Sashe 110
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ɗan jimm kafin ya ce, "Kamar akwai wata da nike jin hakan akan ta, amman kuma bata sani ba don ba komai tsakanin mu." Har sai da gaban Leemarh ya ɗan faɗi jin abun da ya ce, a ranta take raya ke nan ma yana da wadda yake son aura, "Leemarh are you there?" Fahad ya faɗa jin shiru kamar bata kan wayar, cikin ƙoƙarin daidaita natsuwarta ta ce mashi eh, tambayarta ya yi yanzu wace shawara zata bashi kan hakan, baiwar Allah duk ta daburce daga yanayin muryarta ya gane hakan, ta ce mashi kawai ya sanar da ita in dai ta yi mashi ta san ma bazata ƙi amincewa da hakan ba, Fahad ya ce, "Are you sure hakan yakamata in yi?" Farko shiru ta ɗan yi, murya a sanyaye ta ce masa eh, ya yi mata godiya ya ce zai jaraba yin hakan, daga haka bata sake cewa komai ba, daga baya ta ce mashi sai da safe zata kwanta gobe akwai school ya amsa mata da ok ya ce mata good nyt, da murmushi akan fuskarsa yake kallon screen ɗin wayar bayan ya cire daga kunnansa, kife fuskarta ta yi a saman gwiwowinta tana jin wani iri a cikin zuciyarta, yanzu shike nan burin ta na son auren yaya Fahad ba zai cika ba, hakan take rayawa a cikin zuciyarta, wani 6angare na zuciyarta ya shiga ƙarfafata cewa ai bai riga ya tsayar da waccan da ya ce matsayin wadda zai aura ba, tana da damar da zata iya cimma burinta, amman ta yaya? Ta raya hakan, zuciyarta ta shiga tunzurata kan kawai ta sanar masa abun da ke a cikin ranta, to amman idan kuma ya zamana shi bai son ta fa? Wata zuciyar ta raya mata ko don matsayin ta na yar'uwarsa zai iya amincewa da soyayyarta ya aure ta, sai dai ita kuma ta fi son a ce yana son ta kamar yadda take son shi su yi aure ba wai ya aure ta don tana yar'uwarsa ba kawai ba tare da akwai son ta a zuciyarsa ba, ƙarshe zuciyarta ta ci gaba da karfafa mata cewa lokaci bai ƙure ba zata iya saka mashi son ta a cikin ransa har ta cimma burinta, wayarta ta ɗauka ta tura masa saƙo cewa don Allah idan zai yuwu gobe da safe su haɗu, ta yi sending saƙon cike da fatan Allah ya sa bai yi bacci ba, bayan ɗan lokaci sai ga kiransa ya shigo, picking ta yi tare da yin sallama, bayan ya amsa ya tambaye ta lafiya dai ko take son su haɗu, ta ce mashi lafiya lau dama saƙo ne take son bashi, ɗan jim ya yi kamar yana yin nazari, ya tambayi a ina za su haɗu ta ce mashi ko in zai iya zuwa nan gida kafin su tafi school tun da ya ce da sassafe za su wuce Zaria, tambayarta lokacin da suke zuwa school ya yi ta faɗa masa, ya ce zai yuwu su haɗu a school din? ta ce, "Eh zaka iya shigowa, ko kuma in tsaya a wurin gate." Ya ce ok idan ba matsala su haɗu a bakin gate ɗin zai yi ƙoƙarin zuwa da wuri, ta ce, "Ok ya Fahad na gode, hope ban takura ka ba, ka ce da wuri zaku tafi." Ya ce mata no problem sai goben suka yi sallama, saƙe-saƙen yadda zata kasance tsakanin su goben ta shiga yi, a ranta take jin anya hakan da ta yi daidai ne, don kawai ta bashi chocolates zata saka shi ya zo alhalin ya shirya tafiya da sassafe, wata zuciyar ta ƙarfafe ta kan wannan ce damar ta ta fara cusa masa son ta a cikin rai don haka kada ta bari ta rasa ta, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Washe gari Leemarh bata iya tsayawa ta yi breakfast sosai ba, saboda ƙagarar da ta yi su haɗu da Fahad duk da a gefe guda tana jin fargaba a cikin ranta, ƙarfe bakwai daidai suka bar gida saboda makarantar ta su tana da ƴar tazara daga gidansu, sanin ranar monday ce dole za a samu cunkoson ababen hawa ya sa Fahad baro hotel ɗin da wuri, kai tsaye makarantar su ya nufa, su Leemarh na zuwa kusa da bakin gate ɗin makarantar ta ce ma driver ya ajiye ta a nan, da yake makarantar tasu babba ce motoci na shiga da ɗalibai, Batool ta kalle ta sanin ciki ake shiga da su ta ce mata miyasa zata sauka a nan, "Za a kawo mani wani saƙo ne, ku shiga yanzu nan da na amsa nima zan shigo." Ta faɗa tare da kai hannu ta buɗe ƙofar motar ta fita, da yake bakin gate ɗin akwai tarin motoci da ke ta shiga da fita hakan ya sa ba wanda hankalinsa ke a kanta har jami'an dake a bakin gate ɗin, tana tsaye can gefe guda tana ɗan waige-waigen hanya, ba a jima ba ta hango motar Fahad ta shigo titin ta ji wani sanyi a ranta, yana shigowa hanyar ya hango ta kasantuwar ita kaɗai ce a tsaye daga gefe, a gabanta ya yi parking glass ɗin gefen da take ya sauka ƙasa, haɗa ido suka yi da shi sai ta ga fuskarsa ta ƙara yi mata wani fresh, tambayarta ya yi ya fito ne ko za ta shigo, ɗan waigawa ta yi ta ga ba wanda hankalinsa ke a kanta ta kai hannu da sauri ta buɗe ƙofar gaban motan ta shiga, sanyi haɗe da daddaɗan ƙamshi ne suka karaɗe cikin motar, tana ɗan murmushi ta ce, "Good morning ya Fahad." Murmushin ya mayar mata ya ce, "Morning sis Leemarh, how was ur nyt." Ta amsa da Alhamdulillah, shiru ta ɗan yi ta kasa bashi saƙon da ta ce shi kuma yana ta kallonta alamar yana jiran saƙon, tambayarta ya yi Batool da Sultan ta ce an shiga da su cikin school ya ɗaga kai, kauda idonsa ya yi ya koma kallon gabansa ya lura kamar tana jin nauyin wani abu, kallonta ya ƙara yi for the second time ya ce, "Miye saƙon da zaki bada?" Cike da jin nauyi ta ɗago ƙatuwar school bag ɗinta mai kyau ta buɗe zip, kwaso chocolates ɗin ta yi gabanta na ɗan faɗuwa tana tsoron yadda zai reacting idan ya ga shine saƙon, bin abun cikin farin hannunta da ta miƙo mashi ya yi da kallo, ya ɗago idonsa da alamun rashin fahimta ya kalle ta, cikin ƴar rawar murya ta ce, "Dama wannan ne...tun da muka je mall na ɗauko nike son baka, ranan da daddare ban kai ga baka ba mom ta zo, jiya kuma ba a gida ka kwana ba." Da ƙyar ta ƙarasa maganar, sake kallon chocolates ɗin hannunta ya yi, a hankali ya ɗago hannunsa alamar ta bashi ta zuba mashi, bin su ya yi da kallo kana gani kasan masu tsada ne, ba komai ya fi jan hankalinsa ba face sunan da ke jikinsu wato LOVE tare da zanen red heart, lokaci guda ta ga ya yi ɗan murmushi tare da ɗago idanunsa ya kalle ta, yan kame-kame ta shiga yi tana ƙifce-ƙifcen idanu, da ɗan murmushi a fuskarsa slowly ya furta, "Thank you, I appreciate it" Har ta ji sanyi a ranta, ta yi ɗan murmushi sai kuma ta ce, "Ka yi haƙuri idan na 6ata maka lokaci." Still da murmushi ya ce, "No, you are important to me, so har fasa tafiya ina iya yi saboda buƙatan ki." Fuskarta har ta kasa 6oye yadda ta ji daɗin maganar, shima murmushi mai faɗi ya yi yana ci gaba da kallonta, "Ina colleague ɗin naka, ko ba yanzu zaku tafi ba?" Janye idanunsa ya yi daga kanta, haka nan ya ji baya son sake yin ƙarya kan hakan, juyawa ya yi suka haɗa ido calmly ya ce, "Ba wani colleague ɗina da zamu tafi tare, I have no option shi ya sa na faɗa ma dad haka." With confusion akan fuskar Leemarh ta ce, "To yaya Fahad ina ka kwana?" a hankali ya bata amsa da hotel, fuskarta ta bayyana yadda ta jinjina abun a ranta, cikin nuna ƴar damuwa ta ce, "Amman ya Fahad why zaka je hotel ka kwana kuma ga gida?" Shiru ya yi kawai ya ɗan shigar da lips ɗinsa, tana kallon shi ta ce, "Saboda mom ne ko?" Still bai yi magana ba, ɗan yamutsa fuska ta yi ganin mom na neman zame mata matsala, ta san saboda ita ne ya sa bai son zuwa gidansu tuntuni, wanda da yana zuwa tuni soyayya a tsakanin su ta ƙullu, "Ka yi haƙuri da duk abubuwan da mom ke yi maka yaya Fahad, wllh duk we are against it, ba kamar ni bana so cause you are important to me as well, shiyasa take yin faɗa da ni kan hakan." Cike da damuwa kamar zata yi kuka ta ƙarasa, idonsa akanta yana ɗan murmushi ya ce, "She is your mother ki daina yin faɗa da ita." Ta ɗan yarfa hannu muryarta na ɗan yin rawa ta ce, "To ai ni bana son abubuwan da take yi maka ne it hurts me." Ƙwalla ya gani sun cika idanunta, ta ɗan juyar da kai tana kokarin ganin basu zubo ba, "Leemarh..." Gently ya kira ta, ta amsa a hankali, "Look at me." Ta juyo suka haɗa ido, calmly ya ce, "Ki daina damuwa da hakan kin ji?" Ta ɗaga masa kai kafin ta ce, "To kai ma yaya Fahad pls ka daina damuwa da abubuwanta, haka halinta yake." Ya ɗan lumshe ido ya ce, "Na bari in sha Allah. I appreciate your concern for me, lovely sis." Murmushi ta saki tare da sauke idanunta, did he just call her lovely? Duk da ta san hakan ba wani abu bane zai iya zama yabo amman ta ji wani abu a ranta, muryarsa ta ji ya ce ta je kada ta yi latti sai sun yi magana, ta ɗago ta kalle shi ta ce to, har zata buɗe kofar ya sake cewa ya ga ai ana shiga ciki ko ta ce eh, ya ce bari ya shiga da ita daga haka ya tashi motan suka nufi cikin makarantar, bayan jami'ai dake bakin gate sun ɗan