← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 197

Sashe 132

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki tashi hankalin ki, kawai na yi tunanin hakan ya dace ne, idan ta kawo buƙatar kuɗi a rinƙa sanin mi zata yi da su kuma a tabbatar da abun da ta ce ɗin ta yi da su, zai fi ma a rinƙa siya mata duk abun da ta ce tana so zata siya kan a bata kuɗin, ko kuma a ɗauke ta akai ta ta siya, duk hakan a matsayin ƙara saka kula ne akan tarbiyarta musamman da ya kasance ita kaɗai Allah Ya ba mu." Shiru Sapna ta yi tana kallonsa yayin da wani 6angare na zuciyarta ke a cikin fargaba don sai take ganin kaman akwai wani abu da yake 6oye mata duba da bai ta6a kawo magana irin wannan ba, wani 6angare kuma na ganin zai yuwu ba da wani dalili bane kawai ya ga hakan ya dace ne kamar yadda ya ce, kuma ita kanta ba tun yanzu ba ta fahimci kashe kuɗin Basma yana yin yawa, shima Maleek shiru ya yi a ransa yana kokonton idan shawarar da ya bada ta ƙarshe zata zama mafita, yana ganin akwai buƙatar koda an siya mata abun da take so ɗin a tabbatar da ita ɗin ce zata yi amfani da abun, tabbas ya san a halin da ake ciki akwai buƙatar saka ido kan Basma daga wurin mahaifiyarta don ita ce ta fi kusanci da ita ta wasu 6angarorin, shi ba koda wane lokaci yake samun isasshen lokacin kasancewa da su ba, ban da aiki kuma yana yawan yin tafiye-tafiye, to idan shi kaɗai yake kula da ita a lokacin da baya nan hakan na iya bata dama, shirun da ya yi yasa Sapna bin sa da ido tana karantar yanayin sa, sam bata ji ta yarda da ba wani abu da yake boye mata ba, fuskantar sa ta yi sosai ta kama duka hannuwan sa cikin marairaicewa ta ce, "Honey pls ka sanar da ni abun da ke faruwa, na yi maka alƙawarin zan fahimta ba zan tada hankalina ba." A cikin ransa ya fara tunanin ta yadda zai bayyana mata ba tare da hankalinta ya tashi ba, dubara ce ta faɗo masa ya daidaita natsuwarsa ya ce, "Ok let me get you straight into the point...dama yau a wurin aiki ne na lura da wani a cikin ma'aikatan na a cikin damuwa sosai, shine na gayyace shi office don in ji damuwarsa, a nan yake sanar da ni cewa abu mara daɗi ne ya faru da su game da yarinyar su, ita kaɗai ce ɗiyar su mace sauran yaran su duk maza ne, hakan ya sa suke mata gata duk abun da take so suna yi mata, ya ce tana yawan tambayar su kuɗi su bata ba tare da tunanin komai ba, sai yanzu da Allah Ya bayyana masu abun da take aikatawa ba tare da sanin su ba..." Shiru ya yi don abun nauyi yake masa a zuciya, Sapna da ta kafe sa da idanunta tubarkalla a ɗan razane ta ce masa mi take aikatawa? Da ƙyar Maleek ya faɗi mata abun da take yi da ƙawarta, Sapna ta wani zaro idanu tare da kai hannu ta dafe ƙirjinta, kana ganinta ka san hankalinta ya tashi da jin hakan, to ina ga kuma ta ji cewa ɗiyarta ce ke aikatawa, cikin kwantar da murya Maleek ya ce, "Mun tattauna da shi sosai na bashi shawarwarin da nike ganin sune mafita, a cikin shawaran da na bashi har da wannan yanzu da na kawo don muma mu yi hakan akan Basma matsayin gyara kayanka, duniyar ta lalace, kana ba yaron ka tarbiya wasu na lalatawa ba tare da sanin ka ba, dole idan Allah ya baka yara yanzu sai ka jajirce sosai wurin kula da tarbiyar su, ba zancen wai ka yarda da yaron ka ka ƙi saka masa ido komai zai iya faruwa, al'amurra yanzu sai an dage da addu'a, Allah Ya shirya mana zuriya ya taya mu kula da tarbiyan su." A sanyaye Sapna ta amsa da amin duk jikinta ya yi sanyi laƙwas, hannu ya kawo ya jawo ta jikinsa ganin yadda duk ta yi sukuku, ya shiga kwantar mata da hankali ya ce su dage wurin saka ido kan Basma tare da addu'a in sha Allahu ba abun da zai faru, ta ɗaga masa kai tana lafe a jikinsa, Maleek ya ɗaura fuskarsa a saman gashinta tare da lumshe idanunsa, yanzu ya ɗan ji wani bangare na damuwar da yake ciki kan hakan ya ragu don ya san itama zata saka ido akan Basma, nan take a cikin rai Maleek ya yanke tafiya Umra tare da su, don ya ji yana son ya je gaban ka'aba ya roƙa masu shiriya musamman yadda ita Huda iyayenta basu sani ba balle su yi mata addu'a su kuma saka mata ido, duk da yana da tarin ayyuka a gabansa amman yana ganin wannan matsalar ta girmi duk wani aiki dake a gabansa. Bayan wasu kwanaki suka tafi saudia, Maleek ya yi amfani da labarin da ya ba Sapna na abun da ya faru da ɗiyar abokinsa ya ce mata su roƙa ma Basma shiriya sosai dama sauran yaran musulmi, itama Basma tun kafin su zo sai da ya faɗa mata ta yi masu addu'a sosai, yanzu ma bayan sun zo sai da ya jaddada mata hakan ta yi masa alƙawarin zata yi. Dalilin tafiyar tasu ne ya sa Nailah bata samu zuwa wurin su ba kamar yadda ta yi niyya, bayan da ta kira Sapna kan zata zo ta sanar mata da basu nan sun tafi Umra. Ranar Juma'a Leemarh suka ɗauko hanyar Funtua, tana zaune a bayan danƙareriyar baƙar Jeep tare da dad ɗinta, yayin da a gabansu motar jami'ai ce, Leemarh tana sanye da wata haɗaɗɗar baƙar abaya kanta ta yafa gyalen rigan, yayin da baƙar sumarta ta ɗan fito daga gaba, a fuskarta ta saka baƙin glasses da ya matuƙar yi mata kyau, a kallo ɗaya idan ka yi mata zaka yanke balarabiya ce ko kuma ba'indiya yadda haskenta ya fito sosai a cikin shigar, gaba ɗaya a ƙagare take da su ƙarasa Funtua musamman don ta ga yaya Fahad, dama tun da suka ɗauko hanya ta kira shi ta sanar masa ya ce yana wurin aiki amman zai taso da wuri. Suna shigowa cikin garin Funtua mutane ƴan siyasa suka yi ma motar su ƙawanya suna hargowar tarbar ɗan majalissar tarayyan nasu, gaba ɗaya aka ɗan sauke glass ɗin ƙofofin bayan motan dad na ɗaga ma mutane hannu cikin fara'a, ta cikin glasses ɗin fuskar Leemarh take bin mutanen da kallo, har da ita suke ta ma barka da zuwa tana ɗan ɗaga masu kai a hankali, har suka ƙaraso gidan hajiya mutane na biye da su, a bakin gate motan jami'an ta tsaya yayin da tasu leemarh ta kutsa cikin gidan, a cikin harabar gidan aka faka motar jami'in dake a gaba ya fito da sauri ya buɗe ma dad ƙofa, lokacin har Leemarh ta buɗe ta fito, Sule direban hajiya ya ƙaraso cikin girmamawa yana masu sannu da zuwa, Leemarh ta ce mashi ya fiddo boxes a booth ya kawo ciki da sauri ya amsa da to ta nufi shiga cikin gidan, hajiya ce ta fito daga ɗaki tana sanye da leshi mai kyau, cikin falon ta shigo tana faɗin, "Ko ƴan tafiyan ne suka ƙaraso na ji kaman hayaniya..." daidai lokacin Leemarh ta shigo cikin falon, hajiya na ganinta ta shiga washe baki, da sauri Leemarh ta nufo ta hajiya ta wara mata hannuwa tana ƙarasowa gabanta suka rungume juna, cike da farin ciki hajiya ke faɗin, "You are welcome ƴar hutuna." Dariya Leemarh ta yi tare da ɗagowa ta kai hannu ta cire glasses ɗin fuskarta, gaishe da hajiya ta yi bayan ta amsa ta kama hannunta ta ce su zauna yadda za su gaisa da kyau, shigowa Sule ya yi janye da boxes guda biyu masu kyau hajiya ta ce ya kai ciki ya amsa tare da wucewa, "Haleematu mutanen Abuja, duk ya kika baro su." Tana ta dariya ta ce mata duk suna lafiya suna gaishe da ita, "Daga ke sai baban naku kuka zo ke nan, ya ba a taho mani da takwarata ba da kuma maigidana." Leemarh ta gane Batool da Sultan take nufi ta ce mata za su je Kano ne da mom hajiya ta ɗaga kai, ƙwala ma Balaraba kira ta yi ta fito tare da nufo cikin falon, tana ganin Leemarh da fara'a ta yi mata sannu da zuwa ta amsa mata tare da gaishe da ita, hajiya ta ce, "Ga ƴar hutun mu nan ta iso, a kawo mata abun sha, sun sha hanya." Balaraba ta amsa da to tare da juyawa ta koma kitchen, fitowa ta yi hannuwanta riƙe da madaidaicin tray a saman glass jug ne da cups masu kyau, a saman center table ta ɗaura ta ɗauki jug ɗin dake ɗauke da lafiyayyan kunun aya da ya ji kwakwa a ciki ta zuba a cup, miƙa ma Leemarh ta yi hajiya ta yi saurin amsa tana faɗin bari ita zata bata a baki duk suka yi dariya, barin wurin Balaraba ta yi hajiya ta shiga ba Leemarh kunun ayan a baki suna ta ƴar dariya, sallamar da aka yi yasa Leemarh ɗaga idanunta suka shiga cikin na Fahad da ya shigo, lokaci guda ta shiga sakar masa murmushi shima idanunsa na akan ta yana mata ɗan murmushi yayin da yake ƙarasa shigowa jikinsa sanye da ƙananun kaya, a saman kujerar dake gefe da wadda suke ya zauna, hajiya ta kalle shi tana ƴar dariya ta ce, "Gani nan ina lelen baƙuwata, saboda murnar zuwanta ka ga ma a baki nike bata abun sha." Faffaɗan murmushi ya yi ya ce, "Hakan ya yi kyau." Sannu da dawowa ta yi masa ya amsa tare da maida idanunsa kan Leemarh, tana murmushi ta ce, "Ya Fahad sannu da zuwa, ina yini." Dan jinjina kai ya yi ya ce, "Kun zo lafiya." Ta amsa da lafiya, "Kun gaisa da baban naka ne?" Hajiya ta tambaya, ya ce mata a'a yana tare da mutane, yana rufe baki sai ga dad ya shigo, jikinsa ya yi shigan manyan kayan farar shadda ya fito a babban mutum wanda naira ta zauna
Chapter 132 · 0% Book details