← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 197

Sashe 32

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da yake wani lokacin a gida akan samu wanda ya fita zakka, to suma a gidansu Sapna wadda ita ce ke bi ma Jameela ta fita zakka, tana da kamun kai da natsuwa gata tana son karatu kuma ba laifi tana da ɗan ƙoƙari, sa6anin Jameela da sauran ƙannansu waɗanda sam basu wani fahimtar karatu, Allah dai ya basu kyawun sura amman ƙwalwarsu yadda kasan dusa ce a ciki saboda rashin fahimtar karatu, ita Sapna karatu kawai tasa a gabanta sam bata kula samari, ba kamar Jameela ba da tun tana firamare take da samari kuma suke bata kuɗi, wani lokaci har faɗa iyayensu suke ma Safna akan rashin kula samarin da take yi, suna cewa wai tana masu baƙin cikin alherin da zata sama masu kamar yadda suke samu da ƴar uwarta Jameela, sam bata biye ma huɗubar iyayensu duk faɗan da zasu yi mata, karatunta na boko da islamiyya kawai ta saka a gaba, saboda rashin kula samarin da take yi yasa wani lokacin in ta kawo masu buƙatar da ta danganci karatunta sai su ƙi yi mata, su rinƙa cewa da tana kula samari tana samun kuɗi ai da ta rinƙa biya ma kanta buƙata har ma da nasu buƙatun, da yake tana son karatunta bata son abun da zai yanke mata shi hakan ya sa wani lokacin take tambayar Jameela kuɗi, idan ta ci sa'a ta bata, wani lokacin kuma idan Amminsu na kusa sai ta hana Jameela ta bata wai duk don ta ji matsi ta rinƙa kula samari amman hakan bai sawa ta canza. Akwai wani lokaci da ta rasa ina zata samu kuɗin da zata siya littafai don nata duk sun cika sai dai ta samu paper ta yi rubutu sai ta sa cingam ko kuma ta je jikin wata bishiyar makarantar su ta samo ƙwaro sai ta haɗe paper din da karshen littafin, har ta kai bata da sauran paper din da zata rinka yagowa, data rasa mafita gashi gida an ƙi bata kuɗi ta siya, ƙarshe a 6oye ta je gidan su Soffy wurin mahaifiyarta Hajiya Aisha, tana ƙwalla ta sanar da ita halin da take ciki game da karatunta, saidai bata faɗi mata cewa saboda bata kula samari ya sa iyayensu basu bata kuɗin siya ba, kawai ce mata ta yi sun ce basu da kuɗi, lokacin Hajiya Aisha ta ji tausayinta sosai musamman yadda ta san halin Safna ɗin ba irin na sauran yan uwanta bane, bata da kwaɗayi ko ta saki baki ta faɗi matsalan da ta danganci kanta ko gidan su da sunan a taimaka mata, wannan ne karo na farko ma da ta kawo kukanta wajenta, a lokacin Hajiyar ta ce mata ta je gida zata bada a kawo mata littafan, amman sai ta nuna mata ba a san da ta zo ta fadi mata ba bata son hakan ya sa a buge ta in aka ji ta zo ta roƙe ta, Hajiyar ta fahimce ta ta ce mata shike nan ta je zuwa anjima sai ta dawo, bayan tafiyarta ne ɗiyarta Soffy ta shiga bata labarin irin wahalan da Safna din ke yi akan karatu, ta ce mata kullum a ƙafa take zuwa makaranta ta dawo, kuma wani lokacin ko kuɗin break ma ba a bata ga kayan makarantarta duk sun tsufa sun yage, Hajiya ta ƙara jin tausayinta ya kama ta dama ta na son yarinyar saboda natsuwarta.

Bayan Sapna ta dawo da daddaren Hajiya ta sa ta zauna a falo, lokacin dad ɗin su Soffy na nan ta iske shi a falo, bayanin Sapna ta yi mashi ta roƙe shi kan ya taimaka mata a karatun ta, farko ya nuna shi ya yi masu duk abun da zai iya tun da ya ba mahaifinsu jari, wanda inda ya jajirce ya yi kasuwanci ai da duk ya ɗauki wata ɗawainiyar su, cikin lallami da kwantar da kai ta shiga nuna mashi yarinyar ta fita daban da yan'uwanta kuma tana son karatu, ta roƙe shi kan ya taimaka mata tun da su iyayen nata ba ɗaukar ilimin suka yi da mahimmanci ba, cikin nasara ta ja hankalinsa ya amince da zai taimaka ma karatun Sapna. Daga ranar Hajiya ta sa ta rinƙa zuwa da safe idan driver zai kai yaran gidan makaranta sai a tafi da ita a sauke ta a tasu makarantar, sannan duk wata buƙata ta karatunta ta ce ta rinƙa zuwa tana faɗa mata, har sabbin kayan makaranta da jaka da takalma suka siya mata, Sapna ta ji daɗin hakan kuma sosai ta ci gaba da maida hankali akan karatunta ba ruwanta da kula samari.

A shiriri ce Jameela ta kammala karatun ta na sakandire, daga nan bata ƙara bin ta kan karatu ba sai biye ma samari. Duk halin da suke ciki yayan baban su Amadu ya sani, kuma yana tsawartar ma iyayansu sosai kan rashin kula da tarbiyyar yaransu, ƙarshe sai suka maida shi tamkar abokin gabansu, Amminsu ta zuge abbansu wai baƙin ciki yake masu Allah Ya basu yara kyawawa suna samun alheri da su ba kamar nashi yaran ba, har da cewa baya son ci gaban su ya fi son kullum su yi ta zama ƙarƙashin shi yana taimaka masu, ƙiri-ƙiri suka yanke zumunci da shi, hatta yaran nasu suka dasa masu haushin shi a zuciya, ita dai Sapna ba ruwanta ba abun da ya canza daga bangarenta tana zumunci da su, hakan ba ƙaramin ciwo ya yi ma Amadu ba ya shiga damuwa sosai, matarsa Hafsa ta rinƙa kwantar masa da hankali ta ce ya rabu da su kawai tun da ya yi bakin ƙoƙarin shi ya sauke hakkinsa na ɗan'uwan su. Bayan ɗan lokaci da hakan Amadun ya haɗu da haɗarin mota wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuwarsa, a lokacin yana da yara biyar.

Lokacin da Soffy ɗiyar Alhaji Mahmud ta fara karatu a jami'ar BUK hakan ya ja hankalin Jameela ta ji tana son itama ta fara yin karatun jami'a, da yake a lokacin ta zama babbar yarinya idan ka ganta zaka yi tunanin ta girme ma shekarunta saboda tana da ƙira irin ta manyan mata masu diri, hakan ne ma ke ƙara jawo mata samari saboda kyawun surar ta, akwai wani babban mutum ɗan siyasa da take tare da shi a lokacin, tun farkon haɗuwar su ya nuna yana son aurenta amman ta ƙi amincewa ta nuna mashi ita gaskiya ba yanzu zata yi aure ba saboda yarinya ce ita ba wata babba ba, da yake yana samun yadda yake so a wurinta hakan yasa yake sakar mata kuɗi duk abun da take so yana yi mata. Lokacin shi ta yi ma maganar tana son ci gaba da karatu, saidai koda aka amso result ɗinta gaba ɗaya Waec da Neco abun ba kyawun gani duk F9, a lokacin alhajin nata ya ce mata ba yadda za ai ta samu ci gaba da karatu da wannan sakamakon, ganin ta shiga damuwa sosai ya kwantar mata da hankali da cewa hakan ai ba wata babbar damuwa bace, ya nuna mata su da suke da hanya za a canza mata wata jarabawar bama sai ta sake yi da kanta ba. Haka kuwa aka yi sai gashi an yi mata wata jarabawar kuma duk ta ci, ba tare da wata wahala ba sai gashi ta samu admission itama a BUK. Lokacin data fara karatun ita Soffy har ta shiga shekara ta biyu, amman duk da haka manne take da ita, duk ƙawayen Soffyn ta maida su itama ƙawayenta musamman da yake duk yaran masu kuɗi ne, cikin ɗan lokaci sai gashi ta yi suna a makarantar, ba iya yan set ɗinta da na Soffy ba, har cikin manya yan shekarar ƙarshe tana da abokai maza da mata, da yake abu mai kyau na da jan hankali hakan yasa duk waɗanda take manne mawa ta nuna tana son ƙawance da su basu gudun ta ko hantarar ta sai ma son ta da suke yi.

Sam Jameela bata wani maida hankali akan karatu sai shiriritar abokai da samari, wani lokacin har makarantar ake zuwa a ɗauke ta, hatta cikin lakcarorin su tana da samari, gata yar ina da biki ce da ta ji cikin abokanta ana maganar biki sai ta je ko ba a gayyace ta ba har da su ƙarfin halin yin anko, ba kamar in ta ji bikin masu kuɗi ne ta dingi faman zura jiki har sai ta samu shiga. Da yawa waɗanda basu santa ba a makarantar sun yi zaton ɗiyar wani ce saboda kyawunta da yadda take saka suturu, wasu a tunanin su ita ɗin ƴar'uwar su Soffy ce, kuma sam Soffyn ba ta fallasa ko ita wacece, sai wasu daga cikin ƙawayen Soffy da suke tare tun kafin su zo jami'a kuma sun san gidan su da kuma alaƙarta da Jameela, sune suke fallasa ko wacece ita ganin irin yadda take rawar kai tana nuna kamar ɗiyar uban wani ce ita.
Chapter 32 · 0% Book details