Sashe 157
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ƙanƙame da towel ɗin sai faman zabga ihu take, tana yi tana waiwayen Maleek da ya biyo bayan ta cikin sassarfa a fusace, gudu gudu take taka matattakalar, tana kaiwa tsakiya ta yi missing step gaba ɗaya ta tafi ta fara gangarowa har ta ƙundumo ƙasa, gigitaciyar ƙara ta saki a firgice cikin jin raɗaɗi ta ke faɗin, "Mom...mom...come and help me....dad want to kill me..." Gaba ɗaya ihunta ya karaɗe cikin gidan, mrs Helen ce ta fito cikin falon a ruɗe, tana ganin abun da ke faruwa da kuma furucin da Basma ke yi da gudu ta nufi 6angaren Sapna, tare suka dawo da Sapna wadda kana ganinta ka san daga bacci aka taso ta, wani irin zaro ido Sapna ta yi ganin abun da ke faruwa, Basma na ganin ta ta fara kokarin zuwa wurinta amman Maleek ya ƙi bata damar hakan, tuni bakinta da goshinta sun fashe duk jini ya wanke mata fuska har a saman towel ɗinta, cikin matuƙar gigicewa Sapna ta nufo su, tana zuwa ta shiga tsakankanin su tana ƙoƙarin kare Basma daga dukan Maleek, wani irin kuka mai sautin gaske Sapna ta saki ganin yadda yake ta kokarin ci gaba da bugun ta, cikin fitar hayyaci Sapna ta ke faɗin, "Are you okey honey....mi yake faruwa ne kake son kashe ta...mi ta yi maka ne don Allah...Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..mrs Helen ki zo ki taimaka mani honey zai kashe baby!" Mrs Helen da ta yi tsaye gefe jikinta sai rawa yake yayin da take ƙwalla, duƙewa Sapna ta yi ta ƙanƙame duka ƙafafun Maleek ta shiga girgiza masa kai cikin kuka ta shiga faɗin, "Don girman Allah Maleek...don darajar manzon Allah...don darajar iyayenka...ka ƙyale ta, baka ganin ita kaɗai Allah ya bamu....so kake yi ka kashe mana ita ne..." Yadda take yin maganar kamar tana neman suƙewa idanunta sai ɗan lumshewa suke, ɗage kai Maleek ya yi yana kikkafta idanunsa, a hankali ya saki wayar hannunsa ya duƙe a wurin, zama ya yi dirshan a ƙasa ya sa duka hannuwansa ya tallabi kansa, ganin haka Sapna ta yi saurin miƙewa duk da jirin da take jin na neman kwasar ta, nufar wurin Basma dake ƙanƙame jikin Helen ta yi, hannu ta kai ta rungumo ta jikinta, tana jin yadda ta taho ta gane bata numfashi, a kiɗime ta ɗago kanta tana kiran sunanta, kallon Helen ta yi ta ce mata ta ɗauko mata ruwa ta amsa mata tare da nufar kitchen da gudu, bayan ta kawo ruwan ta zuba ma Sapna a hannu ta yayyafa mata a fuska nan take ta ja numfashi ta saki, wurin kujeru ta nufa da ita ta zauna a saman doguwar kujera tana ƙara rungume ta, Mrs Helen da ta biyo su tana tsaye daga gefe tana bin su da ido kana ganinta kasa duk a tsorace take don bata ta6a gani irin hakan ta faru a gidan ba tun da ta fara masu aiki, ɗago fuskar Basma ta yi tana kallo, ganin yadda fuskar tata ta yi ya sa ta sakin kuka mai sauti, cikin kukan ta ce, "What did you do to your dad baby?" Basma da idanunta ke ɗan buɗewa suna lumshewa a wahalce ta furta, "I don't know...." Kan Sapna ne ya ɗaure jin amsar Basma, bayan ɗan lokaci ta ce ma Helen ta zo ta kama ta, miƙewa Sapna ta yi ta nufi Maleek da har lokacin yana a yadda ta barshi bai ɗago kansa ba, zama ta yi a gabansa cikin zubar hawaye ta ce, "Maleek, mi baby ta aikata da ka yi mata wannan ɗanyen hukuncin....pls ka sanar mani...na san haka nan ba tare da dalili ba ba zaka yi mata wannan hukuncin ba...don girman Allah Ka sanar mani." Shiru kamar ba zai ɗago ba, a hankali ya ɗago kansa, abun da Sapna ta gani a fuskarsa ya matuƙar ƙara tayar mata da hankali, kuka ta ga yanayi hawaye sosai na bin fuskarsa, bin ta da kallo ya yi da jiƙaƙkun idanuwa, a ransa yana tunanin ta ina ma zai fara sanar da ita wannan al'amarin, sai dai ya san ba yadda zai yi dole a wannan ga6ar akwai buƙatar ya sanar mata, rokonsa ta ci gaba da yi kan ya faɗa mata, gyara zamansa ya yi cikin raunin murya ya ce, "I'm sorry Sapna..I'm sorry...I have no choice I will tell you this..." Jinjina masa kai ta yi ta kafe sa da idanunta da suma suke a jiƙe, yayin da tun bata ji mi zai faɗa matan ba bugun zuciyarta ya ƙaru, sai da Maleek ya tattaro duk wani ƙwarin gwiwar da ke gare shi sannan ya fara sanar da ita tun farkon al'amarin, har da ɗaukar ta da ya yi suka je gidan su Huda, ya sanar da ita labarin da ya bata kan abokinsa game da ɗiyarsa kawai ya faɗa mata hakan ne don kada hankalinta ya tashi, amman Basma ce ke aikata hakan, ya ce tun lokacin ya ke saka mata ido sosai, hakan ne ya sa ko tafiya ya rage yi in ba ta zama dole ba kuma bai wuce ƴan kwanaki, a wannan tafiyar da zai yi ne ganin zai yi har sati guda hakan ya saka sa zullumi kan Basma, shine kafin ya tafi ya saka camera a ɗakinta wurin gadonta ba tare da ta sani ba don yana son tabbatar da idan ta daina....cikin kuka mai sautin gaske ya ce mata ɗazun nan ya binciki video ɗin da camerar ta naɗa ya gan ta tare da wata daban suna aikata hakan a cikin ɗakinta. Jikinsa har jijjiga yake lokacin da ya ƙarasa faɗi mata, wani kalan zaro idanuwa Sapna ta yi, cikin ƙaraji ta shiga furta, "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun....Allahumma ajirni fi musibati..." Haka ta shiga jera addu'oi duk jikinta ya hau yin rawa, kokowar fita numfashinta ya fara yi, duk ƙoƙarin ta na ganin ta hana abun da ke shirin faruwa da ita abun ya ci tura, gaba ɗaya ta tafi ta faɗa jikin Maleek, da sauri ya kama ta yana ambaton sunanta nan take ya gane sumewa ta yi, miƙewa ya yi ya kinkime ta ya nufi hanyar part ɗinta, duk abun nan idanun Helen da Basma na kan su tun lokacin da suka ji Sapna ta saka salati tana yin addu'oi, Basma na ganin haka ta gane ya sanar ma mom ɗin tata wani abu da ya danganci abun da ya taba kama ta tana aikatawa, duk tsoro ya bayyanar mata, nan take ta fahimci ya gane abun da suka aikata da Lily, cikin rashin ƙarfin jiki ta fara ƙoƙarin miƙewa, mrs Helen na ce mata ta zauna ta ƙara hutawa amman bata bi ta kanta ba, cikin jan ƙafafu ta nufi bene da ƙyar ta fara hawa, tana hayewa sama ɗakinta ta nufa, tana zuwa ta shige tare da garƙame ƙofar.....