Sashe 194
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sallar issha suka iso Funtua, kai tsaye gidan hajiya ta sa suka nufa, bayan sun isa aka buɗe mata ƙofa ta fito, tsabar yadda take son ganinta a Funtua ya sa ko gajiyar tafiya bata ji ta yi ba, a gadarance ta shiga cikin falon hajiya, lokacin ba kowa a cikin falon, sai ga Balaraba ta fito daga cikin kitchen tana riƙe da wata roba, tana yin arba da mom Jameela sai da gabanta ya faɗi da ƙarfi, sanin ita ɗin tauraruwa ce mai wutsiya wadda mafi yawan lokutta babu alkhairi a ganin ta, da sauri ta ƙarasa inda take tsaye ta rankwafa tana gaishe ta tare da yi mata sannu da zuwa, ba tare da ta amsa mata ba a daƙile ta tambayi hajiya, Balaraba ta ce mata tana ɗaki tun da ta shiga da magrib bata fito ba, "Je ki faɗa mata gani na zo." Mom ta faɗa tana ƙoƙarin zama a kan kujera, Balaraba ta yi saurin amsa mata da to ta nufi hanyar part ɗin hajiya, bada jimawa ba ta dawo ta ɗan rankwafa ta ce ga hajiyan nan zuwa ta ɗan ɗaga kai, Balaraba ta wuce sumi sumi kamar mara gaskiya ta koma kitchen, fitowa ta yi riƙe da tray ta ɗauro ruwa da lemu da cup, bayan ta matsar da table gaban mom, cike da taka tsan tsan ta zuba mata lemu a cup, cikin girmamawa ta ce mata ga lemu, sai kuma ta tambayi ta kawo abinci, kamar abun faɗa mom ta bata amsa da, "Bana buƙata." Balaraba ta miƙe ta yi saurin barin wurin don ta fahimci a fusace take, daidai nan hajiya ta fito, idanunta akan mom tana kallon ta da ɗan alamun mamaki ta nufo cikin falon, kallo ɗaya mom ta yi mata ta kauda fuskarta, hajiya ta ƙaraso cikin falon ta zauna a can kujeran gefe, tana kallon mom ta ce, "Kune tafe." Mom ta amsa da unhm, ɗan juyowa ta yi ta kalle ta kamar an yi mata dole ta gaishe da ita, hajiya ta amsa tana dai ta bin ta da kallo, "Yaushe kuka zo?" Tana cika ta bata amsa da isowarta ke nan, hajiya ta ɗaga kai sai kuma ta ce, "Ke kaɗai kika zo ne?" nan ma ta bata amsa da unhm, hajiya ta ɗan yi shiru still kallon ta take don bata ga alamun arziƙi a tattare da ita ba, can hajiya ta ce, "To sannu da zuwa, duk ya aka baro yaran?" A taƙaice ta amsa da lafiya, daga haka suka yi shiru hajiya ta maida idon ta kan tv, can ta juyo ta kalli mom da idonta ke kallon gefe ta wani ɗaure fuska, hajiya ta ce, "Ki sha lemun mana, bari Balaraba ta shirya maki abinci." A dakile ta ce, "Na ƙoshi...ba don su na zo ba." Hajiya ta ɗan yi murmushinta na dattako tare da jinjina kai ta ce, "To don me kika zo Jameela?" Ta wani kalle ta fuska a haɗe ta fara magana, "Na zo ne kan maganar rana da wai aka saka ma Deen ba tare da sanina ba matsayina na wadda ta haife sa." Hajiya da ke kallon ta da murmushi ta ce, "Amman ai mun yi da Ibrahim zai sanar maki." A ɗan harzuƙe mom ta ce, "Eh ya sanar mani, amman bayan an yi gaban kai, shine na zo in sanar cewa a matsayina na mahaifiyarsa ban amince ya auri yarinyar ba, kamar yadda tun farko na sanar da shi Deen ɗin da mahaifinsa." Hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce, "To yanzu ya kike son a yi ke nan?" Da sauri mom ta ce, "A warware saka ranan da aka yi, don ba zan ta6a amincewa da auren ba wllh." Hajiya ta ɗan ta6e baki tana bin ta da kallon mamaki, can ta sauke ƴar ajiyar zuciya ta ce, "Kema kin san mu ba ƙananun mutane bane, bamu yin magana mu dawo mu warware ta, musamman kuma magana da ta shafi aure. Mu tun da ya nuna mana yana son auran yarinyar to zamu goya masa baya in dai ba wata matsala aka samu da zata iya hana hakan ba, saboda mu bama hana namu abun da yake so matuƙar bai sa6a addini ba, koda kuwa mu abun bai yi mana ba muna yin haƙuri bama aiki da son zuciya, kuma ke kan ki shaida ce kan hakan, don haka idan kin ce ke baza ki amince ya auri yarinyar ba wannan ra'ayin ki ne, kuma ya rage tsakanin ki da ɗan ki ba mu ba." Duk da maganganun hajiya sun daki mom sosai bata nuna ba, ta yi ɗan murmushi mai kaman na yaƙe ta ce, "Shike nan, zan yi duk abun da ya dace don tabbatar da ra'ayin nawa." Hajiya ta gyaɗa mata kai ta ce Allah Ya taimaka, daga haka mom ta miƙe a taƙaice ta ce, "Sai Allah Ya kai mu." Hajiya ta ce, "Allah Ya tashe mu lafiya, ta bi mom da kallo ta ɗan kwa6e fuska har ta fita....mom na fita saura ƙiris su yi karo da Balaraba da zata shigo cikin falon, da sauri Balaraba ta ja gefe tare da sauke kanta ƙasa, har mom ta wuce sai kuma ta dakata tare da kallon ta ta ce mata ina ne gidan su yarinyar da aka ce Deen na so, Balaraba ta fara yi mata kwatance, cike da bada umarni ta ce mata su je ta kai ta gidan, har sai da gaban Balaraba ya faɗi, amman ta san bata isa ta ce ba zata je ba, ta yi saurin ce ma mom bari ta sako hijab, ta jefa mata wani kallo ta ce, "In tsaya jiran ki ke nan?" Balaraba ta girgiza kai, sai dai ta warware kallabinta ta yafa suka nufi gate, suna fitowa jami'in da ya zo tare da mom ya miƙe, da hannu ta yi mashi alamar bata buƙatan rakiyan, suka tsallaka hanya idanun officers ɗin bakin gate akan su, "Allah Ya kiyaye fitina..." Ɗaya cikin jami'an da ke tsaron gidan hajiya ya faɗa, "Kaima ka fahimci in da ta dosa ke nan." Wani shima ya faɗa, jami'in mom ya tambaye su ina zata je, ɗaya ya bashi amsa da da ƙyar idan ba gidan su yarinyar da ɗanta ke so zata je ba...suna shiga layin mom ta juyo ta ce ma Balaraba ina gidan, da hannu ta nuna mata gidan, ta ce mata ta koma ita kuma kai tsaye ta tunkari gidan, Balaraba ta yi tsaye gabanta nata faɗuwa, mom na zuwa saitin in da Imrana ke tuyan awara ta ɗan tsaya tana kallon shi fuska a yamutse, wani ƙululun baƙin ciki ya zo ya tokare mata wuya da ta gane ma idonta sana'ar awaran da suke yi da gaske ne, bayan Imrana ya sallami wani yaro ya ɗago ya kalli mom, innocently ya ce, "Awara za a baki?" mom ta ji tamkar ya ɗebo man tuyan waran ya watso mata, wani mugun tsoki ta bugu ta wuce gidan a fusace, Salma na zaune a saman tudunkar baranda, daga gaban ta farantin silver ne da roba tana yanka ma Imrana awara da zai zo ya ɗauka, tsaf tsaf da ita tana sanye da doguwar rigar atamfa, a hankali Salma ta ɗago ido jin kamar an shigo gidan, da sauri ta ƙarasa ɗagowa lokacin da ta yi arba da wadda ke tsaye a bakin ƙofar shigowa tana ƙare ma gidan kallon rashin arziƙi, duk da ba sosai take ganin fuskarta ba saboda hasken ƙwai mai cajin da ke cikin barandar ba ko ina ya haska sosai ba, hasken ya fi yawa a cikin baranda, ganin matar ta nufo ta ya sa Salma ta yi saurin miƙewa tsaye, ƙirjinta ya fara bugawa tana tunanin wacece wannan da ta shigo masu gida haka, sai da ta iso gabanta take ganinta sosai, nan da nan bugun ƙirjin Salma ya ƙaru sakamakon ganin fuskarta, a ranta ta fara raya ko dai aljana ce, amman kuma lokaci guda a ranta ta ji kaman ta san fuskar matar, mom ta bi Salma da kallo from head to toe, sannan ta bi farantin awaran da take yankawa da kallo tana yamutsa fuska sai ka ce ta ga kashi, ƙwarjini ta yi ma Salma sosai, a ɗan tsorace ta ce, "Sannu da zuwa..." mom ta sauke mata wani mugun kallo, duk da ba wadataccen haske ta gane ita ce yarinyar da Deen ke so, "Ina matar gidan!?" Ta tambaya a kausashe, Salma ta ce, "Innar mu?" Wani 6acin rai ya ƙara ziyartar mom jin yadda ta kira sunan mahaifiyarta, "Ban da ita akwai wata matar ne? koda yake na san mawuyacin abu ne a rasa wata matar, don talakan mutum ba a in da ya fi auki sai yin aure aure da tara yara sai ka ce ƴa'ƴan tumaki." Salma ta ɗan wara ido tare da ɗan buɗa baki, a hankali ta sauke idonta don ta ji bata iya jure ma kallon idanun matar, Salma ta shiga tunanin wace mata ce wannan da zata zo masu gida tana faɗin wannan maganganun...dammm! ƙirjinta ya yi wani bugu da ƙarfi lokacin da ta tuno da in da ta san fuskar mom wato a wayar Deen, da sauri ta ɗago ta kalle ta cikin rawar murya ta ce, "Ina yini..." mom ta dalla mata wata uwar harara, a tsawace ta ce, "Zaki kira mani matar gidan ko kuwa zaki tsaya kina mani munafunci." Da sauri Salma ta juya zata nufi ɗakin innarsu, daidai nan innar tasu ta ɗaga labule ta fito tare da faɗin, "Salma ke da wa, na ji kaman magana?" Salma ta tsaya cak ta kasa cewa komai, nufo bakin barandar innarsu ta yi, itama sai da gabanta ya ɗan faɗi lokacin da ta ga fuskar mom, innarsu Salma ta kasa cewa komai saboda yadda mom ta yi mata ƙwarjini gashi ta ɗaure fuska tamau, kallon Salma ta yi daga yanayin fuskarta ta fahimci ba lafiya ba, "Wacece?" Innar su ta tambaya a hankali, "Ni yakamata ai ki tambaya ba ita ba, ko tarbar baƙi ma ba a da basirar iyawa?" Innar su Salma ta ji maganar ta dake ta, amman sai ta ɗan yi murmushin ƙarfin hali ta ce, "A'a, ki yi hakuri hajiya, sannu da zuwa..ki shigo...bari in ɗauko