ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka kafin ya buɗe idanunsa da har sun yi ja sosai, miƙewa ya yi a fusace ya nufi cikin bedroom ɗinsa, bada jimawa ba ya fito hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa, kai tsaye hanyar ɗakin Basma ya nufi idanunsa har rufewa suke yana haɗe hanya, yana isa ya kai hannu ya banka ƙofar ya shiga, a fusace ya furta, "Basma..!!!" Basma da ta miƙe daga gaban dressing mirror ta gama yin shafa tana tsaye bakin closet zata fiddo kayan da zata saka, da sauri ta kai idanunta kan dad ɗinta da ya shigo cikin ɗakin yana mata kiran da ta na ji ta san ba lafiya ba, sakin kayan da ta fiddo ta yi suka faɗi ƙasa ta fara ja da baya ganin yadda ya tunkaro ta, a ruɗe ta buɗe baki ta ce, "Dad...what's happ..." Kafin ta ƙarasa ta ji saukar waya a jikinta, wata gigitacciyar ƙara Basma ta saki yayin da raɗaɗin bugun ya ratsa ta, cikin fitar hayyaci Maleek ya ci gaba da zuba mata wayar ta ko ina, ihu kawai Basma ke saki jin azababben raɗaɗin da bata taba fuskanta ba a rayuwarta, gashi sam ya ƙi bata sararin da zata gudu, da ta yi yunƙurin guduwa ya ke fizgo ta ya hankaɗa ta, towel ɗin jikinta har kwancewa yake Allah ma ya sa ta riga ta saka underwear, da ƙyar Basma ta samu ta kubce masa ta fito daga cikin ɗakin, hanyar sauka ƙasa ta nufo da guda hannuwanta