Sashe 79
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kansa da na gemunsa da ke haɗe da yar hurhura ne zaka iya gane cewa ya ɗan manyanta, sosai Salma ta yaba da kyawun suffar mutumin wanda da gani naira ta zauna masa kuma ɗan gayu ne na gaske, kasa haƙura ta yi sai da ta tambayi Deen wanene shi, daga murmushin da ya bayyana akan fuskar Deen zaka fahimci yana ji da mutumin, ya bata amsa da daddy Maleek a wurinsa ya taso a London, hoton gaba mutumin ne da wata kyakkyawar mata, daga yadda ya rungume ta ta gane matarsa ce, lokaci guda kuma a ranta ta yanke matar baturiya ce ko kuma yar indiya duk da ta ga kamanninta da mom ɗin Deen, hoto na gaba sune sun rungume wata matashiyar yarinya da suka saka a tsakiya, bin budurwar Salma ta yi da kallo a ranta tana ayyana ko wacece don bata ga kamanin su da ita ba, duk da kana ganin yarinyar zaka gane yar hutu ce kuma wayayya, kasa haƙuri Salma ta yi ta tambayi Deen wacece ita, ɗan kallon hoton ya yi ya janye idanunsa tare da bata amsa da cousin sis ɗin shi ce Basma, jin ya ce cousin sis ya sa Salma sake tambayar shi ke nan daddy Maleek ɗin ɗan'uwan mahaifinsa ne, ya ɗan girgiza mata kai ya ce shi aminin mahaifinsa ne mom ɗinta ita ce ƙanwar mom ɗin sa, sake kallon hoton Salma ta yi tana ɗan mamakin yadda Basma ta fi iyayenta baƙi duk da mahaifinta ma ba fari bane amman ya fita hasken fata, ƙarshe zuciyarta ta bata ai hakan na faruwa sosai, ci gaba da kallon hotunan ta yi daga baya ta fita daga cikin folder ta bude ta wata da aka saka 'Bdays' bayan ta shiga hotunan ahalinsa ne a ciki na bikin murnar ranar haihuwar su, kusan kowa cikin waɗanda ta gani akwai hotunan bdays ɗinsu har da iyayensa da kuma shi kansa Deen ɗin, sosai hotunan suka burge ta ba kamar na Deen wasu tare da yan team ɗinsa na kwallo ya yi celebrating wasu a wurare daba-daban, wata folder ta shiga ita kuma an rubuta 'Lifestyle' nan kuma duk hotunan Deen ne a wurare daban-daban, akwai waɗanda ya yi a ƙasashe daban daban da ya je on vacation, wasu a bakin ruwa shi da abokansa fararen fata suna yin barbecue, wasu a snow yana skiing, wasu yana swimming, wasu yana driving a haɗaɗɗun motoci, wasu a saman bike, wasu a cikin jirgi na sama da na ruwa, har da wanda ya yi a gaban ka'aba, Salma ta shagala tana ta kallon hotunan nashi da suka yi matuƙar tafiya da hankalinta, kiran wayar da aka yi ma Deen ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi, faɗin inda suke zaune ta ji ya yi a ranta ta raya ƙilan hajiya ce ke tambayarsa da ta ji shiru, bayan ɗan lokaci da yin wayar tasa kamar ance Salma ta ɗaga idanunta, ganin wanda ya nufo inda suke ya sa gabanta wani irin faɗuwa, da sauri ta ajiye wayar da ke a hannunta hakan ya sa Deen kallonta, Fahad na gab da ƙarasowa ta yi saurin miƙewa ta ce ma Deen za ta tafi, shiru ya yi yana kallonta noticing how nervous she looked, Fahad na ƙarasowa ta bar wurin ko ƙara kallon Deen bata yi ba, sai lokacin Deen ya fahimci dalilin canzawarta, miƙewa Deen ya yi yana kallon Fahad da murmushi ya miƙa masa hannu ya ce, "Welcome ya Fahad." Kai ya ɗaga masa ya ɗan juya yana kallon hanyar da Salma ta bi kafin ya juyo ya kalli Deen, zama suka yi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce ma Deen, "What is dat gal doing here?" Dan murmushi ne akan fuskar Deen ya ce masa shine ya kira ta, wani suspicious look ya ma Deen ɗin jin abun da ya ce bai dai ce masa komai ba, dama ya yi mamakin awaran da ta kawo masa ranan nan har ya zauna yana ci, don ya yi clearing any doubt ya yi ma Fahad bayanin dalilin kiran ta da ya yi, shiru ya ɗan yi sai kuma a taƙaice ya ce Allah Ya tabbatar da alkhairi, bayan Deen ya amsa da Amin yana kallonsa ya ce, "How is work?" Amsa masa ya yi da Alhamdulillah, dama daga wurin aikin yake yanzu, hira suka ci gaba da yi bada jimawa ba aka fara kiran sallar la'asar hakan ne ya tashe su don zuwa yin salla. Lokacin da Salma ta koma gida innarsu bata nan ta tafi gidan gaisuwa kamar yadda Imrana ya sanar mata, jin haka itama ta bita can gidan bayan ta cire gyalen jikinta ta saka hijab, sai bayan da aka gama sallar la'asar suka dawo, sai da suka yi salla sannan Salma ta iske innarsu a ɗakinta nan ta sanar mata dalilin kiran ta da hajiya ta yi, da mamaki innarsu ta maimaita maganar aikin da Deen ɗin ke son badawa Salma ta ƙara tabbatar mata da hakan, daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba ƙaramin daɗin maganar ta ji ba, ta ce, "Shi dai wannan mutumin ya ji daɗi wallahi, da Allah Ya hore masa sai shima yake taimaka ma mutane, dama haka Allah Yake so idan ya baka kai ma sai ka bayar. Sadakar abinci ba ƙaramin taimako bane za a yi ma mutane Salma musamman a lokacin nan da mutane ke cikin hali." Salma da ke ɗan murmushi ta ce, "Wallahi kuwa, ya ce duk yadda muka yi da ke sai in sanar masa, kamar yana son jin amsa da wuri in za a yi ko ba za a yi ba don ya ce bai da lokaci sosai." Da sauri innarsu ta ce, "Yi kai, Salma a yadda mutane ke cikin hali ai duk wanda aka ma tayin aikin nan ban tunanin zai ƙi amsa, ni kaina ina cikin masu yi tun da ko ba komai aikin lada ne, zan yi ma innarsu Habu magana duk dama tana cikin alhinin rasuwa, to amman tun da sauri ake zan je in yi mata bayani tun da abu ne na ƙaruwa, sai dai kuma kada sauran abokan zaman nata su ga an ware su ko su yi tunanin an yi masu baƙin ciki." Ta ƙarasa idonta akan Salma, tambayarta ta yi kamar mutum nawa ake buƙata da za su yi aikin, Salma ta bata amsa da bata sani ba sai dai a tambaye shi, innar ta ce to ta yi hakan idan babansu ya dawo za su yi magana da shi. Bayan sallar isha lokacin da baban su Salma ya dawo innar tasu ta yi masa bayanin aikin na Deen, shima ya yaba sosai da hakan tare da yin fatan alkhairi, suna cikin tattaunawar ne aka yi sallama daga waje, da yake jiya da yau basu yi awara ba saboda rasuwar da aka yi duk yaran na nan, Imrana ne ya je ya dubo mai yin sallamar, bayan ya dawo ya ce masu baban su Habu ne, miƙewa baban su Salma ya yi ya nufi hanyar wajen, tare suka dawo cikin gidan da baban Habun, yaran suka shiga gaishe da shi da fara'a yake amsa masu, miƙewa innarsu Salma ta yi daga kan tabarmar da take tana mashi sannu da zuwa tare da gaishe da shi, a saman tabarmar suka zauna shi da baban su Salma ita kuma innarsu ta koma daga gefe ta zauna kan kujera, kallon su Imrana ya yi duk ya kira sunayen su kafin ya tambayi ina Salma, fitowa ta yi daga cikin ɗakinta ta zo daga bakin barandar tana murmushi ta gaishe da shi, yana murmushi ya ce, "Salma ya ya? An daina kukan ko?" Maida idonta ta yi ƙasa tana ɗan murmushi ta ce mashi eh, "Yauwa haka yakamata. Ya makaranta." Ta amsa da Alhamdulillah, wasu ƴan matasan maza ne guda biyu suka shigo ɗauke da wasu kaya babansu Habun ya ce su kawo su nan bakin baranda, bayan sun ajiye suka gaishe da su baban Salma kafin suka tafi, kowa kallon kayan da aka ajiye ya yi wanda kayan abinci ne da alamun rashin fahimtar na miye akan fuskokinsu, a nutse baban su Habu ya fara magana, "Dama zuwa na yi in sanar da ku abun arziƙin da ya same mu, in kuma yi maku godiya musamman Salma don kusan ita ce silar komai, yanzu bada jimawa ba Hajiyar Ambasada ta kira ni dama ta amshi lambar wayata, sha tara na arziƙi suka mani wllh, an bani buhun shinkafa da na masara da gero, sai katon din taliya da macaroni kowanne biyu har da jarkar mai, sannan ita ta bani dubu ɗari biyar shima jikan nata ɗan kwallon nan ya bani dubu ɗari biyar an ce in nemi wata sana'a in fara yi, suma iyalina kowacce jikan nata ya bata dubu ɗari su ɗan samu sana'a da za su fara yi. Ni dai tsabar farin ciki ma kuka na kama yi masu." Ya ƙarasa tare da kai hannu ya matse kwallan da suka taho mashi, babansu Salma ba abun da yake faɗi sai, "Alhamdulillah, Allah Ya saka da alkhairi..." Haka innar su Salma farin ciki ne ya lullu6e ta, cikin karyayyar murya ya ce, "Ku ma na gode maku ƙwarai, Allah Ya saka da alkhairi Ya sa kyautata ma maƙwabta ya zamo silar shiga aljanna." Gaba ɗaya suka amsa mashi da Amin har da su Imrana, kallon Salma ya yi, "Ke ma Salma Allah Ya saka maki da alkhairi, Ya albarkaci rayuwar ki, Allah Ya baki miji na gari da zai kula da rayuwar ki..." Kallon su Imrana ya yi suma duk ya saka masu albarka, kuɗi masu yawa ya fiddo daga aljihun shi ya miƙa ma babansu Salma yana murmushi ya ce ga wannan su ma sai su saka albarka, da sauri baban su Salma ya ce, "A'a, ka bar su, kai da aka ba ka yi sana'a, Allah Ya saka masu albarka Ya sa silar arziƙi ne." Matsa mashi baban Habu ya yi kan ya amsa, yana murmushi ya ce, "Wallahi malam Umaru ba zamu amshi kudin nan ba." Bin shi ya yi da kallo fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi ya ce ya zai yi rantsuwa haka, sai kuma ya ce, "Tun da haka ne, nima wallahi wanccan kayan sai