Sashe 187
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ƙara tabbatar mashi da ba zai auri Salma ba, idan kuma ya ga ya aure ta sai dai idan bayan ba ranta, kuma ko bayan ba ran nata ya aure ta bata yafe ba, har tana cewa idan ma wasu ne suke ɗaure masa g*ndi suke sa yake ganin zai auri yarinyar to ya sani a matsayinta na mahaifiyarsa ba zata ta6a amincewa ba, ta ƙara jaddada mashi kan komai kudin da yake da su a ƙarƙashin ikon su yake, dole ne kuma ya bi umarnin su matsayin su na iyayensa..shi dai Deen kansa na a ƙasa, kalma ɗaya kawai ya furta mata ita ce ta yi haƙuri, duk su Leemarh suna jin faɗan da mom ɗin ke yi masa don duk suna a falon sun fito tarbar shi, hatta dad yana zaune ya haɗe hannunwansa tare da ɗaura ha6arsa, fuska a kwa6e yake bin mom da kallo bai dai ce mata ƙala ba, kuma ya san gogar zananta kan suwa ta yi, itama mom ɗin tun da ta fara sababin nata bata kalle shi ba don ma kada ya ce zai taka mata burki...sosai Leemarh ta ji tausayin yayan nata ya kama ta, fuska a yamutse take bin mom da kallo, ita dama neutral ce bata ji tana so ko ƙin auren shi da Salma ba, kawai dai ta yi mamakin jin yana soyayya da kamar Salma...haka mom Jameela ta ƙaraci bala'en ta ta juya ta nufi barin falon ko ina na jikinta na amsawa sakamakon yadda take yin tafiyan a fusace, shiru ne ya mamaye wurin na ɗan lokaci, su Leemarh nata kallon yayan nasu da kansa ke a ƙasa, bayan ɗan lokaci dad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ɗaura idanunsa kan Deen, yama rasa mi zai ce masa, cikin kwantar da murya ya ce, "Allah Ya kyauta. Ka je ka samu ka huta ka sha hanya." Slowly Deen ya ɗago kai ya kalli mahaifinsa ba tare da ya ce komai ba, sai da Leemarh ta ƙara ce mashi, "Ya Deen ka je ka huta." Ya ɗan yi murmushin ƙarfin hali ya miƙe ya nufi stairs walking slowly, kana ganin yadda yake yin tafiya kasan jikinsa a sanyaye yake....bayan ya isa part ɗinsa, a edge ɗin gado ya zauna tare da dunƙule hannuwansa ya ɗaura forehead ɗinsa sama, idanunsa a rufe yayin da maganganun mom ke ta masa yawo, ya kasa gane taƙamaimai dalilinta na ƙin auren sa da Salma, idan don Basma ne itama ai ya ce zai aure ta, wani 6angare na zuciyarsa ya shiga raya masa wataƙila Basma kawai take son ya aura, ya raya hakan na nufin shi bai da ƴancin da zai so wata ke nan saboda Basma? gashi a koda yaushe jin son Salma yake na ƙaruwa a zuciyarsa..ya ɗauki ɗan lokaci a haka ba tare da ya san taƙamaimai tunanin da zai yi ba, miƙewa ya yi ya nufi toilet, after some minutes ya fito waist ɗinsa ɗaure da farin towel ƙar, da wani short a hannu yana goge sumarsa ya nufi closet, farar singlet da short ya sako ya dawo cikin ɗakin ya nufi gado ya kwanta, ya ɗage kansa saman pillow tare da lumshe idanunsa, tunanin Salma ya shiga yi don koda yana a hanya sun yi waya da ita, slowly ya buɗe idanunsa jin an dan yi knocking ƙofar ɗakin tare da buɗewa, Leemarh ce ta shigo idanunta akan shi ta nufo cikin ɗakin, daga gefen gadon ta tsaya fuskarta da alamun ƴar damuwa ta furta, "Ya Deen..." Yana ta kallon ta ya yi mata ɗan murmushi tare da yi mata alamun ta zauna da hannu, a bakin gadon ta zauna tana kallon shi, ya tambaye ta da wani matsala, ta ɗan girgiza masa kai ta yi shiru, can ta ce, "Pls ya Deen I'm sorry kan abun da mom ta yi maka, wllh ban ji daɗi ba." Ta ƙarasa maganar kaman zata yi kuka, shiru ya yi yana ta kallon ta kafin ya yunƙura ya tashi zaune tare da jingina da gadon, calmly ya ce, "Nagode....amman ke miye ne ra'ayin ki kan hakan?" Leemarh ta sauke idonta ta ɗan yi shiru, ɗagowa ta yi ta kalle shi ta ce, "Ni kawai ina son ka auri sis Basma don tana son ka sosai, ta shiga damuwa saboda wannan da kake so yanzu, ko jiya da muka yi magana da ita har kuka ta yi." Deen ya ɗan yi shiru, a hankali ya ce, "I will marry them both." Ta ɗan jinjina kai sai kuma ta ce, "Hakan ya yi, in dai kana son ita wannan ɗin nima ina goyon bayan ka aure ta." Deen yay sigh ya ce, "Yea, I love her so much...but mom bata amince in aure ta ba." Leemarh ta ɗan yamutsa fuska tace, "Ina ganin kaman saboda sis Basma ne, ka faɗa mata su duka zaka aura?" Deen ya ɗaga mata kai alamar eh, ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Ban san mi ya sa bata son ka aure ta ba duk da haka....is it because they are not rich ko kuma don tana a garin su dad?" Ta ƙare maganar da sigar tunani, Deen ya bita da kallo, sai da ta yi maganar sannan hankalinsa ya fara kaiwa ga tunanin tabbas zai wuya ba ɗaya daga cikin wannan dalilin da Leemarh ta faɗa bane yasa bata son ya auri Salma. Da daddare bayan sallan isha Deen ya shigo falon dad ɗinsa kamar yadda ya buƙaci ganinsa ta hanyar kiran sa a waya, dad dake zaune saman lafiyayyan kujeran falon ya ɗaga kai yana kallon shi har ya ƙarasa ciki, yana ƙoƙarin zama a saman carpet dad ya nuna masa kujera ya ce ga wuri nan ya zauna mana, bayan ya zauna ya kalli dad a nutse ya yi masa barka da dare, dad na murmushi ya amsa masa, gyara zama dad yay ya fara magana, "Dama dalilin kiran ka da na yi, ina son na tambaye ka ne game da ita yarinyar ta Funtua..." A hankali Deen ya sauke kansa, dad ya ci gaba, "Da gaske ka tabbata kana son ta da aure?" Deen ya yi shiru kuma bai ɗago ba, dad yana ɗan murmushi ya ce, "Kai nake sauraro son, kana jin kunya shine har da ɗaura ta a shafin ka, sannan ka je wurin hajiya ka bayyana mata tsakanin ka da ita har da maganar aure." Deen ya ɗan ɗago ya kalli Dad da ɗan murmushi, dad ya ɗage masa gira ya ce ya bashi amsar tambayar da ya yi mashi, slowly ya furta eh yana son ta da aure, dad ya jinjina kai ya ɗan yi shiru, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Shike nan, Allah Ya zaba mana abun da yake alkhairi. Ka kwantar da hankalin ka, in dai an yi bincike an tabbatar da ba wata matsala dangane da ita ni kana da goyon bayana akan auren ta. Yanzu jibin zaka koma can London ɗin?" Deen ya ce masa eh, "Hajiya ta ce nan da wata biyu ka ce kana son a ɗaura maku aure?" Deen ya ɗaga masa kai idonsa akan carpet, "To ita yar'uwar taka da ka ce duka zaka aure su, ke nan tare za a ɗaura maka auren da su lokaci guda ko kuwa ya ka shirya?" Deen ya ce mashi haka ya yanke shawara amman sai idan ya koma London zai yi magana da daddy Maleek, dad ya ce, "Ok, komi ke nan yadda kuka yi sai ka sanar mani, yanzu dai ka ce mu fara shirin shan biki kawai." Deen ya kalli dad yana murmushi, shima dad ɗin kallon sa yake yana murmushi, tausayin ɗan nasa yake ji har cikin ransa, ba kamar da hajiya ta faɗa masa cewa ashe Basma ba za6in ransa ba ce, kawai ya yi ma mahaifiyarsa biyayya ne ya amince da auren ta, hakan ne ya sa dad jin yana son goya masa baya akan wannan da yake so, "Amma...mom bata amince mani ba." Dad ya tsinkayi muryar Deen ya faɗi haka, kallon shi dad ya yi, daga yanayin fuskar ɗan nasa ya gane hakan na damun sa sosai, dad ya ɗan yi shiru kafin ya gyara zama ya ce, "Kada ka damu, zan yi ƙoƙarin shawo kanta in sha Allah." Deen ya jinjina kai feeling a bit relieved don ya san da yawan lokutta idan ta botsare akan abu dad ɗin na shawo kanta, bayan shiru na ɗan lokaci dad ya ce mashi idan ba wani abu shike nan zai iya tafiya, da alamun jin daɗi Deen ya ce, "Thank you so much dad for supporting me." dad ya yi ƴar dariya ya ce, "Kada ka damu, duk abun da kake so matuƙar bai sa6a shari'a ba kana da goyon bayana...kuma wannan kamar tarihi ne ke maimaita kansa, sai dai akwai in da bana son a kai" Dad ya ƙarasa yana dariya, Deen ya ɗaga kai yana kallon mahaifin nasa shima yana yin ƴar dariya don ya gane inda maganar tashi ta dosa, daga baya dad ya saka masa albarka suka yi sallama ya miƙe ya nufi hanyar fita idon dad akan sa, ɗage kai dad ya yi bayan Deen ya fita, maganganun da mom Jameela ta yi ɗazun na dawo masa, a ganinsa kalaman nata sun yi tsauri, kuma shi ya kasa gane wani irin son kai ne da ita, ta san ita ta matsa kan son ya auri Basma ya amince ba don son ransa ba sai don yi mata biyayya, yanzu ya zo ya nuna yana son wata amma firr ta ƙi ta amince masa, ai koda bata so yakamata ta amince masa don ta faranta masa rai kan biyayyar da ya yi mata, tunanin hanyar da zai bi don ya shawo kanta ya shiga yi, don dole akwai buƙatar amincewar ta matsayin ta na mahaifiyarsa ko don samun albarka a cikin al'amarin. Bayan kwana biyu Deen ya koma London, lokacin daddy Sa'ad ya yi duk wani bincike da ake yi da ya danganci neman aure, cikin sa'a ba a samu wata matsala da zata iya hana auren ba, sai ma yabo da shaida mai kyau da aka yi ma ahalin malam Bashir. Ba ƙaramin farin ciki iyalin suka shiga ba bayan da aka sanar da su zancen neman