Sashe 109
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari kasantuwar ranar lahadi ne ba aiki, gaba ɗaya iyalin gidan bayan sun gama yin breakfast suka nufi backyard sports field ɗin gidan kowa yana sanye da kayan wasa, wasanni iri-iri suka yi cike da nishaɗi har da dad ɗinsu, mom ɗin su ce kawai bata wani saki jiki ta yi annushuwa ba, ba don komai ba sai don Fahad da ya kasance a wurin, wasanni irin su basketball, volleyball, badminton har da favourite wasan dad wato golb suka yi, gaba ɗaya duk Deen ya iya su sosai har shima Fahad, su Leemarh ma duk sun iya kasantuwar dama suna yi sun ƙware, ba ƙaramin kyau suka yi a cikin kayan wasannin ba, ba kamar Leemarh da ta saka jajayen tracksuit kanta ta saka jar sun cap irin hula mai kaman face cap mai buɗaɗɗan sama ta yadda gashinta ya bayyana ta ƙulle shi a baya, idan ka ganta zaka yi tunanin hausa bazata fito a bakinta ba, abun da ya ƙara ƙular da mom ɗinsu a wurin shine ganin yadda Leemarh da Fahad suke ɗaga ma junansu suna yin nasara, bayan wani lokaci dad ya sa chef Alima da sauran ƴan aiki da suna a wurin suna kallon wasannin aka kawo abubuwan ci da sha, sai bayan da lokacin sallar azahar ya gabato sannan suka tashi daga wasannin kowa yana cike da nishaɗi da annashuwa idan ka cire mom. Ko da suka zauna cin abincin rana bata zauna cikin su ba duk don saboda Fahad. Da daddare wuraren ƙarfe tara gaba ɗaya ahalin gidan suka rako Deen airport, Deen na tsaye sanye da jeans da T-shirt kan sa ya saka face cap, dad na kallonsa da murmushi ya ce, "Son, sai kuma yaushe za mu ƙara saka ran ganin ka anan ƙasar?" Deen na murmushi ya ce masa in sha Allah zai zo da ya samu lokaci, "Ya Deen pls kada ka ƙara daɗewa baka zo ba." Leemarh ta faɗa da sigar shagwaba ya ɗaga mata kai, kallon mom da ke sanye da abaya ruwan ƙasa mai shegen kyau ya yi yana murmushi ya ce, "Mom, I'm leaving, sai na ƙara zuwa." Itama murmushi ne akan fuskarta ta ce, "Allah Ya tsare hanya Ya ƙara kare mana kai, ka gaida su Sapnah." Ya amsa mata, kallon Fahad ya yi suka sakar ma juna murmushi ya miƙa masa hannu suka yi musabaha ya ce, "Ya Fahad sai wani lokaci." Fahad ya ce, "Ok, Allah Ya tsare sai mun yi magana." Kallon Omar ya yi ya ce masa sai ya shigo Cyprus ya amsa masa da ok tare da yi masa addu'ar Allah Ya tsare, daga haka ya saki hannun Sultan da Batool da yake riƙe da, Leemarh ta rumgume shi tana jin har ta fara kewar ɗan'uwan nata saboda ko zuwa suka yi London ba wani samun isasshen lokaci suke yi da shi ba in dai ba a lokacin hutun shi bane, bayan ya saki Leemarh ya nufi mom ɗinsa itama suka rungume juna, haka duk sai da suka rungume juna da mutanen wurin kafin ya nufi jirgin ƙungiyarsu da tuni ya hallara don ɗaukar sa har an shiga da kayan sa, suna ta kallon shi yayin da yake tunkarar jirgin cikin tafiyarsa mai cike da natsuwa, bayan ya kai matakalar ƙarshe ta shiga ciki ya juyo yana kallon su shi kan shi ya fara jin kewar su, ɗaga masu hannu ya yi a karon ƙarshe kafin ya juya ya shige, bayan ɗan lokaci ƙofar jirgin ta fara ɗagawa tana rufewa, akan idon su jirgin ya fara tafiya kan hanyar sa har ya tashi sama ƙoli ya tafi. Cike da jin kewar Deen suka nufi inda motocin su suke, dakatawa Fahad ya yi bayan sun ƙaraso idon shi akan dad da ke niyyar shiga mota ya yi mashi sallama cewa zai tafi, da yanayin mamaki dad ya ce, "Ba dai Funtua kake nufin zaka tafi ba a cikin daren nan? Kamar an kore ka son, mu je gida ka kwana idan Allah Ya kai mu ba sai ka yi asubanci ba in ma saboda aiki ne." Fahad na ɗan murmushi ya ce, "No daddy ba can zan tafi ba, akwai wani colleague ɗina a nan mun yi da shi zan je gidansa ne in kwana sai mu wuce Zaria da safe." Daddy ya jinjina kai alamar gamsuwa kafin ya ce, "Shi abokin aikin naka yana da iyali a nan ke nan?" Fahad ya ɗaga masa kai ya ce eh, "To kai sai yaushe zaka yi iyalin kai ma a rinƙa zuwa gidan ka?" Ɗan sunkuyar da kai Fahad ya yi yana dan murmushi ba tare da ya ce komai ba, mom ta shiga jifar sa da wani kallo mai kaman harara, daddy ya ce, "Yakamata dai ai niyya son, shekaru tafiya suke yi, kuma kana da aikin ka mai kyau to mi ake jira? Aure yana ƙara ma mutum natsuwa da kamala kuma shine cikar mutum. Ka ga shi ɗan'uwanka yana da mata da lokaci ya yi zai yi aure, amman kai ban ta6a jin an ce akwai wacce kake tare da ita ba da zaka aura, ko kuwa so kake mu yi maka auren dole?" Ɗagowa Fahad ya yi still da murmushi a nutse ya ce mashi in sha Allah zai yi, dad ya ce gara ya yi harama pls ko sun fara samun grandchildren, sosai kunya ta kama Fahad ya sunkuyar da kai ba tare da ya ce komai ba, sallama suka yi da sauran ƴan'uwan nasa har da mom da ta amsa a daƙile, Leemarh duk fuskarta ta nuna alamar rashin jin daɗi, ta so idan suka koma gida su yi hira da shi har ta bashi chocolates din da bata samu bashi ba jiya, bayan sun gama yin sallama da juna duk suka shiga cikin mota ban da Leemarh, matsawa ta yi gaban shi idanunta suka shiga cikin nasa, da alamun damuwa ta ce, "Yaya Fahad mi yasa baza ka koma gida ba sai ku haɗu da shi da safen?" Yana kallonta cikin ido ya ce mata sun riga sun gama magana da shi, ta ce ita dai bata ji daɗi ba da ba gidan su zai sake kwana ba, yanzu shima idan ya tafi sai an daɗe kafin su sake ganin shi, yadda ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka, calmly ya ce, "I'm sorry Leemarh, in sha Allah ba za a daɗe ba zan samu time in zo, hakan ya yi maki?" Ta ɗaga masa kai tana ɗan kikkafta idanu, tana niyyar sake yi mashi magana ta ji muryar mom ɗinsu a kausashe tana faɗin ita za su tsaya jira, sai da fa dad ya ce ta ƙyale su su gama magana amman ta ƙi bari, Fahad ya ce mata ta je sai su yi magana ta waya daga haka ta nufi mota ta shiga, sai da ya ga tafiyar su sannan shima ya shiga motar sa ya tafi, sai dai ba wani gidan abokinsa da zai je, kai tsaye daga nan hotel ya nufa, dama ya yanke Deen na tafiya kwanciyar hankalinsa kada ya koma gidan nan, hakan ya sa shi yanke zuwa hotel ya kama ɗaki. Bayan Fahad ya fito daga wanka a hotel room din da ya kama, shiryawa ya yi cikin kayan bacci ya buƙaci a kawo masa baƙin shayi kawai don sun ci abincin dare kafin su raka Deen airport, ba tare da bata lokaci ba aka yi knocking kofar dakin da yake ya mike ya je ya buɗe, black tea da ya buƙata ne aka kawo masa a cikin tea cup mai kyau saman saucer, daga gefe cokali ne a nade sai kuma sikari don ya sa yadda ransa ke so, amsa ya yi ya dawo ciki ya ɗaura a saman side drawer, abun ka da likita sai da ya je ya wanko cokalin duk da a naɗe yake kafin ya dawo ya yi amfani da shi, a nutse yake shan shayin yana kallon american movie a tv ɗin ɗakin, bayan ya gama ya wanko bakinsa ya dawo ya kashe kayan kallon, sai da ya kwanta sannan ya tuna da ya ce ma Leemarh za su yi magana, lokacin da kiransa ya shigo wayarta tana kwance a saman gado ta gama shirin kwanciya tana ta dakon kiran nasa har ta fara fidda ran zai kira, wani daɗi ta ji lokacin da kiran nasa ya shigo ta yi saurin miƙewa zaune kafin ta ɗaga, "Leemarh..." Ya kira sunanta jin ta yi shiru, a hankali ta ce, "Na'am ya Fahad." Ya sake cewa, "Ko har kin fara bacci?" Da sauri ta ce mashi a'a tana jira ne da ya ce za su yi magana, ya ce mata ok ta yi haƙuri ya ɗan shafa'a ne, ta ce, "Dama na yi tunanin haka da na ji shiru, kuma kamar in kira." Yana murmushi ya ce to mi ya sa bata kira ba, tana wasa da dogayen yatsunta ta ce, "Haka nan, kada in takura maka." Sigh ya yi ya ce, "Dama ɗan'uwa na takura ma ɗan'uwansa ne Leemarh?" Ta yi shiru tana murmushi, a hankali ta ce, "Yaushe zaka ƙara zuwa?" Ya ɗan yi shiru kafin ya ce mata zai sanar mata lokacin, tambayarta ya yi ba ta ce zata zo Funtua hutu ba ko ta fasa, ta ce, "Kana so in zo?" Ya bata amsa da sosai don an daɗe bata je ba, amsa ta bashi da zata zo suka ɗan yi shiru, can ta ce, "Yaya Fahad yaushe zaka yi auren? Na ji dad ɗazun ya yi maka magana ka ce masa zaka yi." Gyara kwanciyarsa ya yi yana murmushi ya ce mata bai san ya zai ce masa bane shine ya bashi amsar, "To ba zaka yi auren ba?" Ya ce, "No, zan yi in sha Allah, amman ba yanzu ba don bani da wadda zan auran." Muryata da alamun rashin yarda ta ce, "Kai yaya Fahad kai ne zaka ce baka da wadda zaka aura kuma na san ai kana da wanda kuke soyayya da su." Ya bata amsa da yin soyayya da mace ba shine ke nufin lalle ita ce mutum yake son aura ba, kuma shi bai ma 6ata lokacin shi kan hakan, ta ce, "Yanzu ke nan ba wadda kake son aura?" Ya yi