Sashe 42
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zuwa bayan sallar la'asar sun gama awaran Salma har ta yi wanka, fitowa innar su ta yi daga ɗaki ta ƙwala ma Salma kira, bayan ta amsa ta ce mata ta fito ta kaima hajiya awaran ta san zuwa yanzu ta tsane, amsawa ta yi da to daga cikin ɗakin, ba a jima ba ta fito jikinta sanye da doguwar rigar material ta yafo madaidaicin baƙin gyale a saman kanta, nufar inda innarsu take a duƙe tana maida awaran cikin roba ta yi ta ce mata gata, nuna mata robar ta yi bayan ta ɗauka ta ɗago ta ce ma innar idan ta tambayi kuɗin ya zata ce mata,
"Jeki kawai, idan ma ta tambaya ki ce kawai ban faɗi maki ba." Amsawa ta yi da to ta wuce hanyar fita. A nutse take tafiya ta rungume robar awaran a gefen cikinta, da alamun mamaki take kallon ƙofar gidan hajiyar da yake danƙam da mutane ga motar jami'an tsaro an faka daga can gefe, yayin da a bakin gate ɗin gidan jami'ai ne sun kai guda shidda sun tare mutane, a cikin ranta ta shiga raya ko lafiya? wani 6angare na zuciyarta ne ya bata ƙilan wannan ɗan majalissar ɗan hajiyan ne ya zo, tabbatar ma kanta ta yi da hakan ne ma, tsallaka titin ta yi tana ci gaba da tunanin ko ma za a barta ta shiga, da ƙyar ta samu kaiwa bakin gate ɗin inda jami'an suke, wani officer ne ya tambaye ta ya aka yi? A ɗarare ta ce mashi aiko ta aka yi ta kawo ma hajiya saƙo, tambayar miye acikin robar ya yi saboda a rufe take, hannu ta kai ta cire marfin ya gani ya ce ta wuce, wani a cikin sauran officers ɗin ya buɗe mata ƙaramar kofa ta wuce, tana shiga nan ma cikin harabar wasu dandazon mutanen ne daga can gefen parking space sun kewaye wurin sai hargowa suke yi, nufar shiga cikin gidan ta yi tana yi tana waiwayen mutanen har ta isa ƙofa ta shige, falon wayam ba kowa sai tv dake ta aiki, shiga ta yi ta tsaya daga tsakiyar falon ta fara yin sallama, sai da ta yi sau ukku sannan ta ji an amsa mata, Balaraba ce ta fito tana amsawa, tana ganin mai yin sallamar ta nufo cikin falon da murmushi, "Salma ke ce?" Tana murmushi ta amsa mata, "Eh Aunty Balaraba, ina wuni." Amsa mata ta yi da lafiya lau ta tambayeta ya makaranta har an dawo ta ce eh, faɗi mata saƙon da aka aiko ta ta yi Balarabar ta ce har an kawo awaran ke nan to bari ta yi ma hajiya magana ta nuna mata kujera ta ce ta zauna, ba a jima ba ta fito daga bangaren hajiyan ta ce mata gata nan zuwa, ba a ɗauki lokaci ba hajiya ta fito ta nufo cikin falon,
"Salma ce?" Ta tambaya da murmushi tana ƙarasowa, miƙewa Salma ta yi ta amsa da eh tare da gaishe da hajiya, amsa mata ta yi ta tambaye ta ya karatu, ganin ta miƙe ta ce mata ta koma ta zauna,
"Wai nikam hayaniyar mi cece nike ji tun a cikin É—aki sama sama?" Hajiya da har zata zauna ta dakata tana tambayar Balaraba,
"Mutane ne da yawa a can wurin ajiye motoci, a waje ma wurin gate akwai wasu sosai ofisoshi sun hana su shigowa, nima na ɗauka baza su barni ma in shigo ba." Salma ce ta faɗa, nufar hanyar babbar window hajiya ta yi ta leƙo wajen, jinjina kai ta hau yi kafin ta juyo ta dawo tana faɗin, "Mutanen Deeni ne. Wannan ma ai har ya fi mahaifin shi tara jama'a. Su dai maza Allah Ya yi su da jarabar son ƙwallo." Dawowa ta yi ta zauna kan kujera tare da kallon Balaraba ta ce mata ta ɗauki awaran ta je ta fara aikinta ta amsa da to bayan ta ɗauka ta tafi,
"Duk ya Æ´an'uwan naki." Hajiya ta tambaya tana kallonta da murmushi, "Suna nan lafiya lau." Ta amsa itama da murmushi,
"Nawa ne ta ce kuɗin?" Amsa ta bata da bata faɗi mata ba kawai ta ce ta kawo, ɗan kwa6e baki hajiya ta yi bata ce komai, gaba ɗaya maida hankalin su suka yi akan tv suka ci gaba da yin kallo a tare, after some minutes suka ji an yi sallama, a tare suka kai idanun su wurin ƙofa, Deen ne ya shigo jikin shi ya sauya shigar da ya zo da ita zuwa farar jallabiya mai gajeran hannu ta fito da suffar shi ta ƙaƙƙarfa, cikin falon ya nufo ya nufi can gefen hajiya saman kujera ya faɗa ya kai hannu ya shafi goshin shi tare da huro iska waje, hajiya dake kallon shi tana murmushi ta ce halan mutanen na shi sun tara mashi gajiya, amsa mata ya yi da wallahi ai bai ma iya gama ganin su ba ya gaji sai wani lokacin, tun lokacin da ya shigo Salma ta kafe shi da ido tana bin shi da kallon al'ajabi, tabbas in dai ba ƙarya idanunta ke nuna mata ba wannan shine mutumin nan na ɗazu, abun da ya ƙara tabbatar mata da hakan sumar kan shi duk da a yanzu ba a fake take ba ya sake ta ta kwanto a wuyanshi, sai kuma muryarsa da bata tunanin zata ƙara jin irinta ba tare da gane ba don ta fita daban, sam bai kalle ta ba bayan ya gama yi ma hajiya magana wayar shi ya shiga latsawa, Fahad ne ya shigo da sallama shima ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt dama bayan sun yi wanka ne suka fita yin sallar la'asar da lokacin ta ya yi shine fa mutane suka hana su shigowa ciki sai yanzu, wani iri faɗuwa gaban Salma ya shiga yi lokacin da ta kallo mai shigowar idanunta suka yi tozali da Fahad suka haɗa ido, da sauri ta janye idanun nata ta koma kallon ƙasa, cikin falon ya shigo ya nufi kujera ya zauna hajiya ta ce mashi an shigo ya ɗaga mata kai, bin Salma ya yi da kallo tun da ya shigo suka haɗa ido ya so ya gane ta, a hankali ta ɗago zata saci kallon shi aikuwa karaf idanunsu suka haɗu, kasa janye idanun nata ta yi duk ta bi ta kama kanta ta shiga kikkafta idanu yayin da bugun zuciyarta ya tsananta, ji take kamar ta tashi ta tafi amman ta rasa ƙwarin gwuiwar yin hakan, ganin irin kallon da yake jefa mata yasa ta sauke idanunta da sauri tana yamutsa yatsun hannunta,
"What the hell are you doing here?!" Kallon Fahad hajiya ta yi jin yayi magana duk da bata fahimci mi ya ce ba, ce mashi ta yi magana yake ne, ganin direction ɗin da yake kallo yasa ta juya ta kai idonta kan Salma da itama shi take kallon tana ɗan motsa baki, kasa fahimtar kallon mi suke ma juna hajiya ta yi ta sake kallon Fahad, a daidai lokacin ya miƙe ya nufo wurin da Salma take ta miƙe da sauri, bayan ya tsaya daga gabanta, fuska a ɗaure tamkar bai ta6a yin dariya ba ya sake furta, "Mi ya kawo nan!" Cikin yar tsawa ya yi maganar, hakan ne ya jawo hankalin Deen da ke latsa waya ya maido hankalin shi kan su,
"Baki ji maganan da nake maki ba, uban me ya kawo ki gidan nan??" Jikinta ne ya shiga yin rawa don a fusace yake mata maganar, cikin rawar murya ta ce, "D..dama aiko ni aka yi wurin hajiya..."
"Get out of this house! Idan na sake ganin ki a gidan nan sai na tattaka ki." Da sauri ta juya zata tafi hajiya da gaba ɗaya ta ruɗe da ganin abun da ke faruwa da sauri ta miƙe tana faɗin, "Fahad wai mike faruwa ne? Ka san Salma ne? Mi ya haɗa ka da ita?" Shiru bai bata amsa ba idon shi na kan Salma da ta fara tafiya da sauri za ta bar falon,
"Ke Salma dakata, zo nan!" Hajiya ta faÉ—a, tsayawa ta yi ta juyo a É—arare ta dawo ta tsaya daga gaban su, tambayar ta ta yi miya haÉ—a ta da shi, motsa baki ta shiga yi ta kasa cewa komai, kawai sai gani hajiya ta yi Fahad É—in ya kai hannu cikin zafin nama zai wanka ma Salma marin da yayi niyya yi É—azun, da sauri Salma ta goce duk da haka saida ya É—an same ta, ruÉ—ewa ta yi ta fashe da kuka gyalenta ya zame daga saman kanta, salati hajiya ta rafka tana ce ma Fahad mike damun shi? Mi ta yi mashi wai?"
"Hajiya just ta bar gidan nan yanzu, and I don't want to see her again, idan ba haka ba yanzun nan zan sa officers su kama ta su je su kulle ta." A zuciye ya yi maganar, wani salatin hajiya ta ƙara zabgawa hakan ya ja hankalin Balaraba dake a cikin kicin ta fito bakin ƙofa tana kallon abun da ke faruwa, yunƙurin barin falon Salma ta sake yi hajiyar ta dakatar da ita tana tambayar wai mi ya haɗa su,