← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 197

Sashe 60

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Kasuwanci yana da daɗi sosai, musamman idan Allah Ya riƙe maka, ba don kasuwancin nan da muke yi ba watakil yanzu abun da muke samu matsayin pension ba lalle ya iya riƙe mana iyali ba a yadda rayuwar ta yi tsada..." Ya ɗan dakata su Deen suka jinjina kai alamar tabbatar da gaskiya ne zancensa, ya ci gaba da cewa, "Shi ya sa yana da kyau bayan aikin gwamnati mutum ya samu wata kasuwa yana yi, hakan na da amfani sosai musamman a lokacin da ba aikin. Idan kuma kasuwancin kaɗai mutum ke yi yana da kyau ya bullo da wasu hanyoyi da dubaru da za su inganta sana'ar tasa, ya zama a koda yaushe ana tafiya da shi...." Dakatawa ya sake yi yana shafa sumar gemunsa dake haɗe da ƴar furfura, "Son, na san bayan tamolan baka rasa wata kasuwar da kake yi ko, kamar yadda na ga yawancin yan ƙwallo zaka ga suna wasu kasuwancin daban-daban." Deen ya ɗaga kai with calmness ya ce,"Yes daddy, ina da hannayen jari da wasu kamfuna daban-daban, sannan akwai wasu hanyoyin da muke samu da so da yawa." Kai daddy ya jinjina, "Ma sha Allah..."

Gyara zama Deen ya yi ya ce, "Daddy idan ba damuwa dama ina son neman shawara a wurin ka." Ɗagowa daddy ya yi ya fuskance shi da kyau ya ce, "To Allah Ya bani ikon baka mai amfani." Amsawa ya yi da Amin kafin ya ce, "Ina son buɗe company ne a nan, shi ne nike son ka bani shawara abun da kake ganin zai samu kar6uwa kuma zai kawo ma mutane sauƙi." Jinjina kai daddy ya yi tare da yin shiru alamar yana nazari, after few minutes ya gyara zamansa tare da ɗan yin gyaran murya ya ce, "To a ganina cikin abubuwan da za su samu karbuwa idan aka bude companyn su akwai abinci, wato kamfanin da ya danganci sarrafa kayan abinci tunda shi wannan ba shi da wani lokaci da za a ce ba a tafiya da shi, saboda abinci abu ne wanda ake buƙatarsa sosai a koda yaushe. Sannan buɗe company da ya danganci abinci a nan za a samu sauƙin tafiyar da shi duba da yadda muke da albarkar noma a nan, akwai kamfuna da dama dake sarrafa abinci ciki da wajen nijeriya waɗanda a nan suke siyan kayan da suke sarrafawa. Ka ga dama an ce wai da arziƙi a garin wasu gara a naku, a nakun ma a cikin gidanku, idan namu ya buɗe kamfanin ai ba buƙatar siyar ma wasu kayan amfanin gona ke nan." Gaba ɗaya suka yi ƴar dariya, bayan shiru na ɗan lokaci ya ci gaba, "Sai abu na biyu da nike tunanin idan aka buɗe kamfaninsa zai samu kar6uwa shine kamar textile ko kayan sakawa, ka ga mu nan a arewa bamu da kamfuna irin haka, yawanci a kudu ake da su wasu kayan ma masu inganci sai dai a shigo mana da su daga ƙasar waje, kuma ka ga suma yawancin abubuwan da suke sarrafawar wasu duk a nan suke samun su, kamar auduga da sauransu. To ina ga cikin waɗannan biyun duk wanda aka yi zai samu karbuwa, kuma zai kawo sauƙi da ci gaba a arewa." Kai Deen ya jinjina alamar gamsuwa, Daddy ya ce "Sai ka natsu ka ga wanda ya yi maka, wanda kuma nauyin aljihunka ko in ce account ɗin ka zai iya yi." Ya ƙarasa yana ƴar dariya, Deen yana kallon daddyn da murmushi ya ce, "Zan duba duka in sha Allah." Dan waro ido daddy ya yi ya ce, "Duka son...!Hakan ba ƙaramin shiri yake buƙata ba musamman na kuɗi." Still da murmushi a fuskarsa ya ce, "In sha Allah ba zai gagara ba, ko ba duka ba a lokaci guda." Jinjina kai daddy ya yi, "Ma sha Allah, Allah Ya taimaka Ya tabbatar da hakan. In sha Allahu nima ba za a barni a baya ba zan bada duk wata gudunmawa domin tabbatuwar hakan idan Allah Ya nuna mana, kuma muna daga cikin masu saka hannayen jari, tun da muka ma saka ma wasu balle namu." Duk murmushi ne akan faces ɗin su, Deen ya dan rankwafar da kai ya ce, "Thank you daddy..."

"Fahad kai ya maganar ginin asibitin naka?" Kallon daddy ya yi da murmushi ya ce, "Tana nan daddy, dama na bari in shirya sosai yadda aikin ba zai delay ba idan aka fara, but...jiya Deen ya ce we should collaborate on it." Kallon Deen ya yi ya ce, "Haka ne son?" Kai ya jinjina ya ce eh, daddy ya ce, "Hakan ya yi kyau, amman ka fara tuntu6ar iyayenka kan hakan." Shiru Deen ya ɗan yi a ransa yana raya ya san ko da mahaifinsa ya amince to mom ɗinsa ba zata ta6a amincewa da hakan ba, kallon daddy ya yi ya ce, "Daddy tun da kai ka sani ai duk ɗaya ne." Murmushinsa na dattako ya yi mai nuni da jin daɗin maganar Deen ya ce, "Duk da haka son, suma suna da hakkin ka sanar masu ko don ka samu sakawar albarkar su." Amsa masa ya yi da toh, kamar daddy ya san abun da Deen ya saƙa a ransa ya sake cewa, "Ka sanar da su before a fara gudanar da aikin don ka ji miye ra'ayin su a kai." Shiru Deen ya ɗan yi don a yadda ya yanke kawai sai bayan an gama gaba ɗaya aikin asibitin zai sanar da su, slowly ya furta"Okay daddy."

"Allah Ya ƙara saka albarka a dukkanin abun da muka sa a gaba, nima da na ce ma Fahad filin da na bashi matsayin bashi ne idan komai ya kammala aiki ya kankama zai biya ni koda a hankali, a yanzu na janye batun bashin na mallaka maku shi kyauta matsayin tawa gudunmawar, sai ku yi haɗin gwiwa wurin aikin ginin, zuwa a kammala mu gani idan da gudunmawar da zamu ƙara baku." A tare suka haɗa baki wurin yi masa godiya da adduar Allah Ya ƙara girma da lafiya, bayan ya tambaye su ko akwai wani abu duk suka ce masa a'a ya sallame su, bin su da kallo ya yi yayin da suka nufi ƙofa, a ransa yana matuƙar jin daɗin haɗin kan su, suna tuna masa lokacin da suna matasa shi da mahaifin Deen, haka suke kansu a haɗe yake komai za su yi sai sun tambayi shawaran juna, sa6anin yanzu da komai ya canza a tsakanin su, duk da daddyn bai bari hakan ya zame masa damuwa ba, ya saka a ransa cewa kowa yana da iyalin da zai iya yin shawara da su. Bayan sun baro part ɗin daddy upstairs suka nufa zuwa part ɗin Fahad, suna fara taka staircases Sadeeya da ta shigo cikin falon ta kira sunan Deen, hakan ya sa shi dakatawa yana jiran ta ƙaraso, tana washe baki ta miƙa masa wayarta ta ce, "Duba ka gani don Allah yadda hotunan suka ɗauko, kuma packaging ɗin nawa ya yi, motan ta hau da ni sosai Allah..." Ta ƙarasa maganar tana dariya, Kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, da gaske sun yi kyau dama ga wayan tata iphone ce, bayan ya gama kalla ya ce, "Yakamata ai snapping naki ai kina driving yadda za a fi yarda naki ne." Ya faɗa yana ƴar dariya, ɗan waro ido ta yi ta ce bata yi gigin hakan ba don gani take kaman ba zata iya driving motan ba, miƙa mata wayan ya yi ya ce lafiya lau zata iya tuƙa ta mana ba ta iya driving ba, ta ce a'a gara dai idan ya fara nuna mata, ci gaba da hawa matattakalar ya yi yana faɗin ok idan ya fito zai nuna mata lokacin tuni Fahad ya wuce ya bi bayansa.....

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_

_ZAINAB BATURE_

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

22
Chapter 60 · 0% Book details