← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 197

Sashe 45

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun a walkway ɗin shiga cikin gidan zaka fara shaida tsaruwar shi, har da wani haɗaɗɗan console mirror da manyan flower vases masu ɗauke da tafka tafkan fulawoyi, wani babban falo suka shigo mai ɗauke da light purple ɗin kujeru, komai na cikin falon kalar light purple ne wasu abubuwan an yi ratsin dark purple, hatta hasken fitulun cikin falon wasu na bada launin purple, a saman luntsuma luntsuman kujerun dake ciki wasu daga cikin ƴan gidan ne ke yin kallo, autar su Binafa ce ta shigo cikin falon zata nufi wurin da sauran suke, tana hango su Fahad da suka shigo ta nufi wurin su, tun kafin ta ƙarasa idanunta suka sauka akan Deen, cikin ƙaraji ta furta, "Laa, ga yaya Deen ɗin ball nan wllh!" Hakan ne ya jawo hankalin sauran kan su, da gudu Binafa ta nufi Deen ya wara mata hannu yana sakin faffaɗan murmushi, tana zuwa ya ca6e ta tare da ɗaga ta sama ta shiga ƙyalƙyata dariyar farin cikin ganin shi, Sadeeq ne ya rugo shima yana washe baki, Deen ya sauke Binafa shima ya ca6e shi ya ɗaga shi yana faɗin, "My man ka ƙara girma ka yi nauyi da yawa.." Duk suka yi dariya, Binafa ta ruga tana faɗin bari ta je ta faɗo ma momy ga ya Deen ɗin ball ya zo, bayan ya sauke Sadeeq kallon Khaleel dake tsaye yana ta sakin faffaɗan murmushi ya yi ya miƙa mashi hannu suka gaisa, cike da zolaya Khaleel ɗin ya ce shi ba za a ɗaga shi irin na su Sadeeq, Deen na murmushi ya ce, "Ai kai ka girma da yawa, kama kusa kamo ni tsawo." Duk suka yi dariya Khaleel ɗin ya yi mashi an zo lafiya ya amsa mashi, yayarsu Sadeeya wadda ita ce ke bima Fahad ta ƙaraso wurin tana sakin murmushi jikinta tana sanye da straight skirt da riga na atamfa, a yanayin halitta bata da tsawo sosai amman tana da diri kuma tana da kyawun fuska, akwai kamanceceniya sosai tsakaninta da Fahad duk da haskenta bai kai na Fahad ba,

"What a surprise visit! You'are highly welcome my lil bru." Ta yi maganar tana miƙo mashi hannu alamar su gaisa, Deen na kama hannun ya murɗe shi ba arziƙi ta saki ƙara tare da duƙewa, cikin jin zafi ta furta, "Mi na yi maka kuma, daga abun arziƙi na yi welcoming naka." Yana murmushin ƙeta ba tare da ya saki hannun ba ya ce, "Who's ur lil bru?" Cikin nuna alamun jin zafi ta furta, "Ƙarya na yi to kai ba ƙanin nawa bane..." Bata ƙarasa ba ta ƙara sakin ƙara da ƙarfi sakamakon ƙara lanƙwasa hannun nata da ya yi,

"Ahhh...kar fa ka karya mani hannu Deen, kasan dai wanda zan aura soldier ne zaka tsinci kan ka a guardroom wllh." Yana ƴar dariya ya ce tun da ita yayar shi ce ba sai ta ƙwace hannun ba, su Fahad dake tsaye suna ta murmushi, hajiya Amina ce ta shigo cikin falon tana tafiya a nutse irin ta manyan mata masu cikar kamala, tana da ƙwarjini sosai a fuska gata jajir da ita, doguwar riga ce a jikinta ta yafa mayafi a saman kanta daga gaban kanta kitson da aka yi ma baƙar sumarta ya ɗan fito, da murmushi akan fuskarta ta iso wurin, Sadeeya na ganinta ta ce, "Momy kin gani zai karya ma ɗiyar ki hannu ko, pls ki ce mashi ya sakar mani hannu." Dariya ta yi ta ce ita ba ruwanta dama ai sun saba kuma ta san ita ce ta ja shi.

"Welcome my son." Ta faÉ—a da murmushi, É—an rankwafar da kan shi ya yi ya gaishe da ita ta amsa tare da yi mashi an zo lafiya,

"Pls ka sakar mani hannu wllh fa ina jin zafi." Yar harararta ya yi, ya ce, "Sai kin faÉ—a da bakin ki ni yayan ki ne." Tura baki ta yi ta ce, "To wai a ina ka zama yayan nawa ba na girme ka ba, ko don ka ga ka zama jibgege shine zaka fara yin runton shekaru." ÆŠan girgiza kai momy ta yi jin yadda basu gajiya da yin musun shekaru duk in suka haÉ—u,

"Bari in raba gardaman, rigima ne kawai naki Sadeeya amman kin san Deen ya girme ki, duk da ba wani nisa ne sosai tsakanin ku ba, ya baki shekara ɗaya." Dariya duk suka yi Deen ya ce mata small girl, tana dariya ta ce ta ji to ya sakar mata hannu, ƙin saki ya yi ya ce sai ta faɗa a gaban kowa shi yayanta ne, ƴar hararar shi ta yi aikuwa ya ƙara murɗe hannun ta saki ihu tana faɗin, "Don Allah Ya Deen ka yi haƙuri wllh zaka karya mani hannu fa." Gaba ɗaya suka saki dariya jin ta yada makaman nata ta kira shi da yaya, yarfe hannun ta shiga yi bayan ya saki tana faɗin kamar da hannun ƙarfe ya riƙe ta,

"Wllh ya yi maki ma da sauƙi yaya Sadeeya, da ya kama ki sosai to sai kin yi acawi a jiki." Dariya duk suka yi jin kalaman Sadeeq, momy ta ce mutum ya zo sun ƙi bari ya shiga ya je ya zauna, kallon Deen ta yi ta ce, "Let's go in my son." nufar ciki suka yi duk suka zazzauna a saman kujeru, ƙara gaisawa suka yi da momy ta tambaye shi ya zo lafiya da kuma iyayensa na can,

"Yaya Deen ai duk in kuna yin ƙwallo muna ganin ka." Binafa ce da ta maƙale a jikinsa ta faɗi hakan, ɗage mata gira ya yi ya tambaye ta da gaske, ta ɗaga mashi kai ta sake cewa, "Kuma ka iya sosai, idan ka ci ball sai mu yi ihu mu ce, 'A goalll..' har rawa muke yi, idan kuma baku ci ba sai bamu jin daɗi, mu yi ta tsoki har mu zagi waɗanda suka ci ku." Momy da ke zaune ta ce 'assha' duk suka yi dariya, ƙara rungume ta Deen ya yi ya ce mata ai haka wasa yake ba kowane lokaci nasara ke a wurin naku ba su daina damuwa. Hira suka ci gaba da yi Sadeeya ta iso wurin su tana riƙe da tray an ɗaura jug da glass cup a kai, a saman wani babban haɗaɗɗan center table na glass wanda ke bada launin purple ta ɗaura tray din, wani ƙarami ta ɗauko a can gefe ta aje daga gaban Deen ta sauko tray ɗin ta ɗaura sama, tsiyaya mashi lemun ta yi ta bashi tare da faɗin gashi don ba halin shi na mugunta ba, yana murmushi ya kar6a ya ce, "Thank you my lil sis." Ƴar hararar shi ta yi tana murmushi ta zauna a saman kujera,

"Son, ka yi mana zuwan bazata, ban yi tunanin zamu gan ka yanzu ba, I thought sai ka ɗan kwana biyu a Abujan, gashi ba a shirya maka abu na musamman ba nasan ka yi missing food din nan. Koda yake ƙilan ai mom ɗinka na can na yi maku irin su." Ta ƙarasa da murmushi a kan fuskarta, amsa mata ya yi da ba komai ai sun ma jima da zuwa suna gidan hajiya, kallon Fahad ta yi ta ce miyasa bai kira ya sanar da zuwan su ba, dakatawa ya yi da latsa wayan da yake ya ɗan kalle ta ya ce ya manta bai yi tunanin hakan ba,

"Akwai tuwo, kasan dad din naku ƙa'ida sai ya ci tuwo da dare, amman idan baka son shi sai Sadeeya ta yi preparing maka wani abincin." Momy ta faɗa da murmushi, ce mata ya yi lafiya lau yana son tuwon ya daɗe bai ci shi ba,

"Yaya Deen a can ba a yin tuwo?" Binafa ta tambaya, kallonta ya yi ya bata amsa da mom Sapna na yi masu idan ya je gidan amman wani lokacin yana daɗewa bai samu zuwa ba idan sun tafi wasa, umarnin zubo mashi tuwon momy ta ba Sadeeya ta tafi, kafin ta dawo daddy ɗin su ya shigo cikin falon ya nufo inda suke, Alhaji Sa'ad mutum mai dattako da haiba yana sanye da riga da wando na brown ɗin shadda, da ganin kayan ƴan cikin babbar riga ne amman bai saka babban rigan ba, sannu da zuwa mutanen cikin falon suka shiga yi mashi yana amsawa yayin da ya nufi Deen da murmushi, miƙewa Deen ya yi yana gaishe da shi dad ɗin ya miƙa mashi hannu suka gaisa, "Mutan turai barka da zuwa, fatan ka zo lafiya" Amsawa ya yi da ɗan faffaɗan murmushi, daddy ya ce mashi ya zauna shima ya nufi kujera ya zauna,

"To ya ƙasar taku, ya kuma tamolan. Ai ina ganin yadda ake ta ƙoƙari, Allah Ya ƙara taimako Ya kuma tsare." Gaba ɗaya suka amsa da Amin, Deen na murmushi ya ce, "Daddy ashe kana kallon ball." Dariya daddy ɗin ya yi, ya ce, "Can baya dai ina kalla amman sai na bari, yanzu kuma tun da yarona na yi ai dole in rinƙa kallo." Duk murmushi suka yi, Binafa ta ce, "Ai tare ma muke kalla, kasan mi yaya Deen?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, ta ci gaba, "Idan muna kallon ball en ka ka ci sai daddy ya ce, 'goalll, that's my son, I'm very very proud of you Deen, ya yi ta jin daɗi yana dariya. Idan kuma kuka gama yin ball baku winning ba sai bai jin daɗi, fuskan shi ya yi haka, sai ya ce, 'dama wasa ya gaji haka sai haƙuri." Ta ƙarasa tana ƙyalƙyata dariyar kwaikwayon daddy ɗin nasu da ta yi, kowa dariya ya yi har da daddy ɗin, hannu ya kawo alamar zai kamo ta yana faɗin,"Zo nan ummina, wato kina nan kina karantar duk yadda nike yi ko, har na zama abun zolaya." Hayewa ta yi kujera ta lafe jikin Deen tana ta dariya, Sadeeya ce ta iso hannunta riƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci, tambayar Deen ta yi ko ta kai mashi dining area ya ce eh ta juya,
Chapter 45 · 0% Book details